Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 10/1 pp. 24-29
  • Yaya Za Ka Iya Taimakon Ɗa “Mubazzari”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaya Za Ka Iya Taimakon Ɗa “Mubazzari”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Sa Wasu Suke Barin Gaskiya
  • Ka Kusaci Allah
  • Ka Yi Haƙuri Amma da Gaba Gaɗi
  • Yayin da an Yi wa Yaro Yankan Zumunci
  • Yadda Wasu Za Su Taimaka
  • Kada Ka Fid da Rai
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Iyaye, Kuna Taimaka wa Yaranku Su Yi Baftisma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ku Koya Wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 10/1 pp. 24-29

Yaya Za Ka Iya Taimakon Ɗa “Mubazzari”?

“Yi farinciki . . . ya ɓace, ya samu kuma.”—LUKA 15:32.

1, 2. (a) Yaya wasu matasa suka aikata game da gaskiyar Kirista? (b) Yaya iyaye da yaran da suke cikin irin yanayin nan suke ji?

“ZAN bar gaskiya!” Abin baƙin ciki ne iyaye da suke tsoron Allah da sun yi ƙoƙari sosai wajen renon yaransu a hanyar Kirista su ji kalmomin nan daga ɗansu! Wasu matasa sai su ‘janye’ kawai ba tare da faɗar niyyarsu ba. (Ibraniyawa 2:1) Waɗannan da yawansu suna kama da ɗa mubazzari na almarar Yesu, wanda ya bar gidan ubansa kuma ya yi almabazzaranci da kayan gadōnsa a ƙasa mai nisa.—Luka 15:11-16.

2 Ko da yake yawancin Shaidun Jehovah ba su da irin wannan matsalar, waɗanda suke da ita, babu ta’aziyyar da za ta iya cire baƙin cikinsu gabaki ɗaya. Kuma ba za a manta da baƙin ciki da matashi da ya yi tawaye zai iya sha ba. Cikin zuciyarsa, lamirinsa zai iya damunsa. A cikin almarar Yesu, ɗan mubazzari daga baya ya “koma cikin hankalinsa,” wannan ya sa ubansa farin ciki. Ta yaya iyaye da wasu cikin ikilisiya za su taimaka wa mubazzarai su ‘koma cikin hankalinsu’?—Luka 15:17.

Abin da Ya Sa Wasu Suke Barin Gaskiya

3. Menene wasu dalilai da suke sa matasa suke barin ikilisiyar Kirista?

3 Da akwai matasa dubbai da suke bauta wa Jehovah da farin ciki cikin ikilisiyar Kirista. To, me ya sa wasu matasa suke barin ikilisiya? Suna jin cewa suna hasarar wani abin da duniya take da shi ne. (2 Timothawus 4:10) Ko kuma suna jin cewa garken tumaki na Jehovah na kāriya yana matsa wa mutum lamba. Lamiri mai laifi, son kishiyar jinsi sosai, ko kuma neman amincewar tsara ma zai iya sa matashi ya janye daga garken Jehovah. Mai yiwuwa ne matashi ya daina bauta wa Allah saboda wani abin da yake ganin cewa riya ce wajen iyayensa ko kuma wasu Kiristoci.

4. Sau da yawa menene ainihin dalilin da ke sa matasa su ratse?

4 Halayen tawaye na yaro alamu ne na kumamanci a ruhaniya, bayyanar abin da ke cikin zuciyarsa. (Misalai 15:13; Matta 12:34) Ko da menene dalilin da ya sa matashin ya ratse, ainihin matsalar rashin ‘cikakken sanin gaskiya’ ne. (2 Timothawus 3:7) Maimakon bauta wa Jehovah kawai babu himma, muhimmin abu ne matasa su gina dangantaka na kud da kud da shi. Me zai taimake su su yi haka?

Ka Kusaci Allah

5. Menene ake bukata don matashi ya gina dangantaka na kansa da Allah?

5 “Ku kusato ga Allah,” in ji almajiri Yaƙub, “shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yaƙub 4:8) Don a yi haka, dole a taimaki matashi ya so Kalmar Allah. (Zabura 34:8) Da farko zai bukaci “madara”—muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki. Amma sa’ad da ya nuna yana son Kalmar Allah kuma da marmarin “abinci mai-ƙarfi”—koyarwa masu zurfi ta ruhaniya—jim kaɗan zai manyanta a ruhaniya. Wani matashi da ya yarda da cewa ya shagala cikin hanyoyin duniya ya fara daraja ɗabi’o’i na ruhaniya. Me ya taimake shi ya juyo? A bin shawarar da aka ba shi cewa ya karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa, ya adana tsarin karanta Littafi Mai Tsarki na kullum. Hakika, karanta Kalmar Allah a kai a kai muhimmi ne don a gina gami na kud da kud da Jehovah.

6, 7. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su koyi yin sha’awar Kalmar Allah?

6 Lalle yana da muhimmanci iyaye su taimaki yaransu su gina son Kalmar Allah! Duk da cewa suna nazari na iyali a kai a kai, wata yarinya mai shekara goma sha ta yi tarayya da yara masu taka doka. Ta tuna haka game da nazarinsu na iyali: “Sa’ad da Babana ya yi tambayoyi, sai na karanta amsoshi kawai, ba tare da kallon fuskarsa ba.” Maimakon su karanta littafin kawai a nazari na iyali, iyaye masu hikima suna amfani da fasahar koyarwa. (2 Timothawus 4:2) Domin matashin ya ji daɗin nazarin, dole ne ya kasance ciki. Me ya sa ba za ka yi tambayoyin bincike don ya furta abin da ke zuciyarsa ba? Ka ƙarfafa matashin ya yi amfani da abin da kuke nazarinsa.a

7 Bugu da ƙari, ka sa tattaunawa ta Nassi ta zama na ban marmari. A inda ya dace, ka sa matasan su yi kwaikwayon wasu aukuwan Littafi Mai Tsarki. Ka taimake su su ƙaga a zuci wurare da kuma abubuwan da ke cikin ƙasar da ake tattaunawa ta faru. Yin amfani da taswira da tsari zai taimaka. Hakika, idan an ɗan tsara a ka, nazari na iyali zai zama da ban marmari kuma ya bambanta. Iyaye su ma ya kamata su sake duba dangantakarsu da Jehovah. Yayin da su kansu sun kusato ga Jehovah, za su iya taimaka wa yaransu su yi hakan.—Kubawar Shari’a 6:5-7.

8. Ta yaya addu’a take taimakon mutum ya kusaci Allah?

8 Addu’a tana taimakon mutum ya kusaci Allah. Wata yarinya ’yar shekara goma sha ta riƙice a zancen bin hanyar rayuwa ta Kirista da kuma tarayyarta da abokai da ba sa bin imaninta. (Yaƙub 4:4) Me ta yi game da wannan? “A lokaci na farko,” in ji ta, “na faɗa wa Jehovah cikin addu’a yadda nake ji da gaske.” Ta kammala da cewa an amsa addu’arta lokacin da ta samu wata abuya cikin ikilisiyar Kirista da za ta iya gaya wa asirinta. Da jin cewa Jehovah yana kāre ta, ta soma gina dangantaka da shi. Iyaye za su iya taimakon yaransu ta wurin ƙara ingancin addu’ar da suke yi. Sa’ad da suke addu’a ta iyali, iyaye za su iya faɗar dukan zuciyarsu don yaransu su ga irin dangantaka da ke tsakanin su da Jehovah.

Ka Yi Haƙuri Amma da Gaba Gaɗi

9, 10. Wane misali ne Jehovah ya bari a kasancewa da tsawon jimrewa da Isra’ilawa da suka ratse?

9 Yayin da matashi ya fara janyewa, zai so ya ware kansa kuma ya ƙi wani ƙoƙarin da iyayensa za su yi na yin taɗi na ruhaniya da shi. Menene iyaye za su yi a irin yanayin nan na gwaji? Ka yi la’akari da abin da Jehovah ya yi da Isra’ila ta dā. Ya jimre da Isra’ilawa “masu-ƙarfin kai” na fiye da shekara 900 kafin ya yashe su ga hanyarsu ta tawaye. (Fitowa 34:9; 2 Labarbaru 36:17-21; Romawa 10:21) Duk da yadda suke ‘gwada shi’ sau da yawa, Jehovah ya yi musu “jinƙai.” “Sau dayawa fushinsa ya kan juya, ba ya zuga dukan hasalarsa ba.” (Zabura 78:38-42) Allah ba shi da laifi a yadda ya bi da su. Iyaye masu ƙauna suna koyi da Jehovah kuma suna haƙuri sa’ad da yaro bai bi dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na son su taimake shi nan da nan ba.

10 Kasancewa da tsawon jimrewa, ko haƙuri ba ya nufin ‘jimrewa da daɗewa’; yana nufin ƙin fid da rai cewa gyara ba za ta yiwu ba kuma cewa dangantakar ta riga ta ɓace. Jehovah ya ba da misalin yadda za a kasance da tsawon jimrewa. Ya ɗauki mataki ta aika manzanni zuwa ga Isra’ilawa ‘sau da yawa.’ Jehovah ya yi “juyayin mutanensa,” ko da ‘suna yi wa manzannin Allah na gaskiya ba’a, suna rena maganarsa.’ (2 Labarbaru 36:15, 16) Ya roƙi Isra’ilawa, yana cewa: “Ku juyo dukanku yanzu ga barin hanyarku ta mugunta.” (Irmiya 25:4, 5) Duk da haka, Jehovah bai karya ƙa’idodinsa na adalci ba. An ce Isra’ilawan su “juya” zuwa wurin Allah da hanyoyinsa.

11. Ta yaya iyaye za su iya kasancewa da tsawon jimrewa amma da gaba gaɗi a bi da yaron da ya ratse?

11 Iyaye za su iya yin koyi da Jehovah a kasancewa da tsawon jimrewa su ƙi fid da rai a kan yaro da ya ratse. Ta kasancewa da bege, za su iya ɗaukan mataki don barin hanyar sadarwa a buɗe ko kuma sake buɗe hanyar sadarwa. Ko da suna manne wa bin ƙa’idodin adalci, ‘sau da yawa’ za su iya addu’a yaron ya komo zuwa hanyar gaskiya.

Yayin da an Yi wa Yaro Yankan Zumunci

12. Wane hakki ne iyaye suke da shi ga yaron da yake zama da su amma aka fitar da shi daga ikilisiya?

12 Me za a ce idan yaron da ke tare da iyayensa ya yi laifi mai tsanani kuma saboda halinsa na ƙin tuba aka fitar da shi daga ikilisiya? Tun da yake yaron yana zama da iyayensa, har ila yau, suna da hakkin koyar da shi kuma su yi masa horo da zai jitu da Kalmar Allah. Yaya za a yi wannan?—Misalai 6:20-22; 29:17.

13. Ta yaya iyaye za su yi ƙoƙarin su taɓa zuciyar yaronsu da ya yi zunubi?

13 Zai yiwu—E, zai fi kyau—a yi irin koyarwa da kuma horon lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki naku kawai da shi. Kada iyayen su hukunta halin yaron kawai ba amma su yi ƙoƙarin bincika abin da ke zuciyarsa. Yaya yawan ciwonsa na ruhaniya yake? (Misalai 20:5) Za a iya taɓa motsin zuciyarsa? Waɗanne nassosi za a iya amfani da su da kyau? Manzo Bulus ya tabbatar mana: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibraniyawa 4:12) Hakika, iyaye za su iya taimakon yaransu fiye da gaya musu kawai cewa su guji sake yin laifi. Za su yi ƙoƙarin soma shi kuma su yi gyara a tsarin warkarwar.

14. Wane mataki ne na farko da matashi da ya yi laifi zai ɗauka don ya maido da dangantakarsa da Jehovah, kuma yaya iyaye za su iya taimakon yaron ya ɗauki wannan matakin?

14 Matashi da ya yi laifi yana bukatar ya gyara dangantakarsa da Jehovah. Mataki na farko da dole ya ɗauka don ya “tuba . . . [ya] juyo.” (Ayukan Manzanni 3:19; Ishaya 55:6, 7) A taimakon matashin da ke gidansu ya tuba, dole ne iyaye za su ‘kame kansu, suna koyarwa mai sauƙi da haƙuri’ ga yaron da yake da damuwa. (2 Timothawus 2:24-26) Suna bukatar su yi masa ‘gyara’ da Littafi Mai Tsarki. Kalmar Helenanci da aka fassara ‘gyara’ ana iya fassara ta ‘bayar da tabbaci.’ (Ru’ya ta Yohanna 3:19; Yohanna 16:8) Saboda haka, yin gyara ya ƙunshi bayar da cikakken tabbaci don a tabbatar da yaron game da tafarkinsa na zunubi. Hakika, yin haka ba shi da sauƙi. Inda ya yiwu, iyayen za su iya motsa zuciyarsa, su yi amfani da kowacce hanya ta Nassi da ta dace su ba shi tabbaci. Ya kamata su taimake shi ya fahimci bukatar ya “ƙi mugunta, [ya] ƙaunaci nagarta.” (Amos 5:15) Zai iya komo ‘hankalinsa daga tarkon Iblis.’

15. Wane aiki addu’a take yi wajen maido da dangantakar mutum da ya yi wa Jehovah laifi?

15 A maido da dangantakar mutum da Jehovah, addu’a muhimmiyar aba ce. Hakika, kada wani ya yi ‘roƙo’ game da zunubin wanda ya ƙi tuba da yake tarayya dā da ikilisiyar Kirista. (1 Yohanna 5:16, 17; Irmiya 7:16-20; Ibraniyawa 10:26, 27) Amma, iyaye za su roƙi Jehovah ya ba su hikima su bi da yanayin. (Yaƙub 1:5) Idan matashin da aka yi masa yankan zumunci ya nuna tuba a fili amma ba shi da ‘gaba gaɗi wajen Allah,’ iyayen za su iya addu’a cewa Allah ya sake duba dalilin gafarta laifin yaron, cewa nufinsa ya kasance. (1 Yohanna 3:21) Ya kamata addu’o’insu su taimaki matashin ya ga cewa Jehovah Allah ne mai jinƙai.b—Fitowa 34:6, 7; Yaƙub 5:16.

16. Ta yaya za mu taimaki waɗanda suke cikin iyalin matasa da aka yi musu yankan zumunci?

16 Idan aka yi wa matashin da ya yi baftisma yankan zumunci, ana bukatar waɗanda suke cikin ikilisiyar “kada su yi tarayya da” shi. (1 Korinthiyawa 5:11; 2 Yohanna 10, 11) A ƙarshe, wannan zai taimake shi ya ‘komo cikin hankalinsa’ kuma ya komo cikin garken Allah mai kāriya. (Luka 15:17) Ko ya dawo ko a’a, waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya ƙarfafa iyalin matashin da aka yi wa yankan zumunci. Dukanmu za mu iya rifta zarafi mu nuna ‘juyayi’ kuma mu zama “masu-tabshin zuciya” gare su.—1 Bitrus 3:8, 9.

Yadda Wasu Za Su Taimaka

17. Menene waɗanda suke cikin ikilisiya za su tuna da shi yayin da suke ƙoƙarin su taimake yaron da yake ratsewa?

17 Matashi da ba a yi masa yankan zumunci ba daga cikin ikilisiyar Kirista amma wanda ya raunana a bangaskiya fa? “Idan gaɓa ɗaya kuwa ya sha raɗaɗi,” in ji manzo Bulus, “dukan gaɓaɓuwa suna shan raɗaɗi tare da shi.” (1 Korinthiyawa 12:26) Wasu za su iya nuna suna son matashin nan sosai. Amma, ana bukatar a mai da hankali domin matashi da yake ciwo a ruhaniya zai iya kasancewa da mummunar rinjaya a kan wasu matasa. (Galatiyawa 5:7-9) A wata ikilisiya, wasu da suke neman su taimaka wa wasu matasa da suka raunana a ruhaniya suka gayyace su zuwa wata liyafa su yi kaɗe-kaɗe tare. Ko da yake matasan sun yarda kuma sun ji daɗinsa, rinjayarsu a kan juna ya sa suka daina tarayya da ikilisiyar. (1 Korinthiyawa 15:33; Yahuda 22, 23) Abin da zai taimaka a warkar da ɗa da ya raunana, ba liyafa ba ce da ba ta da ƙa’idodi na ruhaniya, amma tarayya da zai taimake shi ya koyi son abubuwa na ruhaniya.c

18. Ta yaya za mu yi koyi da halin uban ɗa mubazzari cikin almarar Yesu?

18 Yayin da wani matashi da ya bar ikilisiya dā ya dawo zuwa Majami’ar Mulki ko kuma ya halarci babban taro, ka yi tunanin yadda yake ji. Bai kamata mu nuna halin maraba da uban ɗa mubazzari ya yi cikin almarar Yesu ba? (Luka 15:18-20, 25-32) Wani matashi da ya bar ikilisiyar Kirista daga baya ya halarci taron gunduma ya ce: “Tsammani nake kowa zai yi banza da ni, amma ’yan’uwa maza da mata suka kusace ni kuma suka yi mini maraba. Abin ya taɓa ni ƙwarai.” Ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki kuma daga baya ya yi baftisma.

Kada Ka Fid da Rai

19, 20. Me ya sa ya kamata mu kasance da hali mai kyau game da ɗa mubazzari?

19 Taimakon ɗa “mubazzari” ya komo ‘hankalinsa’ na bukatar haƙuri kuma yana da wuya ga iyaye da kuma wasu. Amma kada ku fid da rai. “Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa, yadda waɗansu mutane su ke aza jinkiri; amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Muna da tabbaci daga Nassi cewa Jehovah yana son mutane su tuba kuma su rayu. Hakika, ya ɗauki mataki na shirya mutane su sulhunta gare shi. (2 Korinthiyawa 5:18, 19) Haƙurinsa ya sa ya yiwu mutane miliyoyi su komo hankalinsu.—Ishaya 2:2, 3.

20 To, bai kamata iyaye su yi amfani da kowacce hanya da ta yiwu na Nassi don taimaka wa yaro mubazzari ya komo hankalinsa ba? A yin koyi da Jehovah, ka kasance da tsawon jimrewa yayin da ka ke ɗaukan matakai masu kyau don taimaka wa yaronka ya komo wurin Jehovah. Ka manne wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, ka yi ƙoƙarin nuna halayen Jehovah na ƙauna, shari’a, da kuma hikima yayin da ka ke yin addu’a don taimakonsa. Yadda ’yan tawaye da yawa sun karɓi gayyatar Jehovah ta ƙauna cewa su dawo, yaronka mubazzari ko ’yarka za su iya komowa zuwa garken Allah na kāriya.—Luka 15:6, 7.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani a kan yadda za a koyar da yara sosai, duba Hasumiyar Tsaro 1 ga Yuli, 1999, shafuffuka 13-17.

b Ba za a yi addu’o’in nan cikin jama’a a kan wanda aka yi masa yankan zumunci a taron ikilisiya ba, tun da yake wasu ba su san yanayin wanda aka yi masa yankan zumuncin ba.—Duba Hasumiyar Tsaro, 15 ga Oktoba, 1979, shafi na 31 (Turanci).

c Don shawarwari, duba Awake! 22 ga Yuni, 1972, shafuffuka 13-16; 22 ga Satumba, 1996, shafuffuka 21-23, Turanci.

Ka Tuna?

• Menene wataƙila tushen matsalar yayin da matasa sun bar ikilisiya?

• Ta yaya za a iya taimaka wa matasa su gina dangantaka ta kansu da Jehovah?

• Me ya sa iyaye suke bukatar tsawon jimrewa amma kasancewa da gaba gaɗi wajen taimaka wa ɗa mubazzari?

• Ta yaya waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya taimaka wa matashi mubazzari ya komo?

[Hoto a shafi na 26]

Karatun Kalmar Allah muhimmi ne a gina gami na kud da kud da Jehovah

[Hoto a shafi na 26]

Addu’ar iyaye daga zuci zai iya taimaka wa yaransu su ga dangantaka da ke tsakaninsu da Jehovah

[Hoto a shafi na 28]

Ka yi wa ɗa mubazzari maraba yayin da ya komo ‘hankalinsa’

[Hoto a shafi na 29]

Ka ɗauki matakai masu kyau don taimaka wa ɗanka ya komo wurin Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba