Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/15 pp. 3-7
  • Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Karɓi Gayyatar Yanzu
  • Ka San Jehobah Sosai
  • Yadda Addu’a Take Zurfafa Ƙaunarka ga Jehobah
  • Halin Kirki Yana Nuna Cewa Kana da “Zuciya Mai Tsarki”
  • Matasa Masu Yabon Jehobah
  • Matasa, Ku Zaɓi Ku Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Addini Zaɓi Na ne Ko na Iyaye Na?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Matasa Ku Ci Gaba da Samun Ci Gaba Bayan Kun Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/15 pp. 3-7

Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah

“Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.”—M. WA. 12:1.

1. Wace gayyata ce Jehobah ya miƙa ga yara a Isra’ila?

WASU shekaru 3,500 da suka shige, annabin Jehobah, Musa ya umurci firistoci da kuma dattawa na Isra’ila: “Ka tattara jama’a, maza da mata da ƙanana . . . , domin su ji, su koya, su ji tsoron Ubangiji Allahnka, su kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a domin su aikata.” (K. Sha 31:12) Ka lura da waɗanda aka umurta su halarci taro na sujjada: maza, mata, da kuma yara ƙanana. Hakika, yara ƙanana suna cikin waɗanda aka gaya musu su saurara, su koya, kuma su bi ja-gorar Jehobah.

2. Ta yaya Jehobah ya nuna kulawarsa ga matasa a ikilisiyar Kirista ta farko?

2 A ƙarni na farko, Jehobah ya ci gaba da furta kulawarsa ga matasa cikin mutanensa. Alal misali, ya hure manzo Bulus ya haɗa umurni musamman ga matasa a cikin wasu wasiƙu da ya aika wa ikilisiyoyi. (Karanta Afisawa 6:1; Kolosiyawa 3:20.) Matasa Kiristoci da suka yi amfani da wannan shawarar sun ci gaba da nuna ƙauna ga Ubansu na sama mai ƙauna kuma sun sami albarkarsa.

3. Ta yaya yara ƙanana suke nuna muradinsu na bauta wa Allah?

3 An gayyaci yara ƙanana a yau su taru domin su yi wa Jehobah sujjada kuwa? Hakika! Saboda haka, abin farin ciki ne ga dukan mutanen Allah su lura cewa matasa masu yawa bayin Allah a kewayen duniya suna saka faɗakarwar Bulus a zuci: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka, kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗar da juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibran. 10:24, 25) Bugu da ƙari, yara da yawa suna fita yin wa’azin bishara ta Mulkin Allah tare da iyayensu. (Mat. 24:14) Kuma domin su nuna cikakkiyar ƙaunarsu ga Jehobah, dubban matasa a kowace shekara suna ba da kansu domin yin baftisma kuma sun more albarkar da ke tattare da zama almajirin Kristi.—Mat. 16:24; Mar. 10:29, 30.

Ka Karɓi Gayyatar Yanzu

4. A wane lokaci ne matasa za su karɓi gayyatar Allah na yi masa bauta?

4 Mai wa’azi 12:1 ta ce: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.” Shekara nawa ne ya kamata yara su kai kafin su karɓi gayyatar nan mai daɗaɗa rai na yin bauta da hidima ga Jehobah? Nassosi bai taƙaita ainihin shekaru ba. Saboda haka, kada ka ja da baya, ta wajen yin tunanin cewa ka yi ƙanƙantar saurarar Jehobah da kuma bauta masa. Ko da menene shekarunka, an ƙarfafa ka ka karɓi wannan gayyatar da wuri.

5. Ta yaya ne iyaye za su taimaka wa yaransu su ci gaba a ruhaniya?

5 Yawancinku kun samu taimakon ci gaba a ruhaniya ne wurin ɗaya daga cikin iyayenku ko kuma su biyun. A wannan hanyar, kuna kama ne da Timoti na lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da yake ɗan ƙaramin yaro, mahaifiyarsa, Afiniki, da kakarsa, Loyis, sun koya masa littattafai masu tsarki. (2 Tim. 3:14, 15) Wataƙila, iyayenka suna koyar da kai a irin wannan hanyar ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, yin addu’a tare da kai, ɗaukan ka zuwa taro na ikilisiya da kuma manyan taro na mutanen Allah, da kuma zuwa hidimar fage tare da kai. Hakika, koya maka hanyoyin Allah hakki ne mai muhimmanci sosai da iyayenka suka samu daga wurin Jehobah. Kana nuna godiya kuwa ga ƙauna da kuma kulawar da suke nuna maka?—Mis. 23:22.

6. (a) In ji Zabura 110:3, wace irin bauta ce take faranta wa Jehobah rai? (b) Menene za mu tattauna yanzu?

6 Duk da haka, yayin da ku yara kuke girma, Jehobah yana son “ku gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke,” kamar yadda Timoti ya yi. (Rom. 12:2) Idan kuka yi hakan, za ku saka hannu a ayyuka na ikilisiya, ba wai domin iyayenku suna so ku yi hakan ba, amma domin kuna son ku yi nufin Allah. Idan kuka bauta wa Allah da son rai, hakan zai faranta ransa. (Zab. 110:3) To, ta yaya za ku iya nuna cewa kuna son ku ƙarfafa muradinku na saurarar Jehobah da kuma bin ja-gorarsa? Za mu tattauna hanyoyi uku masu muhimmanci da za ku iya yin hakan. Su ne nazari, addu’a, da kuma ɗabi’a. Bari mu bincika su ɗaya bayan ɗaya.

Ka San Jehobah Sosai

7. Ta yaya Yesu ya kafa misali a matsayin daliɓi na Nassosi, kuma menene ya taimaka masa ya yi hakan?

7 Hanya ta farko da za ku nuna cewa kuna son ku zurfafa muradinku na bauta wa Jehobah ita ce ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki a kullum. Za ku gamsar da bukatarku ta ruhaniya kuma ku samu sani mai tamani na Littafi Mai Tsarki ta wajen karanta Kalmar Allah a kullum. (Mat. 5:3) Yesu ya kafa misali. A wani lokaci sa’ad da yake ɗan shekara 12, iyayensa sun iske shi a cikin haikali, “yana zaune a tsakiyar malamai, yana jinsu, yana kuwa yi masu tambayoyi.” (Luk 2:44-46) Sa’ad da yake ɗan yaro, Yesu yana da marmarin Nassosi kuma yana son ya fahimce su. Menene ya taimaka masa ya yi hakan? Babu shakka, mahaifiyarsa, Maryamu, da kuma mijinta, Yusufu, sun ɗauki muhimmiyar matsayi a wannan batu. Bayin Allah ne su, kuma sun koya wa Yesu umurnin Allah tun yana ƙarami.—Mat 1:18-20; Luk 2:41, 51.

8. (a) A wane lokaci ne ya kamata iyaye su soma gina ƙaunar Kalmar Allah a yaransu? (b) Ka ba da wani labari da ya tabbatar da muhimmancin koyar da yara tun suna ƙanana.

8 Hakazalika, iyaye masu tsoron Allah a yau sun gane muhimmancin gina marmarin gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a zukatan yaransu tun suna ƙanana. (K. Sha 6:6-9) Abin da Rubi, wata ’yar’uwa Kirista ta yi ke nan, ba da daɗewa ba da haihuwar ɗanta na farko, Joseph. A kowace rana, tana karanta masa Littafina Na Labarun Bible. Yayin da yake girma, ta taimaka masa ya haddace nassosi dabam-dabam. Joseph ya amfana daga wannan koyarwar kuwa? Bayan ya koyi yadda ake yin magana, yana ba da labarai na Littafi Mai Tsarki da nasa kalmomi. Kuma sa’ad da yake ɗan shekara biyar, ya ba da jawabinsa na farko a Makarantar Hidima ta Allah.

9. Me ya sa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan abin da ka karanta yake da muhimmanci?

9 Don faɗaɗa ci gabanku na ruhaniya, ya kamata ku matasa ku sa karanta Littafi Mai Tsarki a kullum ya zama halinku a dukan kwanakin kuruciyarku da kuma sa’ad da kuka girma. (Zab. 71:17) Me ya sa karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku ku sami ci gaba? Ku lura da abin da Yesu ya ce a cikin addu’a ga Ubansa: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya.” (Yoh 17:3) Hakika, yayin da kuke ƙara samun sani game da Jehobah, za ku san Shi sosai kuma za ku zurfafa ƙaunarku a gare shi. (Ibran. 11:27) Saboda haka, a duk lokacin da kuka karanta wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki, ku yi amfani da wannan zarafin ku ƙara koya game da Jehobah. Ku tambayi kanku: ‘Menene wannan batun ya koya mini game da Jehobah da Kansa? Ta yaya wannan sashe na Littafi Mai Tsarki ya nuna ƙaunar Allah da kuma kulawarsa a gare ni?’ Yin bimbini sosai a kan irin waɗannan tambayoyin zai taimaka muku ku koyi yadda Jehobah yake tunani da kuma yadda yake ji da kuma abin da yake bukata a gareku. (Karanta Misalai 2:1-5.) Kamar Timoti matashi, za ku “tabbata da” abin da kuka koya daga Nassosi, kuma hakan zai motsa ku ku bauta wa Jehobah da son rai.—2 Tim. 3:14.

Yadda Addu’a Take Zurfafa Ƙaunarka ga Jehobah

10, 11. Ta yaya addu’a za ta taimaka muku ku ƙarfafa muradinku na bauta wa Allah?

10 Hanya ta biyu da za ku ƙarfafa muradinku na bauta wa Jehobah da yardar rai ita ce ta wurin addu’o’inku. A Zabura 65:2, mun karanta: “Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.” Ko a lokacin da Isra’ila take da matsayin mutanen da suka ɗauki alkawari da Allah, baƙin da suka zo haikalin Jehobah za su iya yin addu’a a gare shi. (1 Sar. 8:41, 42) Allah ba mai son zuciya ba ne. Waɗanda suke kiyaye dokokinsa suna da tabbaci cewa zai saurare su. (Mis. 15:8) Hakika, “masu rai duka” sun haɗa da ku yara ƙanana.

11 Kun san cewa tushen abuta na ainihi ita ce sadarwa mai kyau. Wataƙila, kuna jin daɗin tattauna abin da ke zuciyarku, damuwarku, da kuma yadda kuke ji tare da aboki na kud da kud. Hakazalika, ta wurin yin addu’a daga zuci, kuna magana ne da Mahaliccinku. (Filib. 4:6, 7) Ku yi magana da Jehobah kamar kuna gaya wa uba mai ƙauna ko aboki na kud da kud abin da ke zuciyarku. A gaskiya, akwai dangantaka sosai tsakanin yadda kuke yin addu’a da kuma yadda kuke ji game da Jehobah. Za ku lura cewa idan abokantakarku da Jehobah ta yi ƙarfi, addu’o’inku za su ƙara kasancewa masu ma’ana.

12. (a) Me ya sa addu’o’i masu ma’ana sun ƙunshi fiye da kalmomi kawai? (b) Menene zai taimake ku ku fahimci cewa Jehobah yana kusa da ku?

12 Ku tuna cewa, addu’a mai ma’ana ta ƙunshi fiye da faɗin kalmomi kawai. Ta haɗa da yadda kuke ji a cikinku. A cikin addu’o’inku, ku nuna ƙauna, ladabi mai zurfi, da kuma dogara sosai ga Jehobah. Yayin da kuka gane yadda Jehobah yake amsa addu’o’inku, za ku ƙara fahimtar cewa “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi.” (Zab. 145:18) Hakika, Jehobah zai kusance ku, ya ƙarfafa ku don ku yi tsayayya da Iblis kuma ku yi zaɓi mafi kyau a rayuwa.—Karanta Yaƙub 4:7, 8.

13. (a) Ta yaya yin abota da Allah ya taimaki wata ’yar’uwa? (b) Ta yaya yin abota da Allah ya taimake ka ka yi nasara wajen sha kan matsi na tsara?

13 Yi la’akari da yadda Cherie ta sami ƙarfi daga kasancewa da dangantaka na kud da kud da Jehobah. A makarantar sakandare, ta sami lambobin yabo domin tana da ilimi sosai kuma ta ƙware a wasannin guje-guje. Sa’ad da ta gama makaranta, an ba ta sukolashif da zai sa ta biɗi ilimi a babbar jami’a. “Kyautar, abu ne da ke shiga ido” in ji Cherie, “kuma masu koya mana wasanni da kuma abokan makaranta sun matsa mini in karɓe ta.” Ta gano cewa, biɗar ƙarin ilimi zai bukaci ta ba da yawancin lokacinta ga karatu da kuma yin shiri domin wasannin guje-guje, da ƙaramin lokaci na bautar Jehobah. Menene Cherie ta yi? Ta ce, “Bayan da na yi addu’a ga Jehobah, na ƙi karɓan sukolashif ɗin kuma na fara hidima ta majagaba na kullum.” A yanzu, ta yi shekara biyar tana hidimar majagaba. “Ba ni da wani da na sani,” in ji ta. “Sanin cewa na yi shawara da ta gamsar da Jehobah ya sa ni farin ciki. A gaskiya, idan kun fara biɗan Mulkin Allah, waɗannan abu duka fa za a ƙara muku su.”—Mat. 6:33.

Halin Kirki Yana Nuna Cewa Kana da “Zuciya Mai Tsarki”

14. Me ya sa halin ka mai kyau yake da muhimmanci a idanun Jehobah?

14 Hanya ta uku da za ka nuna cewa kana bauta wa Jehobah da yardar zuciya ita ce ta wurin halin ka. Jehobah yana yi wa matasa da suke da tsabta a ɗabi’a albarka. (Karanta Zabura 24:3-5.) Matashi Sama’ila ya ƙi yin koyi da halin lalata na ’ya’yan Babban Firist Eli. An lura da halin kirki na Sama’ila. Labarin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ɗan yaro fa Sama’ila ya yi ta girma, yana da tagomashi a wurin Ubangiji duk da mutane.”—1 Sam. 2:26.

15. Menene wasu dalilai da ya sa ka riƙe hali mai kyau?

15 Muna rayuwa ne a duniya da take cike da mutane masu son kansu, masu-girman kai, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, masu-zafin hali, masu-kumbura, mafiya son annishuwa da Allah, an ambata kaɗan daga cikin halayen da Bulus ya lissafta. (2 Tim. 3:1-5) Saboda haka, zai zama ƙalubale a gare ku ku riƙe hali mai kyau duk da zama a kewaye da wannan mugun mahalli. Duk da haka, duk lokacin da ka ƙi yin abu marar kyau, kana nuna kana gefen Jehobah a kan batu na ikon mallakar dukan sararin samaniya. (Ayu. 2:3, 4) Za ka sami gamsuwa na sanin cewa kana amsa gayyatar Jehobah: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Mis. 27:11) Ƙari ga haka, sanin cewa kana da amincewar Jehobah zai ƙarfafa ka a muradinka na bauta masa.

16. Ta yaya wata ’yar’uwa ta faranta zuciyar Jehobah?

16 Sa’ad da take matashiya, wata ’yar’uwa Kirista mai suna Carol ta manne wa ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki a lokacin da take makaranta kuma an lura da halinta mai kyau. Menene ya faru? Carol ta fuskanci ba’a daga ’yan ajinta domin lamirin ta da Littafi Mai-Tsarki ya koyar ba zai ƙyale ta ta yi wasu bukukuwa na ranar hutu da kuma bukukuwa na ƙasa ba. A waɗannan lokatai, ta ƙara sami damar bayyana bangaskiyarta ga wasu. Shekaru da yawa bayan hakan, Carol ta karɓi kati daga ’yar ajinta, wadda ta rubuta: “Ina sa zuciya kullum in tuntuɓe ki kuma na gode miki. Halin ki mai kyau da kuma misalin ki na matashiya Kirista, haɗe da gaba gaɗinki game da bukukuwa, bai kasance a banza ba. Ke ce Mashaidiyar Jehobah da na fara saduwa da ita.” Misalin Carol ya shafi ’yar ajinta sosai har daga baya ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Ta rubuta a katinta zuwa ga Carol cewa ta yi fiye da shekara 40 da zama Mashaidiya mai baftisma! Kamar Carol, ku matasa a yau da kuka manne wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da gaba gaɗi za ku iya motsa masu zuciyar kirki su zo ga sanin Jehobah.

Matasa Masu Yabon Jehobah

17, 18. (a) Yaya kake ji game da matasa da ke cikin ikilisiyarku? (b) Menene ke jiran matasa masu tsoron Allah a nan gaba?

17 Dukanmu da muke ƙungiyar Jehobah na dukan duniya muna murnar ganin dubban matasa masu yawa waɗanda suke yin bauta ta gaskiya! Waɗannan matasa suna ƙarfafa muradinsu na yi wa Jehobah sujjada ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki kullum, yin addu’a, da kuma nuna halin da ya jitu da nufin Jehobah. Irin misalin waɗannan matasa abin farin ciki ne ga iyayensu da kuma ga dukan mutanen Jehobah. —Mis. 23:24, 25.

18 A nan gaba, matasa masu aminci za su kasance cikin waɗanda za su tsira zuwa sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. (R. Yoh. 7:9, 14) A wurin, za su more albarka masu yawa yayin da suka ci gaba da nuna godiya ga Jehobah, kuma za su iya yabonsa har abada.—Zab. 148:12, 13.

Za Ka Iya Ba da Bayani?

• Ta yaya matasa za su sa hannu a cikin sujjada ta gaskiya a yau?

• Don ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki, me ya sa bimbini ke da muhimmanci?

• Ta yaya addu’a take taimaka maka ka matso kusa ga Jehobah?

• Me ake cim ma ta wurin hali mai kyau na Kirista?

[Hoton da ke shafi na 5]

Kana karanta Littafi Mai Tsarki Kullum?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba