Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 9/15 pp. 3-6
  • Addini Zaɓi Na ne Ko na Iyaye Na?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Addini Zaɓi Na ne Ko na Iyaye Na?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Hakkin Yara
  • Hakkin Iyaye
  • Hakkin Ikilisiya
  • Zaɓinka
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Matasa, Ku Zaɓi Ku Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 9/15 pp. 3-6

Addini Zaɓi Na ne Ko na Iyaye Na?

A ƘASAR Poland mutane da yawa suna gaya wa Shaidun Jehobah, “An haife ni a cikin wannan addinin, kuma a cikinta zan mutu.” Hakan yana nufin cewa, a ra’ayinsu mutane suna gadon addini ne daga tsara zuwa tsara. Mutane suna da irin wannan ra’ayin game da addini a yankin ku? Menene sakamakon kasancewa da irin wannan ra’ayin? Kamar dai addini ya zama abin yi ne kawai da kuma al’adar iyali. Hakan zai iya faruwa ne ga Shaidun Jehobah da suka koyi gaskiya daga iyayensu ko kakaninsu kuwa?

Hakan bai shafi Timoti ba, wanda mahaifiyarsa da kakarsa masu ibada suka yi masa ja-gora ya yi imani da Allah na gaskiya kuma ya ƙaunace shi. Timoti ya san littattafai masu tsarki tun yana “jariri.” Da shigewar lokaci, tare da mahaifiyarsa da kakarsa, Timoti ya gamsu cewa Kiristanci shi ne gaskiya. An ‘tabbatar’ masa abin da ya ji daga Nassosi game da Yesu Kristi. (2 Tim. 1:5; 3:14, 15) Saboda haka, ko da yake iyaye Kiristoci a yau suna iyakar ƙoƙarinsu su taimaka wa yaransu su zama bayin Jehobah, yaran da kansu suna bukatar su yi sha’awar bauta wa Jehobah.—Mar. 8:34.

Dole ne a tabbatar da kowannensu ya gaskata ta wurin tattaunawa da shi idan ana son ya bauta wa Jehobah cikin ƙauna kuma ya riƙe amincinsa ko da menene ya faru. Sa’an nan bangaskiyarsa za ta yi ƙarfi kuma ta kafu sosai.—Afis. 3:17; Kol. 2:6, 7.

Hakkin Yara

“Na san cewa Shaidun Jehobah suna bin addini na gaskiya,” in ji Albert,a wanda aka yi renonsa a cikin iyalin Shaidu, “amma ya yi mini wuya na amince da abin da suke faɗa game da yadda ya kamata na yi rayuwa.” Idan kai matashi ne, wataƙila kana da irin wannan ra’ayin. Idan haka ne, ka yi ƙoƙari ka fahimci abin da hanyar rayuwar da Allah yake son mu bi ta ƙunsa kuma ka yi farin ciki yin nufinsa. (Zab. 40:8) “Na soma yin addu’a,” in ji Albert. “Da farko ya yi mini wuya. Na tilasta wa kaina na yi addu’a. Amma, ba da daɗewa ba, na ga cewa zan iya kasancewa da daraja a gaban Allah idan na yi ƙoƙarin yin abin da yake da kyau. Hakan ya ƙarfafa ni na yi canje-canje da nake bukatar na yi.” Ta wajen ƙulla dangantaka da Jehobah, za ka iya kasancewa da sha’awar yin abin da yake bukata a gare mu.—Zab. 25:14; Yaƙ. 4:8.

Ka yi tunanin wasan da kake yi, kamar wasan kwallo ko kuma wani dabam. Idan ba ka san dokokin yin wasan ba ko kuma ba za ka iya yin sa ba sosai, ba za ka ji daɗin yin wasan ba. Amma, idan ka koyi dokokin kuma ka soma yin wasan da kyau, za ka riƙa marmarin yin wasan kuma ka nemi zarafin yin sa, ko ba haka ba? Haka ayyukan Kiristoci na gaskiya suke. Saboda haka, ka riƙa yin shiri domin tarurrukan Kirista. Ka yi kalami. Ko da menene shekarunka, kana iya ƙarfafa wasu ta wurin misalinka!—Ibran. 10:24, 25.

Hakan yake game da gaya wa mutane game da imaninka. Ya kamata ka yi wannan ma cikin ƙauna, ba don tilas ba. Ka tambayi kanka: “Me ya sa nake son na gaya wa mutane game da Jehobah? Waɗanne dalilai nake da su na ƙaunarsa?’ Kana bukatar ka san Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna. Ya faɗa ta bakin Irmiya: “Za ku neme ni, ku same ni kuma, lokacin da ku ke nemana da zuciya ɗaya.” (Irm. 29:13, 14) Menene hakan yake bukata a gare ka? “Na canja ra’ayi na,” in ji Jakub. “Ina halartan taro kuma ina fita hidimar fage tun ina yaro, amma ina yin waɗannan ayyuka kawai ne. Sai lokacin da na san Jehobah da kyau kuma na ƙulla dangantaka na kud da kud da shi ne na soma bin gaskiya sosai.”

Cuɗanya mai kyau kuma mai ƙarfafawa za ta taimake ka sosai ka ji daɗin hidimarka. Hurarren misali ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.” (Mis. 13:20) Saboda haka, ka nemi yin abokantaka da waɗanda suke biɗan makasudai na ruhaniya kuma suna farin cikin bauta wa Jehobah. Jola ta ce: “Yin tarayya da matasa da yawa da suke mai da hankalinsu ga hidimar Jehobah ya ƙarfafa ni. Na soma fita hidimar fage a kai a kai cike da farin ciki.”

Hakkin Iyaye

“Ina godiya sosai ga iyaye na domin sun koya mini game da Jehobah” in ji Jola. Hakika, iyaye suna iya yin tasiri sosai a kan zaɓin yaransu. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku ubanni, . . . ku goye [yaranku] cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Wannan hurarren gargaɗi ya nuna sarai cewa hakkin iyaye shi ne su koya wa yaransu hanyoyin Jehobah, ba nasu hanyoyin ba. Maimakon ku cusa abin da kuke so cim ma wa a cikin zuciyar yaranku, zai fi kyau ku taimake su su kafa makasudin yin rayuwar da ta jitu da manufofin Jehobah a rayuwar su!

Kuna iya nanata wa yaranku kalmomin Jehobah kuma ku ‘riƙa faɗinsu sa’ad da kuke zaune cikin gidanku, da sa’an da kuke tafiya a kan hanya, da sa’ad da kuke kwanciya, da sa’ad da ku ka tashi.’ (K. Sha 6:6, 7) “Muna tattaunawa sosai game da fannoni dabam-dabam na hidima ta cikakken lokaci,” in ji Ewa da Ryszard, iyayen yara maza uku. Menene sakamakon hakan? “Yaran suna son su shiga Makarantar Hidima ta Allah tun suna ƙananan yara, suna so su zama masu shela, kuma daga baya suka tsai da shawara da kansu su yi baftisma. Bayan hakan, dukan su suka soma hidima ta cikakken lokaci.”

Misali mai kyau na iyaye yana da muhimmanci. Ryszard ya ce, “Mun ƙuduri aniyar cewa ba za mu yi rayuwar da ta saɓa da gaskiya ba, mu aikata dabam a gida kuma aikata dabam a cikin ikilisiya.” Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘Menene yara na suke gani a rayuwata? Suna ganin cewa ina ƙaunar Jehobah sosai? Suna ganin wannan ƙaunar sa’ad da nake addu’a da kuma yin nazari na kaina? Suna ganin hakan a halin da nake nuna wa game da hidimar fage, nishaɗi, da abubuwan mallaka da kuma abubuwan da nake cewa game da waɗanda suke cikin ikilisiya?’ (Luk 6:40) Yara za su lura da rayuwarka ta yau da kullum kuma za su fahimci abubuwa da ba su jitu ba tsakanin abubuwan da kake cewa da kuma abubuwan da kake yi.

Horo yana da muhimmanci wajen renon yara. Amma, hurarriyar Kalmar Allah ta gaya mana cewa ‘ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa.’ (Mis. 22:6) Ewa da Ryszard sun ce, “Muna ba da lokaci mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kowanne cikin yaran.” Hakika, iyaye ne za su tsai da shawara ko za su yi nazari da kowanne yaro. Koma menene yanayin, ya kamata a bi da kowane yaro a matsayin mutumi dabam. Hakan yana bukatan daidaituwa da sanin ya kamata. Alal misali, maimakon ku gaya wa yaranku cewa wasu waƙoƙi ba su da kyau, zai fi kyau ku nuna musu yadda za su tsai da shawarwari masu kyau da kuma yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka shafi batun.

Yaranku suna iya sanin ainihin abin da kuke son su yi kuma su yi hakan. Duk da haka, kuna bukatan ku motsa zuciyarsu. Ku tuna, “shawara a cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai-zurfi: amma mutum mai-fahimi za ya jawo ta.” (Mis. 20:5) Ku zama masu fahimi, ku nemi alamun kowace matsala da ke ɓoye a cikin zuciyar yaranku, kuma ku ɗauki mataki nan da nan. Ba tare da yin wani zargi ba, ku nuna cewa kun damu da su, kuma ku yi musu tambayoyin da suka dace. Duk da haka, ku mai da hankali kada ku riƙa yin tambayoyi masu yawa. Damuwa ta gaske da kuke nunawa za ta motsa zuciyarsu kuma ta taimake ku ku taimake su.

Hakkin Ikilisiya

A matsayinka na bawan Allah za ka iya taimaka wa matasa da ke cikin ikilisiya su daraja gadō na ruhaniya da suke da shi? Ko da yake hakkin iyaye ne su koyar da yaransu, waɗanda suke cikin ikilisiya, musamman dattawa suna iya tallafa wa ƙoƙarce-ƙoƙarcen su. Yana da muhimmanci ku taimaki iyalan da ɗaya daga cikin iyayen ba Mashaidin Jehobah ba ne.

Menene dattawa za su yi don su taimaki matasa su ƙaunaci Jehobah kuma su ji cewa ana bukatarsu kuma ana daraja su? Mariusz, wanda dattijo ne a cikin wata ikilisiya a ƙasar Poland, ya ce: “Ya kamata dattawa su riƙa tattaunawa da matasa. Ba wai za su yi hakan ba ne ba kawai sa’ad da matsaloli suka taso amma a wasu lokatai kuma kamar a hidimar fage, bayan an tashi taro, ko kuma a lokacin da aka zauna ana hira.” Me ya sa ba za ku tambayi matasa yadda suke ji game da ikilisiya ba? Irin wannan tattaunawar tana sa matasa su kusaci ikilisiya kuma tana sa su ji cewa su sashe ne na ikilisiyar.

Idan kai dattijo ne, kana ƙoƙarin ka san matasan da ke cikin ikilisiyarku? Ko da yake a yanzu shi dattijo ne, Albert da aka ambata ɗazu, ya fuskanci jarrabobi dabam-dabam a lokacin ƙuruciyarsa. Ya ce, “Sa’ad da nake matashi, ina bukatan ziyarar ƙarfafawa.” Dattawa suna iya nuna sun damu da matasa ta wajen yin addu’a su yi nasara wajen bauta wa Jehobah su kuma ƙulla dangantaka na kud da kud da shi.—2 Tim. 1:3.

Yana da kyau matasa su sa hannu a ayyukan ikilisiya. Idan ba haka ba, suna iya mai da hankali wajen biɗar makasudai na duniya. Ku tsofaffi za ku iya fita hidimar fage tare da su kuma ku zama abokin su? Ku zauna ku yi nishaɗi da matasa, kuma ku sa su amince da ku kuma su zama abokanku. Jola ta tuna: “Wata ’yar’uwa majagaba ta nuna tana ƙaunata. Da ita ce na fita hidimar fage a lokaci na farko don ina son na yi hakan.”

Zaɓinka

Matasa, ku tambayi kanku: ‘Menene makasudai na? Idan ban yi baftisma ba, ina da makasudin yin baftisma?’ Tsai da shawarar yin baftisma ya kamata ya fito ne daga zuciyar da ke cike da ƙauna ga Jehobah, ba wai don iyayen ku ko addini ba.

Bari Jehobah ya zama Abokinka na gaskiya, kuma ka ɗauki gaskiya da tamani. Jehobah ya sanar ta bakin annabi Ishaya: “Kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka.” Jehobah zai kasance tare da kai muddin kai abokinsa ne. Zai ƙarfafa ka kuma ya ‘taimake ka, ya riƙe ka da hannun damansa na adalci.’—Isha. 41:10.

[Ƙarin bayani]

a An canja wasu sunaye.

[Hoto a shafi na 4]

Ka yi ƙoƙari ka san abin da ke cikin zuciyar yaronka

[Hoto a shafi na 6]

Tsai da shawara na yin baftisma ya kamata ya fito ne daga zuciyar da ke cike da ƙauna ga Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba