Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 1/15 pp. 17-21
  • Ka Yi Zaɓi Mai Kyau a Ƙuruciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Zaɓi Mai Kyau a Ƙuruciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ZAƁI MAFI MUHIMMANCI
  • MENE NE ZA KA YI A ƘURUCIYARKA?
  • ƘA’IDODIN NASSI UKU DA ZA SU JA-GORANCE KA
  • YIN AMFANI DA ƘA’IDODIN NASSI WAJEN YIN ZAƁI MAI KYAU
  • KA JI DAƊIN ƘURUCIYARKA A MATSAYIN KIRISTA
  • Za Su Bauta wa Jehobah Kuwa Sa’ad da Suka Yi Girma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • “Ya Sa Dukan Shirye-Shiryenka Su Yi Nasara”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 1/15 pp. 17-21

Ka Yi Zaɓi Mai Kyau a Ƙuruciyarka

‘Samari da ’yan mata; . . . ku yabi sunan Ubangiji.’—ZAB. 148:12, 13.

ZA KA IYA BAYYANAWA?

  • Mene ne matasa za su iya yi yanzu don su ji daɗin bauta wa Jehobah a nan gaba?

  • Ta yaya wasu suka ji daɗin yin amfani da ƙuruciyarsu don bauta wa Jehobah?

  • Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau?

1. Wane zarafi mai ban sha’awa ne matasa da yawa suke jin daɗinsa?

MUNA zama a zamani mai muhimmanci sosai. Miliyoyin mutane daga dukan al’ummai suna bauta wa Jehobah yanzu fiye da dā. (R. Yoh. 7:9, 10) Matasa da yawa suna jin daɗin hidima sosai yayin da suke taimaka wa mutane su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki da za ta sa su sami ceto. (R. Yoh. 22:17) Waɗannan matasan suna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kuma suna taimaka musu su kyautata rayuwarsu. Wasu kuma suna zuwa ƙasashen da ake harsuna dabam don yin shelar bishara. (Zab. 110:3; Isha. 52:7) Mene ne ya wajaba ka yi idan kana so ka yi irin wannan aiki mai armashi?

2. Ta yaya misalin Timotawus ya nuna cewa Jehobah yana so ya danƙa wa matasa gata? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

2 A matsayin matashi, za ka iya ɗaukan matakai da za su sa ka sami zarafin jin daɗin yi wa Jehobah hidima a nan gaba. Alal misali, Timotawus ya tsai da shawara mai kyau kuma hakan ya sa aka naɗa shi a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje sa’ad da ya kusan kai shekara ashirin ko ya ɗan ɗara hakan. (A. M. 16:1-3) Wataƙila bayan ’yan watanni da aka tsananta wa ’yan’uwan da ke Tasalonika ne manzo Bulus ya tura shi zuwa sabuwar ikilisiyar da aka kafa a birnin. ’Yan tawaye sun tilasta wa Bulus ya bar birnin, amma ya san cewa Timotawus zai ƙarfafa ’yan’uwan da ke wurin. (A. M. 17:5-15; 1 Tas. 3:1, 2, 6) Ka yi tunanin yadda Timotawus ya ji sa’ad da aka danƙa masa wannan gatan!

ZAƁI MAFI MUHIMMANCI

3. Wane zaɓi mafi muhimmanci ne za ka iya yi a rayuwarka, kuma yaushe ne ya kamata ka yi wannan zaɓin?

3 A lokacin ƙuruciya ne ake yin zaɓi masu muhimmanci. Amma, akwai zaɓin da ya fi muhimmanci sosai, wato zaɓin bauta wa Jehobah. A wane lokacin ne ya fi dacewa ka yi wannan zaɓin? Jehobah ya ce: “Ka tuna da Mahaliccinka . . . a cikin kwanakin ƙuruciyarka.” (M. Wa. 12:1) Hanya ɗaya kawai da za mu iya “tuna” da Jehobah ita ce ta bauta masa da dukan zuciyarmu. (K. Sha 10:12) Wannan ita ce shawara mafi muhimmanci da za ka yi. Za ta shafe ka yanzu da kuma a nan gaba.—Zab. 71:5.

4. Waɗanne shawarwari ne za su shafi yadda kake bauta wa Allah?

4 Hakika, ba bauta wa Jehobah ba ne kaɗai zaɓin da zai shafi rayuwarka a nan gaba. Wataƙila za ka so ka yanke shawarar yin aure da kuma macen da za ka aura da aikin da za ka yi. Waɗannan shawarwari masu amfani ne, amma wajibi ne ka yi shawara ko za ka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya tukuna. (K. Sha 30:19, 20) Me ya sa? Domin waɗannan matakan suna da alaƙa da juna. Shawarar da ka tsai da game da aure da kuma aiki, za su shafi yadda kake bauta wa Allah. (Duba Luka 14:16-20.) Hakazalika, idan ka yi shawarar bauta wa Jehobah, hakan zai shafi zaɓin da za ka yi game da aure da kuma aiki. Saboda haka, ka yanke shawara a kan abin da zai fi muhimmanci a rayuwarka.—Filib. 1:10.

MENE NE ZA KA YI A ƘURUCIYARKA?

5, 6. Ka ba da labarin da ya nuna cewa yin zaɓi mai kyau zai sa a ji daɗin rayuwa a nan gaba. (Ka kuma duba talifin nan, “Zaɓin da Na Yi Sa’ad da Nake Yaro” a shafi na 32.)

5 Da zarar ka tsai da shawarar bauta wa Jehobah, za ka iya sanin abin da yake so ka yi, kuma za ka iya yanke shawara a kan yadda za ka bauta masa. Wani ɗan’uwa daga Japan ya ce: “Sa’ad da nake ɗan shekara 14, na fita wa’azi da wani dattijo a ikilisiya da ya lura cewa ba na jin daɗin wa’azin. A hankali ya ce mini: ‘Yuichiro, ka koma gida. Ka zauna ka yi tunani a kan alherin da Jehobah ya yi maka.’ Na yi abin da ya gaya mini. Hakika, na ci gaba da yin tunanin da kuma addu’a har wasu ’yan kwanaki. A hankali, sai ra’ayina ya canja. Ba da daɗewa ba, na soma jin daɗin bauta wa Jehobah. Ina jin daɗin karanta labarin masu wa’azi a ƙasashen waje kuma hakan ya sa na soma tunanin kyautata ibadata ga Jehobah.

6 Yuichiro ya daɗa cewa: “Na soma yin zaɓin da zai taimaka mini in bauta wa Jehobah a ƙasar waje. Alal misali, na soma koyon Turanci a makaranta. Sa’ad da na gama makarantar, na nemi aikin koyar da Turanci, wato aikin da zai ba ni damar yin hidimar majagaba. Sa’ad da nake ɗan shekara 20, na soma koyon yaren Mongolia kuma na sami zarafin ziyartar wani rukunin da ke yaren. Shekara biyu bayan haka, wato a shekara ta 2007, sai na je ƙasar Mongolia. Sa’ad da na fita wa’azi da wasu majagaba kuma na ga cewa mutane da yawa suna so su san gaskiya, hakan ya sa na soma tunanin ƙaura don in taimaka. Na komo Japan don na yi shiri. A yanzu, ina hidimar majagaba a ƙasar Mongolia kuma na soma wannan hidimar tun watan Afrilu na 2008. Rayuwa ba ta da sauƙi a wannan ƙasar, amma mutane suna jin bisharar kuma ina taimaka musu su san Jehobah. Na san cewa na yi zaɓi mafi muhimmanci.”

7. Waɗanne zaɓi ne za mu yi wa kanmu, kuma wani misali ne Musa ya kafa mana?

7 Wajibi ne ka tsai da shawara a kan yadda za ka yi amfani da rayuwarka wajen bauta wa Jehobah. (Josh. 24:15) Ba za mu iya tsai da maka shawarar yin aure ko wadda za ka aura ko kuma irin aikin da ya kamata ka yi ba. Shin za ka zaɓi aikin da ba ya bukatar horarwa sosai? Wasu cikinku suna zama a ƙauyukan da ake talauci wasu kuma a manyan birane. Halinku da iyawarku da horon da aka yi muku da abin da kuke so da kuma maƙasudanku sun bambanta sosai. Wataƙila rayuwarku ta bambanta kamar yadda rayuwar Musa ta bambanta da na sauran Ibrananiyawa matasa a ƙasar Masar a lokacin da yake matashi. A matsayin ɗan ’yar sarki, Musa yana da arziki, amma sauran matasa Ibraniyawa bayi ne. (Fit. 1:13, 14; A. M. 7:21, 22) Kamar kai, sun yi rayuwa a zamani mai muhimmanci. (Fit. 19:4-6) Amma, kowannensu yana bukatar ya yanke shawara a kan ko zai bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Musa ya tsai da shawarar da ta dace.—Karanta Ibraniyawa 11:24-27.

8. Me zai iya taimaka maka ka yi zaɓi mai kyau?

8 Jehobah yana taimaka maka ka yi zaɓi mai kyau a ƙuruciyarka. Ta yaya yake yin hakan? Yana koya maka ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka a kowane irin yanayi da ka sami kanka. (Zab. 32:8) Ƙari ga hakan, iyayenka da Shaidu ne da kuma dattawan ikilisiya za su iya taimakon ka ka yi tunani a kan yadda za ka yi amfani da waɗannan ƙa’idodin. (Mis. 1:8, 9) Bari mu tattauna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki guda uku da za su taimaka maka ka yi zaɓi masu kyau da za su amfane ka a nan gaba.

ƘA’IDODIN NASSI UKU DA ZA SU JA-GORANCE KA

9. (a) Ta yaya Jehobah ya daraja mu ta wajen ba mu ’yancin yin zaɓi? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka ‘fara biɗan Mulkin’?

9 Ku fara biɗan Mulkin Allah da kuma adalcinsa. (Karanta Matta 6:19-21, 24-26, 31-34.) Jehobah ya daraja mu da ya ba mu ’yancin yin zaɓi. Bai ce lallai sai mun yi amfani da dukan lokacinmu muna wa’azi ba. Amma, Yesu ya koya mana muhimmancin fara biɗan Mulkin Allah. Sa’ad da ka fara biɗan Mulkin, za ka sami zarafin nuna ƙaunarka ga Allah da maƙwabtanka kuma za ka iya nuna godiyarka ga begen yin rayuwa har abada. Shin shawarar da kake so ka tsai da game da aure da kuma aiki za ta nuna cewa ka damu da abin duniya ne fiye da “fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa”?

10. Mene ne ya sa Yesu farin ciki, kuma waɗanne irin zaɓi ne za su sa ka farin ciki?

10 Ka yi wa wasu hidima da farin ciki. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:20, 21, 24, 35.) Wannan ƙa’ida mai muhimmanci ce a rayuwa. Yesu ma ya san da hakan, shi ya sa ya bauta wa Ubansa ta yin nufinsa kuma ya yi wa wasu hidima ta wajen koyar da su game da bishara. Babu shakka, hakan ya sa shi farin ciki. (Luk 10:21; Yoh. 4:34) Wataƙila ka taɓa yin irin wannan farin cikin sa’ad da ka taimaka wa wasu. Idan zaɓin da ka yi ya jitu da ƙa’idar da Yesu ya koyar, hakika za ka yi farin ciki kuma Jehobah ma zai yi hakan.—Mis. 27:11.

11. Me ya sa Baruch ya daina farin ciki, kuma wane gargaɗi ne Jehobah ya ba shi?

11 Abin da ke fi sa mu farin ciki shi ne bauta wa Jehobah. (Mis. 16:20) Wataƙila Baruch, wato sakataren Irmiya, ya mance da hakan. Akwai wani lokacin da ya daina jin daɗin hidimar da yake yi wa Jehobah. Saboda hakan, Jehobah ya gaya masa cewa: “Kana fa biɗa wa kanka manyan abu? kada ka biɗe su: gama, ga shi, zan jawo mugunta a bisa dukan masu-rai, . . . amma zan ba ka naka rai ganima gareka, dukan wuraren da ka tafi.” (Irm. 45:3, 5) Shin mene ne zai sa Baruch farin ciki? Shin zai yi abin da yake so kuma daga baya a halaka shi ne, ko kuwa zai yi nufin Jehobah kuma ya rayu sa’ad da aka halaka Urushalima?—Yaƙ. 1:12.

12. Wane zaɓi ne Ramiro ya yi da ya sa shi farin ciki?

12 Wani ɗan’uwa mai suna Ramiro ya yi farin cikin taimaka wa mutane. Ya ce: “An haife ni a wani ƙauye a ƙasar Bolivia kuma iyayena talakawa ne. Ina da zarafin zuwa jami’a sa’ad da yayana ya ce zai biya mini kuɗin makaranta. Amma a lokacin, ban daɗe da yin baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah ba kuma wani majagaba ya ce mu ƙaura zuwa wani gari don yin wa’azi. Na ƙaura zuwa wurin, sai na koyi yin aski kuma daga baya na buɗe nawa shagon aski don na tallafa wa kaina. Mutane da yawa a wannan garin sun yarda a yi Nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Bayan wasu lokatai, sai na soma halartar wata sabuwar ikilisiyar yare da aka kafa. Yanzu na yi hidima ta cikakken lokaci na tsawon shekara goma a wannan yankin. Babu wani aiki da zai sa ni farin ciki kamar taimaka wa mutane su koyi Littafi Mai Tsarki a yaren su.”

13. Me ya sa ya dace ka bauta wa Jehobah sosai a ƙuruciyarka?

13 Ka ji daɗin bauta wa Jehobah a ƙuruciyarka. (Karanta Mai-Wa’azi 12:1.) Kada ka ji cewa wajibi ka sami aiki mai kyau kafin ka soma hidimar majagaba. Yanzu ne lokaci mafi kyau da za ka soma bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka. Matasa da yawa ba su da hakki sosai a iyalinsu kuma suna da ƙarfin jure ƙalubalen yin hidima. Mene ne za ka so yi wa Jehobah a ƙuruciyarka? Wataƙila maƙasudinka shi ne ka zama majagaba kuma mai yiwuwa ka so yin wa’azi a wasu yankunan da ake wasu yaruka dabam. Ƙila ka so faɗaɗa hidimarka a ikilisiyar da kake. Ko da wane irin maƙasudi ne kake da shi, kana bukatar ka soma wata sana’a don biyan bukatunka. Ka tambayi kanka: ‘Wace sana’a ce zan zaɓa? Shin koyon wannan sana’ar za ta ci mini lokaci sosai?’

YIN AMFANI DA ƘA’IDODIN NASSI WAJEN YIN ZAƁI MAI KYAU

14. Mene ne ya wajaba ka mai da wa hankali sa’ad da kake neman aiki?

14 Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da muka tattauna za su taimake ka ka yi zaɓi mai kyau a irin sana’ar da kake so ka koya. Wataƙila za ka iya samun bayani a kan irin sana’o’in da ke da sauƙin samu a yankinka ko kuma a yankin da kake so ka yi hidima daga wurin malaman makarantarka ko wasu da ka sani ko kuma jaridu. Wataƙila waɗannan mutanen za su iya taimaka maka, amma ka yi hattara domin ba sa bauta wa Jehobah kuma za su iya sa ka soma son abin duniya. (1 Yoh. 2:15-17) Ka tuna cewa zuciyarka za ta iya yaudararka idan ka soma mai da hankali ga abin duniya.—Karanta Misalai 14:15; Irm. 17:9.

15, 16. Wane ne zai iya ba ka shawara mai kyau game da neman sana’a?

15 Da zarar ka san waɗannan sana’o’in, za ka bukaci shawara mai kyau. (Mis. 1:5) Wane ne zai iya taimaka maka ka yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don zaɓan sana’ar da ta dace? Ka saurari mutanen da suke ƙaunar Jehobah, suke ƙaunarka, kuma suka san ka da yanayinka sosai. Za su taimake ka ka yi tunani da kanka a kan abin da za ka iya yi da kuma abin da kake so ka yi. Wataƙila abin da za su faɗa zai sa ka sake tunani game da maƙasudanka. Idan iyayenka suna bauta wa Jehobah, za su iya taimaka maka sosai. Kuma dattawan ikilisiyarku za su ba ka shawara mai kyau. Ka tambayi majagaba da kuma masu kula masu ziyara abin da ya sa suka soma hidima ta cikakken lokaci. Ta yaya suka soma hidimar? Wane irin sana’a ne suke yi? Wane albarka ne suka samu?—Mis. 15:22.

16 Waɗanda suka san ka sosai za su iya ba ka shawara mai kyau. Alal misali, a ce kana so ka daina zuwa makarantar sakandare kuma ka zama majagaba don kawai ka guje wa ayyuka masu wuya da ake yi a makaranta. Wataƙila mutumin da ke ƙaunarka zai fahimci dalilin da ya sa kake so ka bar makaranta. Zai iya taimaka maka ka fahimci cewa jurewa a makaranta zai iya sa kada ka yi sanyin gwiwa nan da nan. Irin wannan halin ne kake bukata idan kana so ka bauta wa Jehobah har abada.—Zab. 141:5; Mis. 6:6-10.

17. Wace irin sana’a ce ya kamata mu ƙi yi?

17 Duk wanda ke bauta wa Jehobah zai fuskanci yanayin da zai iya raunana bangaskiyarsa kuma hakan zai sa ya daina bauta masa. (1 Kor. 15:33; Kol. 2:8) Wasu sana’o’in za su iya raunana bangaskiyarka. Wataƙila ka lura cewa wasu “sun lalace ga wajen imani” sanadin irin sana’a ko kuma aikin da suke yi. (1 Tim. 1:19) Zai dace ka ƙi zaɓan aiki ko sana’ar da za su ɓata dangantakarka da Jehobah.—Mis. 22:3.

KA JI DAƊIN ƘURUCIYARKA A MATSAYIN KIRISTA

18, 19. Mene ne ya kamata ka yi idan ba ka marmarin bauta wa Jehobah yanzu?

18 Idan kana so ka bauta wa Jehobah, ka yi amfani da zarafin da ya ba ka yayin da kake ƙuruciya. Yanzu ne lokacin da za ka yi zaɓin da zai taimaka maka ka ji daɗin bauta wa Jehobah.—Zab. 148:12, 13.

19 Idan har yanzu ba ka marmarin bauta wa Jehobah yadda ya kamata fa? Kada ka ja da baya wajen ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Bayan manzo Bulus ya bayyana abin da ya yi don Jehobah ya albarkace shi, ya ce: “In kuwa game da wani abu ra’ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma. Sai dai duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.” (Filib. 3:15, 16, Littafi Mai Tsarki) Ka tuna cewa Jehobah yana ƙaunarka kuma shawararsa ce ta fi. Ka bari ya taimake ka ka tsai da shawara mai kyau yanzu, wato a ƙuruciyarka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba