Jehobah Yana Dubanmu Don Amfaninmu
“Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.”—2 LABA. 16:9.
1. Me ya sa Jehobah yake bincika mu?
JEHOBAH Uba ne kamiltacce. Ya san mu sosai har ya san ‘siffofin tunaninmu.’ (1 Laba. 28:9) Amma, ba ya bincika mu don ya ga laifinmu. (Zab. 11:4; 130:3) Maimakon haka, yana kāre mu daga duk wani abu da zai lalata dangantakarmu da shi ko kuma gatanmu na samun rai na har abada.—Zab. 25:8-10, 12, 13.
2. Su wanene Jehobah yake nuna ƙarfinsa dominsu?
2 Jehobah maɗaukaki ne kuma yana ganin kome. Don haka, yana taimakon ƙaunatattunsa a duk lokacin da suka nemi taimakonsa, kuma yana taimakonsu a lokacin da suke fuskantar jarrabobi. 2 Labarbaru 16:9 ta ce: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” Ka lura cewa Jehobah yana amfani da ƙarfinsa don waɗanda suke bauta masa da zuciya ɗaya, zuciyar da take da tsarki kuma marar son kai. Ba ruwansa da waɗanda suke yaudarar mutane ko kuma munafukai.—Josh. 7:1, 20, 21, 25; Mis. 1:23-33.
Ka Yi Tafiya da Allah
3, 4. Mecece “tafiya tare da Allah,” take nufi kuma waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki ne suka taimake mu mu fahimci hakan?
3 Ga mutane da yawa, ba zai yiwu Mahaliccin dukan sararin samaniya ya yarda mutane su yi tafiya da shi a ruhaniya ba. Amma, abin da Jehobah yake so mu yi ke nan. A zamanin dā, Anuhu da Nuhu sun yi “tafiya tare da Allah.” (Far. 5:24; 6:9) Musa ya “jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Ibran. 11:27) Sarki Dauda ya ƙasƙantar da kansa don ya yi tafiya tare da Ubansa na samaniya. Ya ce: Domin ‘Jehobah yana hannun damana ba zan jijjigu ba.’—Zab. 16:8.
4 Hakika, ba za ba mu iya riƙe hannun Jehobah mu yi tafiya tare da shi ba a zahiri. Amma za mu iya yin haka a ruhaniya. Ta yaya? Mai zabura Asaph ya rubuta: “Kullum ina tare da kai: ka riƙe ni a hannuna na dama. Za ka bishe ni da shawararka.” (Zab. 73:23, 24) Muna tafiya tare da Jehobah idan muka bi umurninsa da muke samu a cikin Kalmarsa da aka rubuta da kuma ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”—Mat. 24:45; 2 Tim. 3:16.
5. Ta yaya ne Jehobah yake kula da ƙaunatattunsa, kuma yaya ya kamata mu ɗauke shi?
5 Saboda Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke tafiya tare da shi, yana kula da su kamar Uba mai ƙauna, yana kāre su, kuma yana koyar da su. Allah ya ce: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” (Zab. 32:8) Ka tambayi kanka: ‘Ina tafiya tare da Jehobah, kuma ina bin umurninsa da sanin cewa yana kallo na? Sanin cewa yana tare da ni yana ja-gorar tunanina, kalamai na, da kuma ayyukana kuwa? Idan na yi kuskure, ina fahimtar cewa Jehobah ba Allah mai tsanantawa ba ne, amma Uba ne mai kula kuma mai jin ƙai da yake so ya taimaki waɗanda suka tuba suka dawo gare shi?’—Zab. 51:17.
6. Ta yaya ne Jehobah ya fi iyaye na zahiri?
6 A wani lokaci, Jehobah yakan taimake mu kafin mu bi tafarki da bai dace ba. Alal misali, zai ga cewa zuciyarmu mai rikici tana sa mu soma sha’awar abubuwan da ba su dace ba. (Irm. 17:9) A irin wannan yanayi, zai ɗauki mataki da sauri fiye da iyaye na zahiri saboda “idanunsa” suna iya ganin zuciyarmu, kuma su bincika tunaninmu. (Zab. 11:4; 139:4; Irm. 17:10) Ka yi la’akari da abin da ya faru da Baruch, sakataren Irmiya kuma amininsa.
Uba na Gaskiya Ga Baruch
7, 8. (a) Wanene Baruch, kuma wace sha’awa ce da ba ta dace ba ya soma yi? (b) Ta yaya ne Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar Baruch?
7 Baruch marubuci ne da ya yi hidima tare da Irmiya a wani aiki mai wuya da aka ba shi na sanar da saƙon hukunci a Yahuda. (Irm. 1:18, 19) A wani lokaci, Baruch da ya fito daga wani sanannen iyali, ya soma biɗan “[ma kansa] manyan abu.” Sai ya bari sha’awar abin duniya ta cika zuciyarsa. Jehobah ya ga cewa wannan mugun tunanin ya soma jijiya a zuciyar Baruch. Ta wurin Irmiya, Jehobah ya daidaita batun, ya ce wa Baruch: “Ka ce, Kaitona yanzu! gama Ubangiji ya daɗa baƙinciki a kan azabata; na gaji da nishina, ban sami wani hutu ba.” Sai Allah kuma ya ce: “Kana fa biɗa ma kanka manyan abu? kada ka biɗe su.”—Irm. 45:1-5.
8 Ko da yake ya gaya wa Baruch gaskiya, Jehobah bai yi hakan da ɓacin rai ba, amma cikin ƙauna. Hakika, Allah ya ga cewa ko da yake Baruch yana da sha’awar da za ta jawo masa lahani, yana da zuciyar kirki. Jehobah ya san cewa ya kusan halaka Urushalima da Yahuda, kuma ba ya son Baruch ya yi sanyin gwiwa a wannan lokaci mai wuya. Don ya ceci bawansa, Allah ya tuna masa cewa zai “jawo mugunta a bisa dukan masu-rai,” kuma ya ce idan Baruch ya bi umurninsa, zai sami rai. (Irm. 45:5) Wato, Allah ya ce: ‘Ka lura Baruch. Ka tuna da abin da zai faru da Yahuda da Urushalima don zunubansu. Ka kasance da aminci don ka sami rai. Zan kāre ka.’ Hakika, Jehobah ya motsa zuciyar Baruch, don ya bi umurninsa kuma ya tsira daga halakar Urushalima da ta faru bayan shekara 17.
9. Ta yaya za ka amsa tambayoyin da aka yi a wannan sakin layin?
9 Sa’ad da kake tunanin labarin Baruch, ka yi la’akari da waɗannan tambayoyin da nassosin: Menene yadda Allah ya bi da Baruch ya nuna game da Jehobah da kuma ra’ayinsa game da bayinsa? (Ka karanta Ibraniyawa 12:9.) Saboda zamani mai wuya da muke ciki, menene za mu iya koya daga umurnin da Allah ya ba Baruch da kuma yadda Baruch ya bi umurnin? (Ka karanta Luka 21:34-36.) Ta wajen yin koyi da Irmiya, ta yaya dattawa Kiristoci za su iya nuna yadda Jehobah yake kula da bayinsa?—Ka karanta Galatiyawa 6:1.
Ɗan Ya Nuna Irin Ƙaunar Ubansa
10. Ta yaya aka shirya Yesu don ya yi aikinsa na Shugaban ikilisiyar Kirista?
10 Kafin zamanin Kirista, Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga mutanensa ta wurin annabawansa da kuma amintattun bayinsa. A yau, shugaban ikilisiya, Yesu Kristi, yana nuna hakan. (Afis. 1:22, 23) A littafin Ru’ya ta Yohanna, an kwatanta Yesu da Ɗan rago mai “ido bakwai, Ruhohin Allah bakwai ke nan, aikakku ne cikin dukan duniya.” (R. Yoh. 5:6) Hakika, cike da ruhu mai tsarki na Allah, Yesu yana da fahimi sosai. Shi ma yana ganin zuciyarmu kuma ya san dukan abin da ke faruwa.
11. Wane aiki ne Kristi yake yi, kuma ta yaya ne halinsa yake nuna halin Ubansa?
11 Kamar Jehobah, Yesu ba ɗan sanda da ke kallo daga sama ba ne. Yana bincika mu da idanunsa na ƙauna. Ɗaya cikin laƙabin Yesu, wato, “Uba Madawwami,” yana tuna mana da aikin da zai yi na ba wa dukan waɗanda suka gaskata da shi rai na har abada. (Isha. 9:6) Bugu da ƙari, a matsayinsa na Shugaban ikilisiyar Kirista, Kristi yana iya amfani da Kiristoci da suka manyanta, musamman ma dattawa don su ƙarfafa gajiyayyu.—1 Tas. 5:14; 2 Tim. 4:1, 2.
12. (a) Mecece wasiƙun da aka rubuta zuwa ga ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama ta nuna game da Yesu? (b) Ta yaya ne dattawa suke nuna yadda Kristi yake ɗaukan tumakin Allah?
12 Kristi ya nuna ƙaunarsa ga tumaki a wasiƙu zuwa ga dattawan ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama. (R. Yoh. 2:1–3:22) A cikin wasiƙun, Yesu ya nuna cewa ya san dukan abu da ke faruwa a cikin kowace ikilisiya kuma ya damu da mabiyansa. Haka yake ma a yau, musamman ma tun da wahayin da ke cikin Ru’ya ta Yohanna take cika a “ranar Ubangiji.”a (R. Yoh. 1:10) Dattawa da suke kula da ikilisiya suna nuna irin ƙaunar da Yesu yake yi wa mabiyansa. Yana iya amfani da waɗannan “kyautai ga mutane” su ƙarfafa ko kuma su ba da shawara a lokacin da ake bukata. (Afis. 4:8; A. M. 20:28; ka karanta Ishaya 32:1, 2.) Kana ɗaukan ƙoƙarce-ƙoƙarcen da suke yi a matsayin ƙauna da Kristi yake yi maka ne?
Taimako a Lokacin da Ya Dace
13-15. Ta yaya Allah yake zaɓan ya amsa addu’armu? Ka ba da misali.
13 Ka taɓa yin addu’a sosai don taimako kuma ka sami amsar sa’ad da Kirista da ya manyanta ya ziyarce ka kuma ya ƙarfafa ka? (Yaƙ. 5:14-16) Ko kuwa ka sami taimako ta wajen jawabi da aka ba da a taron Kirista ko kuma bayani da aka yi cikin littattafanmu? Sau da yawa Jehobah yana amsa addu’o’inmu ta waɗannan hanyoyin. Alal misali, bayan da wani dattijo ya ba da jawabi, wata ’yar’uwa da aka yi mata rashin adalci makonni kafin jawabin ta je ta same shi. Maimakon ta yi magana game da matsalarta, ta yi masa godiya don wasu bayanai na nassi da ya ba da a jawabin. Sun yi daidai da yanayinta kuma hakan ya ƙarfafata. Ta yi farin ciki sosai da ta halarci wannan taron!
14 Game da taimako da ake samu ta wurin addu’a, ka yi la’akari da misalin mutane uku da suke kurkuku da suka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke kurkuku kuma suka zama masu shela da ba su yi baftisma ba. Domin wani mugun abin da ya faru, an hana waɗanda suke kurkukun yin wasu abubuwa. Hakan ya sa suka yi tawaye. Waɗanda suke kurkukun suka tsai da shawara cewa bayan sun karya da safe, ba za su mai da kwanonin su ba don su nuna fushinsu. Waɗannan masu shela da ba su yi baftisma ba suna cikin matsala. Idan suka sa hannu cikin tawayen, za su taka dokar Jehobah da ke cikin Romawa 13:1. Idan ba su sa hannu ba, sauran waɗanda suke cikin kurkuku tare za su yi fushi da su.
15 Da yake ba su iya tattauna da juna ba, sai mutane ukun suka yi addu’a don su sami hikima. Washegari, su ukun sun yanke shawara iri ɗaya, cewa ba za su karɓi abincin safe ba. Sa’ad da masu gadin suka zo su karɓi kwanukan, mutane ukun ba su da abin da za su ba da. Sun yi farin ciki sosai cewa “mai-jin addu’a” yana kusa. (Zab. 65:2)
Yin Tunanin Rayuwa ta Nan Gaba da Gaba Gaɗi
16. Ta yaya ne aikin wa’azi ya nuna yadda Jehobah yake kula da masu kama da tumaki?
16 Wa’azin bishara a dukan duniya wani tabbaci ne da ya nuna yadda Jehobah yake ƙaunar mutane masu zuciyar kirki, a duk inda suke zama. (Far. 18:25) Sau da yawa Jehobah yana amfani da mala’ika don ya ja-goranci bayinsa zuwa wajen masu kama da tumaki, ko da suna zama a yankin da bishara ba ta kai ba. (R. Yoh. 14:6, 7) Alal misali, ta hanyar mala’ika Allah ya yi wa Filibbus ja-gora, wani mai wa’azin bishara a ƙarni na farko, ya je ya sami wani Bahabashe kuma ya bayyana masa Nassi. Menene sakamakon? Mutumin ya amince da bisharar, ya yi baftisma kuma ya zama mabiyin Yesu.b—Yoh. 10:14; A. M. 8:26-39.
17. Me ya sa ba zai yi kyau mu damu da rayuwa ta nan gaba ba?
17 Yayin da wannan zamani ta kusa kai ƙarshenta, “wahala” da aka annabta za ta ci gaba. (Mat. 24:8) Alal misali, farashin abinci zai iya ƙaruwa don mutane sun yi yawa, canjin yanayi, ko kuma tattalin arziki. Aiki zai yi wuyan samu, kuma za a matsa wa masu aiki su ba da lokaci sosai a aiki. Koma menene ya faru, waɗanda suka sa abubuwa na ruhaniya su zama na farko a rayuwarsu kuma suke yin rayuwa mai sauƙi ba za su damu ba. Sun san cewa Allah zai taimake su kuma zai kula da su. (Mat. 6:22-34) Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya kula da Irmiya a lokacin da Urushalima take cikin matsala a shekara ta 607 K.Z.
18. Ta yaya ne Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga Irmiya a lokacin da aka yi wa Urushalima barazana?
18 A ƙarshen lokacin da Babiloniyawa suka yi wa Urushalima barazana, Irmiya yana cikin kurkuku a cikin gidan Matsara. Ta yaya zai sami abinci? Da an sake shi da ya nemi abinci. Amma, ya dogara ga waɗanda suke tare da shi, wanda yawancinsu sun tsane shi. Duk da haka, Irmiya ya dogara ga Allah wanda ya yi alkawari cewa zai kula da shi ba mutane ba. Jehobah ya cika alkawarinsa kuwa? Hakika. Kowace rana, ya yi wa Irmiya tanadin “dunkulen gurasa . . . har lokacinda dukan gurasa a cikin birni ta ƙare.” (Irm. 37:21) Irmiya, Baruch, Ebed-melech, da waɗansu mutane, sun tsira daga wannan lokaci na karancin abinci, cuta, da kuma mutuwa.—Irm. 38:2; 39:15-18.
19. Sa’ad da muke jiran rayuwa ta nan gaba, wace shawara ya kamata mu tsai da?
19 Hakika, “idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci, kunnuwansa kuma suna buɗe ga jin roƙonsu.” (1 Bit. 3:12) Kana farin cikin yadda Ubanka na samaniya yake kula da kai? Kana jin cewa ba abin da zai same ka da sanin cewa yana kallonka? Ka ƙuduri aniya, ka ci gaba da tafiya tare da Allah, ko ma menene zai faru a nan gaba. Mu tabbata cewa Jehobah zai ci gaba da kula da dukan ƙaunatattunsa.—Zab. 32:8; ka karanta Ishaya 41:13.
[Hasiya]
a Ko da yake ainihi an rubuta wasiƙun don shafaffu mabiyan Kristi ne, amma suna iya shafan dukan mabiyan Allah.
b Za a iya samun wani misali na ja-gora daga samaniya a Ayukan Manzani 16:6-10. A nan, mun karanta cewa “Ruhu Mai-tsarki ya hana” Bulus da abokansa yin wa’azi a Asiya da Bithiniya. Maimakon haka, an ce su yi aiki a Makidoniya, inda mutane da yawa masu tawali’u suka amince da bishararsu.
Za Ka Iya Bayani?
• Ta yaya za mu iya nuna cewa muna “tafiya tare da Allah”?
• Ta yaya ne Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar Baruch?
• A matsayinsa na Shugaban ikilisiya, ta yaya Yesu ya nuna irin halin Ubansa?
• Ta yaya za mu iya nuna cewa muna dogara ga Allah a wannan zamani mai wuya?
[Hotuna a shafi na 9]
Kamar Irmiya da Baruch, dattawa Kiristoci a yau suna nuna irin ƙaunar da Jehobah yake yi
[Hoto a shafi na 10]
Ta yaya ne Jehobah yake taimakawa a lokacin da ya dace?