Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/1 pp. 4-6
  • Don Me Masifu Suke Faɗa wa Mutanen Kirki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Don Me Masifu Suke Faɗa wa Mutanen Kirki?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KASANCEWA A WURIN DA BAI DACE BA A LOKACIN DA BAI DACE BA
  • SHIN LAIFIN ’YAN ADAM NE?
  • KARMA CE KE JAWO WAHALA?
  • AINIHIN SANADIN
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Abin da Allah Zai Yi Game da Munanan Abubuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/1 pp. 4-6

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | DON ME MASIFU SUKE FAƊA WA MUTANEN KIRKI?

Don Me Masifu Suke Faɗa wa Mutanen Kirki?

Tun da yake Jehobaha ne Mahaliccin dukan abubuwa da kuma mai iko duka, mutane da yawa suna saurin ɗora masa alhakin kome da ke faruwa a duniya, har da munanan abubuwa. Amma, ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Allah na gaskiya:

  • ‘Ubangiji mai-adalci ne cikin dukan . . . ayyukansa.’—Zabura 145:17.

  • ‘Dukan tafarkun [Allah] shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.’—Kubawar Shari’a 32:4.

  • ‘Ubangiji . . . [yana] cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.’—Yaƙub 5:11.

Allah ba ya sa munanan abubuwa su faru. Amma, yana zuga wasu su aikata munanan abubuwa ne? Sam! Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Kada kowa sa’ad da ya jarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu.’ Don me? Domin “Allah ba ya jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba ya jarabtan kowa.” (Yaƙub 1:13) Allah ba ya jarabtar mutane ta wajen zuga su su yi abin da bai da kyau. Haka ma, Allah ba ya jawo masifu kuma ba ya sa wasu su yi mugunta. To mene ne ko kuma wane ne ke da alhakin?

KASANCEWA A WURIN DA BAI DACE BA A LOKACIN DA BAI DACE BA

Littafi Mai Tsarki ya bayyana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa mutane suke shan wahala. Ya ce: “Sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.” (Mai-Wa’azi 9:11, Littafi Mai Tsarki) Sa’ad da abubuwa na ba-zato ko haɗarurruka suka faru, hakan yana shafan mutanen da ke wurin. Kusan shekaru 2,000 da suka gabata, Yesu Kristi ya yi maganar wani bala’i da ya auko wa mutane 18 da suka mutu sa’ad da wata hasumiya ta rusa da su. (Luka 13:1-5) Wannan tsautsayin bai auko musu domin irin rayuwarsu ba, amma hakan ya shafe su ne don suna cikin ginin sa’ad da abin ya faru. A shekara ta 2012, an yi wata mummunar ambaliyar ruwa da ta shafi yawancin jihohi a Najeriya kuma ta jawo hasarar rayuka da dukiyoyi da dama. Duk wanda abin ya shafa ya yi hasara, ko da waye ne shi. Hakazalika, kowane irin mutum yana iya kamuwa da cuta a kowane lokaci.

Me ya sa Allah ba ya kāre mutanen kirki daga bala’i?

Wasu suna iya tambaya cewa: ‘Shin Allah ba zai iya hana munanan abubuwan nan faruwa ba? Ba zai iya kāre mutanen kirki daga masifu ba?’ Sai Allah ya san cewa waɗannan abubuwan za su faru kafin ya iya hana su faruwa, ko ba haka ba? A gaskiya, Allah zai iya sanin abin da zai faru a nan gaba, amma ya kamata mu yi la’akari da tambayar nan: Shin Allah ba shi da iyaka ne a yadda yake amfani da ikonsa na hangen gaba?—Ishaya 42:9.

Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Allah kuwa yana sama: Ya aika[ta] iyakar abin da ya ga dama.’ (Zabura 115:3) Jehobah yana yin abin da yake ganin ya kamata ya yi ne kawai, ba duk abin da zai iya yi ba. Haka ma yake da abin da ya ga damar hanga. Alal misali, bayan mugunta ta zama ruwan dare a biranen Saduma da Gwamarata, Allah ya gaya wa uban iyalin nan Ibrahim cewa: ‘Zan sauka yanzu, in gani ko aikinsu ya kai gwargwadon ƙararsa, wanda ta zo gare ni; idan ba haka ba, zan gane.’ (Farawa 18:20, 21) Jehobah ya san iyakar muguntar biranen nan ne a lokacin da ya ga damar yin hakan. Hakazalika, sai abin da ya ga damar sani ne zai hanga. (Farawa 22:12) Hakan bai nuna cewa Allah yana da kasawa ba. Tun da yake “aikinsa cikakke ne,” Allah yakan yi amfani da ikonsa na hangen gaba dangane da nufinsa; ba ya tilasta wa kowa ya bi wani tafarki a rayuwa.b (Kubawar Shari’a 32:4) Mene ne muka fahimta daga hakan? Mun fahimci cewa Allah ba ya amfani da ikonsa na hangen gaba haka barkatai.

SHIN LAIFIN ’YAN ADAM NE?

’Yan Adam ma suna da hannu a mugunta da ke addabar mutane. Ga yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ke haifar da munanan ayyuka: “Kowane mutum yakan jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’annan, lokacin da sha’awa ta habala, takan haifi zunubi: Zunubi kuwa, sa’anda ya ƙasaita, yakan fid da mutuwa.” (Yaƙub 1:14, 15) A duk lokacin da mutane suka gamsar da sha’awoyi marar kyau, suna ɗanɗana sakamako marar kyau. (Romawa 7:21-23) Tarihi ya nuna cewa ’yan Adam sun aikata mugunta sosai kuma hakan ya jawo wahala mai tsanani. Ƙari ga haka, masu mugunta sukan zuga wasu su koyi halayen banza, kuma hakan ya sa mugunta ta daɗa gaba-gaba.—Misalai 1:10-16.

’Yan Adam sun aikata mugunta sosai kuma hakan ya jawo wahala mai tsanani

Shin ya kamata Allah ya sa baki don ya hana mutane yin munanan abubuwa ne? Ka yi la’akari da halittar mutum. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya halicci mutum a kamanninsa, wato, da halaye irin na Allah. (Farawa 1:26) Da yake an ba ’yan Adam ’yancin yin zaɓi, za su iya zaɓan su yi ƙaunar Allah cikin aminci kuma su yi abin da ya dace a gabansa. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Idan Allah ya tilasta wa ’yan Adam su bi wani tafarki, hakan zai hana su amfani da wannan ’yancin, ko ba haka ba? Hakika, ’yan Adam za su zama kamar na’urori da suke yin abin da aka tsara su su yi ne kawai. Haka ma yake idan ana ƙaddara kome da muke yi ko kuma dukan abubuwan da ke faruwa da mu. Babu shakka, muna farin cikin sanin cewa Allah yana mutunta mu ta wajen ba mu ’yancin zaɓan tafarkinmu! Amma hakan ba ya nufin cewa munanan abubuwa da suke faruwa don kuskure ko kuma munanan zaɓin ’yan Adam za su addabe mu har abada.

KARMA CE KE JAWO WAHALA?

Idan ka yi wa mabiya addinin Hindu ko Buddha tambayar da ke bangon gaba na wannan mujallar, mai yiwuwa za su ba ka wannan amsar: “Masifu suna faɗa wa mutanen kirki domin Karma. Suna girbe abin da suka shuka a rayuwarsa ta dā ne.”c

Sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da mutuwa zai taimake mu mu fahimci gaskiyar koyarwar Karma. A cikin lambun Adnin, inda aka halicci mutum, Mahaliccinmu ya gaya wa mutumi na farko, wato Adamu, cewa: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:16, 17) Da a ce Adamu bai yi zunubi ta wajen taka dokar Allah ba, da ya rayu har abada. An soma mutuwa ne sanadiyyar taka dokar Allah. A lokacin da Adamu ya sami ’ya’ya sai “mutuwa ta bi kan dukan mutane.” (Romawa 5:12) Saboda haka, za a iya cewa “hakkin zunubi mutuwa ne.” (Romawa 6:23) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya mutu ya kuɓuta daga zunubi.” (Romawa 6:7) Ma’ana, mutane ba za su ci gaba da ɗanɗana sakamakon zunubansu bayan sun mutu ba.

Miliyoyin mutane a yau suna ganin ana shan wahala ne saboda Karma. Waɗanda suka yi imani da wannan koyarwar ba sa ta da kura a kan wahalar da su ko kuma wasu ke sha. Amma a gaskiya, wannan koyarwar ta nuna cewa ba za a taɓa ganin ƙarshen masifu ba. Ƙari ga haka, waɗanda suke bin wannan koyarwar sun yarda cewa sai mutum ya ’yantu daga tsarin sake haihuwa kafin ya daina shan wahala, kuma hakan zai faru ne idan ya sami ilimi na musamman kuma ya yi abin da zai faranta ran jama’a gaba ɗaya. Hakika, waɗannan ra’ayoyin sun bambanta sosai da koyarwar Littafi Mai Tsarki.d

AINIHIN SANADIN

Ba ’yan Adam ba ne ainihin sanadin mugunta. Shaiɗan Iblis, wanda a dā can amintaccen mala’ikan Allah ne, bai “tsaya a kan gaskiya ba” kuma ta hakan ya shigo da zunubi cikin duniya. (Yohanna 8:44) Shi ne ya cinna wutar tawaye a lambun Adnin. (Farawa 3:1-5) Yesu Kristi ya kira shi “mugun” da kuma “sarkin duniya.” (Matta 6:13; Yohanna 14:30) Yawancin ’yan Adam suna bin Shaiɗan ta wajen ƙin bin tafarkun Jehobah masu kyau. (1 Yohanna 2:15, 16) Littafin 1 Yohanna 5:19 ya ce: ‘Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.’ Akwai kuma wasu mala’iku da suka bi Shaiɗan a tawayensa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan da aljanunsa suna “ruɗin dukan duniya,” kuma sakamakon hakan shi ne ‘kaiton’ duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Saboda haka, Shaiɗan Iblis ne ainihi yake da alhakin mugunta.

Hakika, ba Allah ne ke da alhakin masifun da ke faruwa da mutane ba, kuma ba ya sa mutane su sha wahala. Akasin haka, ya yi alkawarin kawar da mugunta, kamar yadda za a bayyana a talifi na gaba.

a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.

b Idan kana so ka san abin da ya sa Allah ya ƙyale mutane suna shan wahala, ka duba babi na 11 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

c Don bayani a kan tushen koyarwar Karma, ka duba shafuffuka na 8-12 na ƙasidar nan Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

d Don ka san koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan yanayin matattu da kuma begen da suke da shi, ka duba shafuffuka na 6 da 7 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba