Kana “Biɗan Aiki” Mai Kyau Kuwa?
DATTAWA biyu sun gaya wa Fernandoa cewa suna son ganinsa kuma hakan ya sa shi fargaba. Bayan da mai kula da da’ira ya ziyarci ikilisiyarsu sau da yawa, dattawan sun gaya masa abubuwan da yake bukata ya yi don ya cancanci samun ƙarin aiki a cikin ikilisiya. Da shigewar lokaci, Fernando ya soma tunani ko zai yiwu a naɗa shi dattijo. Sai mai kula da da’ira ya sake ziyartar ikilisiyarsu. Shin mene ne dattawan za su gaya masa a wannan karon?
Fernando ya kasa kunne sosai da ɗaya daga cikin dattawan yake masa magana. Ɗan’uwan ya yi ƙaulin 1 Timotawus 3:1 kuma ya ce dattawan ikilisiyar sun sami rahoto cewa an naɗa shi dattijo. Fernando ya yi mamaki kuma ya ce, “Me ka ce?” Ɗan’uwan ya sake maimaita abin da ya ce, sai Fernando ya soma murmushi. Daga baya, sa’ad da aka sanar a cikin ikilisiya cewa an naɗa shi dattijo, kowa ya yi farin ciki.
Shin ya dace mutum ya kasance da burin neman gata a cikin ikilisiya? Hakika. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk mai burin aikin kula da ikilisiya, yana burin aiki mai kyau ke nan.” (1 Tim. 3:1, Littafi Mai Tsarki) Kiristoci maza da yawa suna bin wannan shawarar kuma suna inganta ibadarsu don su cancanci samun gata a cikin ikilisiya. A sakamakon haka, Allah ya albarkaci mutanensa da dubban ’yan’uwa maza da suke hidima a matsayin dattawa da bayi masu hidima. Amma da yake ana samun ci gaba a ikilisiyoyi da yawa, ana bukatar ƙarin ’yan’uwa maza su biɗi yin hidima a cikin ikilisiya. Yaya ne ya kamata a yi hakan? Shin ya kamata waɗanda suke burin yin hidima su damu da batun kamar yadda Fernando ya yi?
MENE NE “BIƊAN AIKI” MAI KYAU YAKE NUFI?
An fassara furucin nan, “biɗan aiki” daga wata kalmar Helenanci da ke nufin yin marmarin abu sosai ko kuma miƙa hannu don samun abu. Kamar yadda mutum zai iya miƙa hannu don ya tsinka nunannen mangwaro mai kyau daga itace. Amma biɗan aiki ba ya nufin neman gatan zama mai “kula” ido a rufe. Me ya sa? Domin ya kamata waɗanda suke son su yi hidimar dattawa su kasance da burin yin “nagarin aiki,” ba neman matsayi ba.
An ambaci halaye da yawa da za su sa mutum ya zama mai nagarin aiki a 1 Timotawus 3:2-7 da Titus 1:5-9. Wani ɗan’uwa mai suna Raymond da ya daɗe yana hidima a matsayin dattijo ya yi furuci game da waɗannan ƙa’idodi, ya ce: “A gare ni, abin da ya fi muhimmanci shi ne halinmu. Ko da yake yana da muhimmanci mutum ya iya koyarwa da kuma ba da jawabi, amma waɗannan abubuwan ba su fi kasancewa marar abin zargi da mai-kamewa da mai shimfiɗaɗɗen hankali da natsattse da mai karɓan baƙi muhimmanci ba.”
Idan ɗan’uwa da ke biɗan aiki da gaske ya guji dukan rashin gaskiya da kazamta, ba za a iya zarginsa ba. Da yake shi mai-kamewa ne, mai shimfiɗaɗɗen hankali da kuma natsattse, ’yan’uwa masu bi za su amince ya yi ja-gora kuma ya taimaka musu da matsalolinsu. Yana karɓan baƙi, yana ƙarfafa matasa da waɗanda ba su daɗe da zama Shaidu ba. Yana ƙarfafa marasa lafiya da kuma tsofaffi don shi nagari ne. Yana ƙoƙari ya kasance da waɗannan halayen ne don yana son ya taimaka wa mutane amma ba don yana son ya nuna cewa ya cancanta a naɗa shi ba.b
Rukunin dattawa za su yi marmarin ba wa ɗan’uwan da yake biɗan aiki shawara da kuma ƙarfafa, amma shi ne ke da hakkin bin waɗannan umurnan Littafi Mai Tsarki. Wani ƙwararen dattijo ya ce: “Idan kana biɗan aiki, ka yi ƙwazo sosai don ka cancanta. Littafin Mai-Wa’azi 9:10 ta ce: ‘Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da [dukan, NW] ƙarfinka.’ Ka yi duk wani aikin da dattawa suka ba ka da ƙwazo. Ka so dukan aikin da aka ba ka a cikin ikilisiya, har ma da shara. Da shigewar lokaci, za a ga ƙoƙarinka.” Idan kana son ka yi hidima a matsayin dattijo a nan gaba, ka kasance mai ƙwazo da kuma amintacce a dukan fannonin ibada. Ya kamata a san ka da tawali’u ba mugun buri ba.—Mat. 23:8-12.
KA GUJI TUNANI DA KUMA AYYUKA MARASA KYAU
Wasu da suke da burin samun gata a cikin ikilisiya za su iya nuna ta halayensu cewa suna so su zama dattawa ko bayi masu hidima ko kuma su rinjayi dattawa. Wasu kuma sukan ɓata rai idan dattawa suka ba su shawara. Ya kamata irin waɗannan ’yan’uwan su tambayi kansu, ‘Shin ina biɗan aiki don amfanin kaina ko kuma ina son in kula da tumakin Jehobah?’
Kada waɗanda suke biɗan aiki su manta cewa wani abin da ake bukata daga wajen dattawa shi ne su zama ‘gurbi ga garken.’ (1 Bit. 5:1-3) Ya kamata wanda yake so ya kafa wa ikilisiya gurbi ya guji mugun tunani da kuma ayyukan banza. Ya kamata ya kasance mai haƙuri ko da an naɗa shi yanzu ko a’a. Kasancewa dattijo ba ya sa mutum ya zama marar aibi. (Lit. Lis. 12:3; Zab. 106:32, 33) Ƙari ga haka, zai iya zama cewa ɗan’uwan bai san cewa yana da ‘wani aibi a kansa ba,’ amma wasu za su iya ganin sa da wasu halayen da ba su dace ba. (1 Kor. 4:4) Saboda haka, idan dattawa suka ba ka shawara mai kyau daga cikin Littafi Mai Tsarki, ka saurare su ba tare da yin fushi ba. Bayan haka, ka yi ƙoƙarin bin shawarar da suka ba ka.
IDAN KA DAƊE KANA JIRA FA?
Wasu ’yan’uwa suna ganin kamar dai yana daɗewa sosai kafin a naɗa su. Idan ka yi shekaru da dama kana ‘biɗan aikin’ dattijo, hakan na sa ka damuwa ne a wani lokaci? Ka yi la’akari da wannan ayar Littafi Mai Tsarki: “Muradin da ba a biya ba ya kan sa zuciya ta yi ciwo: amma sa’anda abin so ya samu, itacen rai ne.”—Mis. 13:12.
Mutum zai iya yin sanyin gwiwa idan bai cim ma wani maƙasudin da yake so ba. Ibrahim ya taɓa samun kansa a cikin irin wannan yanayin. Jehobah ya yi masa alkawari cewa zai ba shi ɗa, amma shekaru da yawa suka wuce kuma shi da matarsa Saratu ba su sami ’ya’ya ba. (Far. 12:1-3, 7) Sa’ad da Ibrahim ya ga cewa yana tsufa, ya yi kuka ga Jehobah cewa: “Ya Ubangiji Yahweh, me za ka ba ni, da shi ke zan fita nan marar-ɗa . . . Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba.” Jehobah ya tabbatar wa Ibrahim cewa zai cika alkawarin da ya yi masa. Amma sai da aka sake yin shekaru 14 kafin Allah ya cika wannan alkawarin.—Far. 15:2-4; 16:16; 21:5.
Sa’ad da Ibrahim yake jira, shin ya karaya ne a bautarsa ga Jehobah? A’a. Bai yi shakkar alkawarin da Allah ya yi masa ba. Ya ci gaba da kasancewa da bege cewa Allah zai cika alkawarin. Manzo Bulus ya ce game da Ibrahim: “Bayan da ya jimre da haƙuri, ya karɓi alkawarin.” (Ibran. 6:15) A ƙarshe, Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkaci wannan mutum mai aminci fiye da yadda yake tsammani. Wane darasi ne za mu iya koya daga Ibrahim?
Idan kana so ka yi hidima a matsayin dattijo amma ba a naɗa ka ba ko da yake ka yi shekaru da yawa kana biɗan wannan aikin, ka ci gaba da dogara ga Jehobah kuma ka riƙa bauta masa da farin ciki. Wani ɗan’uwa mai suna Warren ya taimaka wa ’yan’uwa da yawa su sami ci gaba a ibadarsu kuma ya bayyana dalilin, ya ce: “Yana ɗaukan lokaci kafin halayen mutum su nuna cewa ya cancanta a naɗa shi. Da shigewar lokaci, ta ra’ayinsa da halinsa da kuma ayyukansa a cikin ikilisiya za a gane cewa ɗan’uwa zai iya yin ayyuka da aka ba shi. Wasu suna gani cewa za su sami ci gaba ne kawai idan an ba su wani gata ko kuma an naɗa su dattawa ko bayi masu hidima. Irin wannan tunanin bai da kyau kuma zai iya haifar da jarabar neman matsayi. Idan kana bauta wa Jehobah da aminci a duk inda kake kuma a dukan abin da kake yi, ka sami ci gaba ke nan.”
Wani ɗan’uwa ya fi shekara 10 yana jira kafin aka naɗa shi dattijo. Ya yi magana game da wani sanannen kwatanci da ke Ezekiyel sura 1, sai ya bayyana darasin da ya koya, ya ce: “Jehobah ne yake ja-gorar karusarsa, wato ƙungiyarsa, kuma yana yin hakan yadda yake so.” Abin da yake da muhimmanci shi ne lokacin da Jehobah ya zaɓa ba lokacinmu ba. Idan ya zo ga batun yin hidima a matsayin dattijo, ba abin da nake so ko kuma muradina ba ne ke da muhimmanci. Wataƙila abin da nake so ba shi ne abin da Jehobah ya san cewa ina bukata ba.”
Idan kana da burin yin hidima a matsayin dattijo a nan gaba, ka biɗi aiki mai kyau ta wajen daɗa sa farin ciki ta kasance a cikin ikilisiya. Idan ka ga kamar ka daɗe kana jira, ka tuna cewa mai haƙuri yakan dafa dutse kuma ya sha romonsa. Raymond da aka ambata ɗazun, ya ce: “Mugun buri yana hana mutum kasancewa da wadar zuci. Waɗanda suke yawan damuwa ba sa samun farin ciki a ibadarsu ga Jehobah.” Ka yi ƙoƙari ka nuna halaye da ke nuna kana da ruhu mai tsarki, musamman ma haƙuri. Ka yi ƙoƙari ka inganta ibadarka ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka daɗa ƙwazo a wa’azin bishara da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Ka ja-goranci iyalinka a ayyukan ibada da kuma ibada ta iyali. Ka ji daɗin kasancewa da ’yan’uwanka maza da mata. Yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma burinka, za ka yi farin ciki a ibadarka ga Jehobah.
Yin aiki tuƙuru don cancantar yin hidima a cikin ikilisiya gata ne kuma albarka ce daga Jehobah; shi da ƙungiyarsa ba sa so waɗanda suke biɗan aiki a cikin ikilisiya su yi taƙaici ko kuma baƙin ciki a ibadarsu ba. Allah yana tare da waɗanda suke bauta masa da zuciya ɗaya kuma yana musu albarka. Idan Jehobah ya albarkaci bayinsa, “ba ya kan haɗa ta da baƙin ciki ba.”—Mis. 10:22.
Ko da a ce ka daɗe kana burin yin hidima a ikilisiya, akwai abubuwan da za ka iya yi don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Yayin da kake ƙoƙari don ka kasance da halayen da ake bukata kuma kana aiki da ƙwazo a cikin ikilisiya ba tare da ka yi watsi da iyalinka ba, Jehobah ba zai manta da abubuwan da ka yi a ibadarka gare shi ba. Bari ka ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki a kowane lokaci kuma a duk wani aikin da aka ba ka.
a An canja sunaye a wannan talifin.
b Ƙa’idodin da aka ambata a wannan talifin sun shafi waɗanda suke so su zama bayi masu hidima har ila. An ambaci halayen da ya wajaba su kasance da su a 1 Timotawus 3:8-10, 12, 13.