Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 11/15 pp. 28-32
  • Ku Koyar Da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Koyar Da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Na Ce da Ku Abokai”
  • “Na Yi Muku Kwatanci”
  • ‘Yesu ya Aike Su Kuma ya Dokace Su’
  • “Mai-Hikima Ya Kan Saurari Shawara”
  • “Ka Wasa Kanka”
  • ’Yan’uwa Maza, Ku Yi Shuka Ga Ruhu Kuma Ku Yi Burin Samun Hakki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Jehobah Yana Koyar Da Makiyaya Don Garkensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Kana “Biɗan Aiki Kuwa?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 11/15 pp. 28-32

Ku Koyar Da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula

“Kowa sa’anda ya kamalta za shi zama kamar malaminsa.”—LUK 6:40.

1. Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, mene ne ya yi don ya koyar da kuma tsara aikin wa’azi?

DA YAKE kammala labarinsa na Linjila, manzo Yohanna ya rubuta: “Akwai kuma waɗansu abu dayawa da Yesu ya yi; ina tsammani da a ce za a rubuta su kowane ɗaya, da duniya da kanta ba za ta ɗauki littatafai waɗanda za a rubuta ba.” (Yoh. 21:25) Yesu ya yi aiki tuƙuru a hidima a ɗan lokacin da yake duniya, ya nema da koyar da kuma tsara maza da za su yi shugabanci bayan ya bar duniya. Sa’ad da Yesu ya koma sama a shekara ta 33 A.Z., ya kafa tushen ikilisiya mai ƙarfi da za ta samu ƙaruwa da sauri.—A. M. 2:41, 42; 4:4; 6:7.

2, 3. (a) Me ya sa ake bukatar maza sosai da suka yi baftisma su yi burin samun hakki? (b) Mene ne za a tattauna a wannan talifin?

2 Ana bukatar maza da za su yi shugabanci a batutuwa na ruhaniya da yake muna da masu shelar Mulki fiye da miliyan bakwai da suke wa’azi da ƙwazo a cikin ikilisiyoyi sama da 100,000 a dukan duniya a yau. Alal misali, ana bukatar dattawan Kirista sosai. Ya kamata a yaba wa waɗanda suke burin samun wannan gatar hidima, domin suna biɗan “nagarin aiki.”—1 Tim. 3:1.

3 Da akwai abubuwa da ɗan’uwa yake bukatar ya yi kafin ya cancanci samun hakki a cikin ikilisiya. Zuwa makaranta da kuma iyawa ba sa shirya namiji ya samu irin wannan aikin. Dole ne rayuwar mutum ta jitu da abin da Littafi Mai Tsarki yake bukatar ’yan’uwa maza su yi don hidima a cikin ikilisiya. Ta yaya za mu taimaki maza su samu ci gaba a cikin gaskiya kuma su cancanci samun hakki? Yesu ya ce: “Kowa sa’anda ya kamalta za shi zama kamar malaminsa.” (Luk 6:40) A wannan talifin, za mu tattauna wasu hanyoyi da Babban Malami, Yesu Kristi ya taimaka wa almajiransa su cancanci samun hakki mai girma, kuma za mu ga darussa da za mu iya koya daga abin da ya yi.

“Na Ce da Ku Abokai”

4. Ta yaya Yesu ya nuna wa almajiransa cewa shi aboki ne na gaske?

4 Yesu ya bi da almajiransa a matsayin abokai, ba kamar bayi ba. Ya kasance tare da su, ya amince da su da kuma ‘sanar musu dukan abin da ya ji daga wurin Ubansa.’ (Karanta Yohanna 15:15.) Sun yi farin ciki sosai sa’ad da Yesu ya amsa tambayar da suka yi cewa: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Mat. 24:3, 4) Ya kuma gaya wa mabiyansa ra’ayinsa da kuma yadda yake ji. Alal misali, a daren da aka ci amanarsa, Yesu ya ɗauki Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna zuwa cikin lambun Jathsaimani, inda ya yi addu’a sosai don ya damu. Mai yiwuwa manzanni ukun ba su ji abin da Yesu yake faɗa ba sa’ad da yake addu’a, amma sun san cewa ya damu ƙwarai. (Mar. 14:33-38) Ka kuma yi tunanin yadda sake kamani da aka yi ba da daɗewa ba ya shafi su ukun. (Mar. 9:2-8; 2 Bit. 1:16-18) Dangantaka ta kud da kud da Yesu ya ƙulla da almajiransa ta ƙarfafa su su ci gaba da aiki mai muhimmanci da za su yi.

5. A waɗanne hanyoyi ne dattawa Kirista za su iya ba da kansu don taimakon wasu?

5 Kamar Yesu, dattawa Kirista a yau suna abokantaka da mutane da kuma taimaka musu. Suna ƙaunar ’yan’uwansu da kuma nuna musu cewa sun damu sosai da su. Ko da yake dattawa sun fahimci muhimmancin riƙe asiri, su ba masu ɓoye ɓoye ba ne. Dattawa sun amince da ’yan’uwansu kuma suna gaya musu abubuwa da suka koya daga Nassosi. Ba sa tunanin cewa sun fi bawa mai hidima muhimmanci ko da shi matashi ne. Maimakon hakan, suna ɗaukansa a matsayin mutum mai ruhaniya da ke samun ci gaba da yake aiki mai kyau a madadin ikilisiya.

“Na Yi Muku Kwatanci”

6, 7. Ka kwatanta misalin da Yesu ya kafa wa almajiransa da kuma yadda hakan ya taimake su.

6 Ko da yake almajiran Yesu sun nuna godiya ga abubuwa na ruhaniya, amma a wasu lokatai yadda aka rene su da al’adunsu sun shafi tunaninsu. (Mat. 19:9, 10; Luk 9:46-48; Yoh. 4:27) Duk da haka, Yesu bai ba almajiransa dogon jawabi ba ko kuma ya yi fushi da su. Bai taɓa gaya musu su yi wani abu da ya fi ƙarfinsu ba ko kuma ya gaya musu su yi abin da ba zai iya yi ba. Maimakon haka, Yesu ya koyar da su ta misalinsa mai kyau.—Karanta Yohanna 13:15.

7 Wane irin misali ne Yesu ya kafa wa almajiransa? (1 Bit. 2:21) Ya yi rayuwa mai sauƙi don ya samu sauƙin yi wa mutane wa’azi. (Luk 9:58) Yesu ya kasance da filako kuma a koyaushe yana yin koyarwarsa daga Nassosi. (Yoh. 5:19; 17:14, 17) Yana da sauƙi mutane su je wurinsa kuma yana da kirki. Ƙauna ce ta motsa shi yin dukan abubuwan da ya yi. (Mat. 19:13-15; Yoh. 15:12) Misalin da Yesu ya kafa ya taimaki manzanninsa. Alal misali, Yaƙub bai ji tsoro a baƙin mutuwa ba amma ya kasance da aminci ga Allah har mutuwa. (A. M. 12:1, 2) Yohanna da aminci ya bi misalin Yesu har fiye da shekara sittin.—R. Yoh. 1:1, 2, 9.

8. Wane misali ne dattawa suke kafa wa matasa maza da kuma wasu?

8 Dattawa da suke sadaukar da kansu da nuna tawali’u da ƙauna, suna nuna irin misali da maza matasa suke bukata. (1 Bit. 5:2, 3) Bugu da ƙari, dattawa suna farin cikin nuna misali mai kyau don maza su iya yin koyi da bangaskiyarsu mai ƙarfi da yadda suke yin koyarwa da yadda suke yin rayuwa a matsayi Kiristoci da kuma yadda suke yin wa’azi.—Ibran. 13:7.

‘Yesu ya Aike Su Kuma ya Dokace Su’

9. Ta yaya muka sani cewa Yesu ya koyar da almajiransa su yi aikin wa’azi?

9 Bayan ya yi wa’azi na kusan shekara biyu, Yesu ya faɗaɗa aikin wa’azin ta wajen aika manzanninsa goma sha biyu su yi wa’azi. Da farko ya ba su umurni. (Mat. 10:5-14) Sa’ad da yake son ya ciyar da dubban taro ta mu’ujiza, Yesu ya gaya wa almajiransa yadda yake son su shirya mutanen don a rarraba musu abincin. (Luk 9:12-17) A bayyane yake cewa, Yesu ya koyar da almajiransa ta wajen ba su umurni da ya fita sarai kuma takamammu. Wannan koyarwar, haɗe da taimakon ruhu mai tsarki daga baya ya sa manzannin su iya tsara aikin wa’azi mai girma da aka yi a shekara ta 33 A.Z. da kuma bayan hakan.

10, 11. Ta yaya dattawa da wasu za su koyar da maza don su yi hidima a cikin ikilisiya?

10 A yau, sa’ad da mutum ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ne yake soma samun koyarwa ta ruhaniya. Za mu iya taimaka wa mutumin ya iya yin karatu da kyau. Za mu ci gaba da taimaka masa yayin da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Sa’ad da mutumin ya soma halartar tarurrukan Kirista a kai a kai, iliminsa a ruhaniya zai ƙaru sa’ad da ya ya soma aiki a Makarantar Hidima Ta Allah da zama mai shela marar baftisma da kuma sauransu. Bayan ya yi baftisma, koyarwarsa za ta haɗa da taimaka wajen gyara Majami’ar Mulki. Da sannu sannu, za a taimaki ɗan’uwan ya ga abin da yake bukatar ya yi don ya zama bawa mai hidima.

11 Sa’ad da dattijo yake ba ɗan’uwa da ya yi baftisma aiki, zai bayyana masa yadda zai bi ƙa’idodin ƙungiyar da kuma abin da yake bukatar ya yi. Dole ne ɗan’uwan da ake koyar ya fahimci abin da ake bukata a gare shi. Idan aikin yana masa wuya, dattijo mai ƙauna ba zai kammala nan da nan ba cewa ba zai iya aikin ba. Maimakon haka, dattijon zai nuna masa takamammun wurare da yake bukata ya yi gyara kuma yadda zai yi hakan. Dattawa suna farin cikin taimaka wa ɗan’uwa ya kula da hakkinsa domin sun san cewa yi wa wasu hidima a cikin ikilisiya yana kawo farin ciki.—A. M. 20:35.

“Mai-Hikima Ya Kan Saurari Shawara”

12. Me ya sa gargaɗin Yesu yake da amfani?

12 Yesu ya koyar da almajiransa ta wajen ba su gargaɗi da ya dace da bukatunsu. Alal misali, ya tsauta wa Yaƙub da Yohanna don suna son su umurci wuta ta sauko daga sama ta lashe Samariyawa da ba su saurare shi ba. (Luk 9:52-55) Sa’ad da mahaifiyar Yaƙub da Yohanna ta tuntuɓi Yesu a madadinsu don a ba su matsayi mai kyau a cikin Mulkin, Yesu ya yi musu magana kai tsaye cewa: “Zama a damana da haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.” (Mat. 20:20-23) A kowanne lokaci, Yesu ba ya ba da umurni da ke bisa ƙa’idodi na Allah da yake a bayyane da kuma zai taimaka wa mutane su san yadda za su aikata a yanayi dabam dabam. Ya koyar da almajiransa su yi tunani da kuma aikata daidai da Kalmar Allah. (Mat. 17:24-27) Yesu ya kuma san cewa almajiransa ajizai ne kuma akwai wasu abubuwa da ba za su iya yi ba. Ya ba su gargaɗi domin yana ƙaunarsu sosai.—Yoh. 13:1.

13, 14. (a) Wane ne yake bukatar gargaɗi? (b) Ka ba da misalan gargaɗin da dattijo zai iya ba wani ɗan’uwa da ba ya samun ci gaba a ruhaniya.

13 Duk ɗan’uwan da yake son ya yi hidima a cikin ikilisiya zai bukaci gargaɗi na Nassi a rayuwarsa. Misalai 12:15 ta ce: “Mai-hikima ya kan saurari shawara.” Wani ɗan’uwa matashi ya ce: “Abin da ya fi mini wuya shi ne bi da ajizanci na, amma shawara da wani dattijo ya ba ni ta taimaka mini na kasance da ra’ayin da ya dace.”

14 Idan dattawa suka lura cewa halin wani ɗan’uwa ne yake hana shi samun ci gaba, za su taimaka masa nan da nan da “ruhun tawali’u.” (Gal. 6:1) A wasu lokatai, ana bukatar a ba da gargaɗi don a taimaka wa wani ya gyara halinsa. Idan dattawa suka lura cewa wani ɗan’uwa ba ya yin iya ƙoƙarinsa, suna iya gaya masa cewa Yesu mai shelar Mulki ne da ƙwazo kuma ya ba mabiyansa aiki su almajirtar. (Mat. 28:19, 20; Luk 8:1) Idan ɗan’uwan mai son girma ne, wani dattijo yana iya nuna masa yadda Yesu ya taimaki almajiransa su ga haɗarurrukan neman girma. (Luk 22:24-27) Idan wani ɗan’uwa ba ya gafarta wa mutane kuma fa? Dattawa suna iya taimakonsa ta wajen yin amfani da kwatancin bawan da ba ya son ya gafarta wasu ko da yake wasu sun gafarta masa basusuka masu yawa. (Mat. 18:21-35) Idan wani yana bukatar gargaɗi, ya kamata dattawa su yi hakan nan da nan.—Karanta Misalai 27:9.

“Ka Wasa Kanka”

15. Ta yaya iyalin ɗan’uwa za ta iya taimaka masa ya yi wa wasu hidima?

15 Dattawa suna ja-gora wajen koyar da maza su yi hidima a cikin ikilisiya, amma wasu za su iya tallafa wa ƙoƙarce-ƙoƙarcensu. Alal misali, iyalin ɗan’uwa suna iya taimaka masa ya cancanci samun hakki. Amma, idan ya riga ya zama dattijo, matarsa da yaran za su iya tallafa masa yayin da yake aiki tuƙuru a cikin ikilisiya. Sun fahimci cewa dole ne ya yi amfani da wasu cikin lokacinsa da kuzarinsa don ya taimaki wasu. Muna godiya don halinsu na sadaukarwa don kula da hakkinsa da kyau.—Mis. 15:20; 31:10, 23.

16. (a) Wane ne ainihi yake bukatar ya nuna cewa yana son ya yi wa mutane hidima? (b) Ta yaya ɗan’uwa zai yi burin samun hakki a cikin ikilisiya?

16 Ko da yake wasu za su iya taimakonsa, amma ɗan’uwan ne yake bukatar ya nuna cewa yana burin yi wa mutane hidima. (Karanta Galatiyawa 6:5.) Hakika, ɗan’uwa ba ya bukatar ya zama bawa mai hidima ko kuma dattijo kafin ya taimaki wasu da kuma saka hannu sosai a hidima. Amma, yin burin samun hakki a cikin ikilisiya yana nufin yin ƙoƙari don cika bukatun da ke cikin Nassosi. (1 Tim. 3:1-13; Tit. 1:5-9; 1 Bit. 5:1-3) Saboda haka, idan ɗan’uwa yana son ya yi hidima a matsayin bawa mai hidima ko kuma dattijo amma ba a naɗa shi ba tukun, ya kamata ya mai da hankali ga wurare da yake bukatar samun ci gaba a ruhaniya. Yana bukatar ya karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da yin bimbini da addu’a da kuma yin ƙwazo sosai a hidimar Kirista. Idan ya yi waɗannan abubuwan, yana bin gargaɗin da Bulus ya ba Timotawus: “Ka wasa kanka zuwa ibada.”—1 Tim. 4:7.

17, 18. Mene ne ɗan’uwa zai iya yi idan yana jin cewa bai isa yin hidima ba ko kuma ba ya son ya yi hidima?

17 Idan ɗan’uwa yana jin cewa bai isa zama bawa mai hidima ko kuma dattijo kuma fa? Yana da kyau ya tuna da yadda Jehobah da Yesu suke taimaka mana. Hakika, Jehobah “yana ɗauke da nauwayarmu kowace rana.” (Zab. 68:19) Saboda haka, Ubanmu na sama zai iya taimaka wa ɗan’uwa ya karɓi hakki a cikin ikilisiya. Idan ɗan’uwa ba bawa mai hidima ko kuma dattijo ba, yana da kyau ya tuna cewa ana bukatar maza da suka manyanta su karɓi hakki a cikin ƙungiyar Allah. Yin tunani a kan wannan yana iya motsa ɗan’uwa ya yi ƙoƙari sosai don sha kan jin cewa bai cancanta ba. Zai iya yin addu’a don samun ruhu mai tsarki domin hakan zai taimaka masa ya samu salama da kuma kamewa, halaye da yake bukata don ya kawar da alhini da jin cewa bai cancanta ba. (Luk 11:13; Gal. 5:22, 23) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkaci ’yan’uwa da suke son su yi hidima ga wasu da ra’ayin da ya dace.

18 Wataƙila ɗan’uwa ba ya son ya yi wa wasu hidima. Mene ne zai iya taimaka masa? Manzo Bulus ya rubuta: “Allah ne yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma, zuwa abin da ya gamshe shi.” (Filib. 2:13) Allah ne yake sa mutum ya so yin hidima, kuma ruhun Jehobah zai iya ba mutumin ƙarfin yin tsarkakkiyar hidima. (Filib. 4:13) Kuma Kirista zai iya yin addu’a ga Allah ya taimaka masa ya yi abin da yake da kyau.—Zab. 25:4, 5.

19. Ta da “makiyaya bakwai, da shugabannai takwas” ya tabbatar mana da mene ne?

19 Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen dattawa da suke koyar da wasu. Yana kuma yi wa ’yan’uwan da suke son su yi wa wasu a cikin ikilisiya hidima. Nassosi ya tabbatar mana cewa tsakanin mutanen Allah za a ta da “makiyaya bakwai, da shugabannai takwas” wato, adadin maza da suka manyanta don su yi shugabanci a cikin ƙungiyar Jehobah. (Mi. 5:5) Abin albarka ne cewa ana koyar da maza da yawa cikin tawali’u kuma suna burin samun hakki kuma hakan na sa a yabi Jehobah!

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Yesu ya taimaki almajiransa don su cancanci samun hakki mai girma?

• Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu yayin da suke taimaka wa maza a cikin ikilisiya su yi shugabanci?

• Ta yaya iyalin ɗan’uwa za ta iya taimaka masa ya yi burin samun hakki a cikin ikilisiya?

• Mene ne ɗan’uwa zai iya yi don ya samu hakki?

[Hotona a shafi na 31]

Yaya za ka iya koyar da ɗalibinka na Littafi Mai Tsarki yayin da yake neman samun ci gaba?

[Hoto a shafi na 32]

Ta yaya maza za su iya nuna cewa suna burin samun hakki?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba