Ku Taimaki Maza Su Samu Ci Gaba A Ruhaniya
‘Daga nan gaba za ka riƙa kama mutane.’—LUK 5:10.
1, 2. (a) Yaya maza suka ɗauki wa’azin Yesu? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
BAYAN Yesu da almajiransa sun yi wa’azi a dukan Galili, suka hau jirgi zuwa wurin da babu mutane don su huta. Amma jama’a suka bi su zuwa wurin. Kuma adadinsu “maza wajen dubu biyar ne, ban da mata da yara.” (Mat. 14:21) A wani lokaci kuma, mutane ‘dubu huɗu, ban da mata da yara,’ suka zo wurin Yesu don ya warkar da kuma koyar da su. (Mat. 15:38) Hakika, maza da yawa suna cikin waɗanda suka zo wurin Yesu don ya koyarwar da su. Babu shakka, ya sa rai cewa mutane da yawa za su saurare shi, domin bayan ya sa suka kama kifi ta mu’ujiza, Yesu ya gaya wa almajirinsa Siman: “Daga nan gaba za ka [riƙa] kama mutane.” (Luk 5:10) Yesu ya nuna cewa aikin wa’azi kamar kamun kifi ne. Kuma zai iya taimaka musu su samu mutane da yawa da za su amince da gaskiya da suka haɗa da maza ma.
2 Akwai maza da yawa ma a yau da suke son wa’azin da muke yi kuma suna amincewa da shi. (Mat. 5:3) Amma dai, maza da yawa suna jinkiri kuma ba sa samun ci gaba a ruhaniya. Ta yaya za mu taimaka musu? Ko da yake Yesu bai kafa hidima ta musamman don maza ba, amma ya yi magana da ya shafi maza a zamaninsa. Bari mu yi amfani da misalinsa don mu bincika yadda za mu iya taimaka wa maza su bi da abubuwa uku da suka fi damunsu a yau: (1) samun abin biyan bukata (2) tsoro saboda ra’ayin wasu da (3) jin cewa ba su cancanta ba.
Samun Abin Biyan Bukata
3, 4. (a) Mene ne ya fi damun maza da yawa? (b) Me ya sa wasu maza suka saka biyan bukatu na rayuwa a gaba fiye da biɗan abubuwa na ruhaniya?
3 Wani marubuci ya ce wa Yesu: “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” Amma sa’ad da Yesu ya gaya masa cewa “Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa,” sai marubucin ya canja ra’ayinsa. Rashin sanin inda zai samu abincin da zai riƙa ci da kuma inda zai riƙa kwana ya ɗimauce marubucin, domin babu shakka bai zama almajirin Kristi ba.—Mat. 8:19, 20, Littafi Mai Tsarki.
4 Maza da yawa suna tunani cewa samun kuɗi da aiki ya fi muhimmanci da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin biyayya ga abin da yake koyarwa. Samun digiri na jami’a da kuma karɓan albashi mai tsoka ya fi muhimmanci a gare su. Sun san cewa suna bukatar kuɗi don su yi rayuwa kullum. Saboda haka suna tunani cewa kuɗi da kuma aiki zai amfane su fiye da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma zama abokan Allah. Suna iya son abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, amma “ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya” suna iya hana su ƙara koya game da Allah da kuma yin biyayya da abin da ya ce. (Mar. 4:18, 19) Ka yi la’akari da yadda Yesu ya taimaka wa almajiransa su daidaita abin da ya fi muhimmanci a gare su.
5, 6. Mene ne ya taimaki Andarawus da Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna su tsai da shawara game da aikin da ya fi muhimmanci?
5 Andarawas da ɗan’uwansa Siman Bitrus suna aikin kama kifi tare. Yohanna da ɗan’uwansa Yaƙub da kuma mahaifinsu Zabadi ma haka. Sana’arsu tana auki sosai har sun kira ’yan ƙodago. (Mar. 1:16-20) Sa’ad da Andarawus da Yohanna suka fara samun labari game da Yesu daga bakin Yohanna Mai Baftisma, sun tabbata cewa sun samu Almasihu. Andarawus ya gaya wa ɗan’uwansa Siman Bitrus labarin, kuma wataƙila, Yohanna ma ya faɗa wa ɗan’uwansa Yaƙub. (Yoh. 1:29, 35-41) Ba da daɗewa ba bayan wannan lokacin, dukansu huɗu sun yi watanni suna bin Yesu yayin da yake yin wa’azi a Galili da Yahuda da kuma Samariya. Bayan hakan, dukansu huɗu suka koma sana’arsu ta kama kifi. Suna son abubuwa na ruhaniya, amma ba su saka hidima farko a rayuwarsu ba.
6 Jim kaɗan bayan wannan lokacin, Yesu ya gayyaci Bitrus da Andarawus su zo su zama “masuntan mutane.” Mene ne suka ce? “Nan da nan suka bar tarori, suka bi shi.” Hakan ma ya faru da Yaƙub da kuma Yohanna. “Nan da nan suka bar jirgi da ubansu, suka bi shi.” (Mat. 4:18-22) Mene ne ya taimaki waɗannan maza don su soma hidima ta cikakken lokaci? Shin sun tsai da shawara farat ɗaya ne? Da kyar! Watanni da yawa kafin su tsai da shawara, sun saurari Yesu, sun ga yadda ya yi mu’ujizoji, sun lura da yadda yake ƙwazo don adalci kuma sun lura cewa mutane suna son wa’azinsa. A sakamako, imaninsu da dogararsu ga Jehobah suka daɗa ƙarfi sosai!
7. Ta yaya za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su koya su dogara ga Jehobah?
7 Ta yaya za mu iya taimaka wa ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki su daɗa dogara ga Jehobah sosai? (Mis. 3:5, 6) Yadda muke koyarwa za ta iya taimaka musu. Sa’ad da muke koyarwa, za mu iya nanata alkawarin da Allah ya yi cewa zai albarkace mu sosai idan mun biɗi Mulkinsa farko a rayuwarmu. (Karanta Malakai 3:10; Matta 6:33.) Ko da yake za mu iya amfani da nassosi dabam-dabam don mu nuna yadda Jehobah yake yi wa mutanensa tanadi, amma yana da muhimmanci mu kafa misali mai kyau. Ba da labarin kanmu zai iya taimaka wa ɗalibanmu su dogara ga Jehobah. Za mu kuma iya tattauna labarai masu ban ƙarfafa da muka karanta a littattafanmu.a
8. (a) Me ya sa yake da muhimmanci ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya ‘ɗanɗana, ya duba, Ubangiji nagari ne’? (b) Ta yaya za mu taimaki ɗalibanmu su shaida nagartar Jehobah?
8 Ba karanta da kuma jin labari game da yadda wasu suka shaida albarkar Jehobah kaɗai ba ne zai sa mu kasance da bangaskiya. Ɗalibin Littafi Mai Tsarki yana kuma bukata ya shaida nagartar Jehobah. Marubucin zabura ya rera: “Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne: mai-albarka ne mutum wanda ya ke dogara gareshi.” (Zab. 34:8) Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibin ya ga cewa Jehobah nagari ne? A ce ɗalibinka yana da matsalar kuɗi, kuma yana nema ya daina hali marar kyau kamar yin shaye-shaye da caca da maye. (Mis. 23:20, 21; 2 Kor. 7:1; 1 Tim. 6:10) Shin koya wa ɗalibin yin addu’a don Allah ya taimaka masa ya shawo kan halinsa marar kyau ba zai taimaka masa ya shaida nagartar Jehobah ba? Ka kuma yi tunani a kan abin da zai iya faruwa sa’ad da muka ƙarfafa ɗalibin ya mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya ta wurin keɓe lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki duk mako da kuma shirya tarurrukan Kirista. Yayin da yake shaida albarkar Jehobah ga ƙoƙarce-ƙoƙarcensa, imaninsa zai daɗa girma!
Tsoron Ra’ayin Jama’a
9, 10. (a) Me ya sa Nikodimu da Yusufu na Arimathiya ba su sa mutane su san cewa suna imani ga Yesu ba? (b) Me ya sa wasu maza a yau ba sa son su bi Kristi?
9 Matsi na tsara zai iya sa wasu maza su ƙi bin Kristi. Nikodimu da Yusufu na Arimathiya sun amince da Yesu a ɓoye domin suna tsoron abin da Yahudawa za su ce ko kuma za su yi idan suka gano hakan. (Yoh. 3:1, 2; 19:38) Akwai dalilin da ya sa suke jin tsoro. Malaman addini sun tsane Yesu sosai har suna korar duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu daga majami’a.—Yoh. 9:22.
10 Idan namiji ya nuna cewa yana son Allah da Littafi Mai Tsarki da kuma addini a wasu wurare a yau, abokan aikinsa da abokansa da kuma danginsa za su iya tsananta masa. A wasu wurare, zai iya kasance da haɗari mutum ya ce yana son ya canja addininsa. Matsi na tsara yana daɗa tsanani idan namiji yana aikin soja ko siyasa ko kuma a fadar sarki. Alal misali, wani mutum a Jamus ya ce: “Wa’azin da ku Shaidu kuke yi daga Littafi Mai Tsarki gaskiya ce. Amma idan na zama Mashaidi yau, kafin gobe kowa zai sani. Mene ne abokan aikina da maƙwabta da kuma waɗanda suka san ni da kuma iyalina za su ce? Ba zan iya jimrewa da hakan ba.”
11. Ta yaya Yesu ya taimaka wa mabiyansa su jimre da jin tsoron mutum?
11 Ko da yake babu kowanne cikin mabiyan Yesu da matsoraci ne, amma sun yi fama da tsoron mutum. (Mar. 14:50, 66-72) Ta yaya Yesu ya taimaka musu su samu ci gaba duk da matsi daga tsaransu? Yesu ya ɗauki matakai don ya shirya almajiransa don tsanantawa da za su fuskanta. Ya ce: “Albarka gareku sa’anda mutane suna ƙinku, suna ware ku dabam, suna zarginku, suna maida sunanku mugu, sabili da Ɗan mutum.” (Luk 6:22) Yesu ya faɗakar da mabiyansa cewa za su fuskanci tsanantawa “sabili da Ɗan mutum.” Yesu ya kuma tabbatar musu cewa Allah zai goyi bayansu muddin sun dogara gare shi don taimako da iko. (Luk 12:4-12) Bugu da ƙari, Yesu ya gayyaci waɗanda ba su daɗe da sanin gaskiya ba su zama abokan almajiransa.—Mar. 10:29, 30.
12. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya taimaka wa sababbi su shawo kan tsoron mutum?
12 Mu ma muna bukata mu taimaki ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki su shawo kan tsoron mutum. Ya fi kasancewa da sauƙi mu jimre da ƙalubale, idan mun san hakan zai iya faruwa. (Yoh. 15:19) Alal misali, zai dace a taimaki ɗalibin ya shirya amsar Littafi Mai Tsarki mai sauƙi da zai ba da idan abokan aiki da wasu suka yi masa tambaya game da imaninsa. Ƙari ga zama abokinsa, za mu gabatar da shi ga wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya, musamman waɗanda suke da irin yanayinsa. Amma mafi muhimmanci, ya kamata mu koya masa yin addu’a a kai a kai daga zuciyarsa. Hakan zai iya taimaka masa ya kusaci Allah kuma ya mai da Jehobah Mafakarsa da Fa ɗinsa.—Karanta Zabura 94:21-23; Yaƙub 4:8.
Jin Ba Ka Cancanta Ba
13. Me ya sa wasu maza ba sa son su karɓi gaskiya?
13 Wasu maza suna jinkirin saka hannu a abubuwa na ruhaniya domin ba su iya karatu ko magana sosai ba kuma suna jin kunya. Wasu maza ba su da gaba gaɗin furta ra’ayinsu a gaban jama’a. Saboda haka, yin tunani a kan yadda za su yi nazari da ba da kalami a tarurrukan Kirista, ko kuma furta wa mutane imaninsu zai iya sa su sanyin gwiwa. Wani ɗan’uwa Kirista ya ce, “Sa’ad da nake ƙarami, zan je bakin ƙofa, na yi kamar na kada ƙararrawar ƙofa, sai na fita daga wurin nan da nan, ina sa rai cewa ba wanda zai ji da kuma gan ni. . . . Tuna cewa ya kamata na je ƙofa ƙofa yana sa ni zazzabi.”
14. Me ya sa almajiran Yesu ba su iya warkar da wani yaro mai aljanu ba?
14 Ka yi tunani a kan yadda almajiran Yesu suka ji sa’ad da suka kasa warkar da yaron da yake da aljanu. Mahaifin yaron ya zo wurin Yesu ya ce: “[Ɗana] mai-farfaɗiya ne, yana kuwa shan azaba ƙwarai: gama sau da dama ya kan faɗi cikin wuta, dayawa kuma cikin ruwa. Kuma na kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkadda shi ba.” Amma sai Yesu ya fitar da aljanin, kuma ya warkar da yaron. Daga baya almajiransa suka zo wurinsa suka tambaye shi, suka ce: “Don me mu ba mu iya fitarda shi ba?” Yesu ya amsa: “Saboda ƙaramtar bangaskiyarku: gama ina ce muku, Hakika, idan kuna da bangaskiya kwatancin ƙwayar mustard, sai ku ce ma wannan dutse, Ka kawu daganan ka koma can; sai shi kawu; kuma babu abin da ba za shi yiwu gareku ba.” (Mat. 17:14-20) Muna bukatar bangaskiya sosai ga Jehobah don mu shawo kan matsaloli masu tsanani da muke ciki. Mene ne zai faru idan mutum bai lura da wannan ba, kuma ya soma mai da hankali ga ingancin kansa? Ba zai yi nasara ba, kuma hakan zai sa ya ji cewa bai cancanta ya bauta wa Jehobah ba.
15, 16. Ta yaya za mu iya taimaka wa ɗalibanmu sun daina jin cewa ba su cancanta su bauta wa Jehobah ba?
15 Hanya mai kyau da za mu taimaka wa wani da ke fama da sanyin gwiwa shi ne mu ƙarfafa shi ya mai da hankali ga Jehobah ba ga kansa ba. Bitrus ya rubuta: “Ku ƙasƙantar da kanku . . . ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai; kuna zuba dukan alhininku a bisansa.” (1 Bit. 5:6, 7) Hakan yana nufin cewa mu taimaki ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki su yi girma a ruhaniya. Mutum mai ruhaniya da gaske yana daraja abubuwa na ruhaniya. Yana ƙaunar Kalmar Allah kuma yana nuna “’ya’yan Ruhu” a rayuwarsa. (Gal. 5:22, 23) Shi mutum da ke addu’a ne sosai. (Filib. 4:6, 7) Bugu da ƙari, yana dogara ga Allah don ya sa ya samu ƙarfin zuciya da ƙarfi da yake bukata don ya fuskanci kowanne yanayi ko kuma ya yi nasara wajen cim ma kowanne irin hakki.—Karanta 2 Timotawus 1:7, 8.
16 Wasu ɗalibai za su bukaci a taimaka musu su iya karatu da tattaunawa da kuma yin magana. Wasu za su ji cewa ba su cancanta su bauta wa Jehobah ba saboda miyagun ayyukan da suka yi kafin su koya game da Jehobah. Ko mene ne yanayin ɗaliban, ƙaunarmu da kuma haƙuri, zai taimaka musu. Yesu ya ce, “Lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo.”—Mat. 9:12.
Ku ‘Kamo’ Maza da Yawa
17, 18. (a) Me za mu yi don mu tattauna da maza da yawa a hidima? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
17 Muradinmu ne cewa ƙarin maza za su saurari saƙon Littafi Mai Tsarki da ke kawo farin ciki. (2 Tim. 3:16, 17) Yaya za mu iya samun ƙarin maza a hidimarmu? Za mu iya yin hakan ta sa ƙwazo wajen fita hidima da yamma a kai a kai a ƙarshen mako da rana da kuma lokacin hutu da maza da yawa suke zama a gidajensu. Idan zai yiwu, muna iya cewa muna son mu tattauna da maigidan. Zai dace mu tattauna da abokan aikinmu maza sa’ad da ya dace kuma mu tattauna da mazan da matansu kaɗai ne masu bi.
18 Yayin da muke wa kowa da muka tarar da su wa’azi, za mu iya kasance da gaba gaɗi cewa waɗanda suke da zukatan kirki za su saurari saƙonmu. Bari mu taimaka wa dukan waɗanda suke son gaskiya cikin haƙuri. Amma ta yaya za mu iya taimaka wa mazan da sun riga sun yi baftisma a cikin ikilisiya su cancanci samun ƙarin hakki a ƙungiyar Allah? Talifi na gaba zai tattauna wannan tambayar.
[Hasiya]
a Ka duba Yearbooks of Jehovah’s Witnesses da kuma tarihi da aka buga cikin Hasumiyar Tsaro da Awake!
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za a taimaka wa maza su biɗi abubuwa na ruhaniya farko?
• Ta yaya za mu iya taimaka wa sababbi su jimre da matsi na tsara?
• Mene ne zai taimaki wasu su shawo kan jin cewa ba su cancanta ba?
[Hoto a shafi na 25]
Shin kana neman zarafi don ka yi wa maza wa’azi?
[Hoto a shafi na 26]
Ta yaya za ka iya taimaka wa ɗalibinka na Littafi Mai Tsarki ya shirya don ƙalubalen da zai fuskanta?