Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 11/15 pp. 3-7
  • Mene Ne Ma’anar Tashin Yesu Daga Matattu a Gare Mu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene Ne Ma’anar Tashin Yesu Daga Matattu a Gare Mu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA YA SA TASHIN YESU DAGA MATATTU YA BAMBANTA
  • JEHOBAH YA NUNA IKO A KAN MUTUWA
  • ABIN DA YA SA MUKA SAN CEWA AN TA DA YESU DAGA MATATTU
  • MA’ANAR TASHIN YESU DAGA MATATTU A GARE MU
  • Za A Yi Tashin Matattu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • “Ina da Bege ga Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Begen Tashin Matattu Yana Da iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 11/15 pp. 3-7

Mene Ne Ma’anar Tashin Yesu Daga Matattu a Gare Mu?

“Ya tashi.”—MAT. 28:6.

ZA KA IYA BAYYANAWA?

  • Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya bambanta da tashin matattu da aka yi kafin nasa?

  • Wane tabbaci ne muke da shi cewa an ta da Yesu daga matattu kuma yana da rai yanzu?

  • Mene ne ma’anar tashin Yesu daga matattu a gare ka?

1, 2. (a) Mene ne wasu shugabanan addinai suke son su sani, kuma wace amsa ce Bitrus ya ba su? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Me ya sa Bitrus ya kasance da gaba gaɗi a lokacin?

BA DA daɗewa ba bayan Yesu ya mutu, rukunin shugabannin addinin Yahudawa masu ƙiyayya suka tuhumi manzo Bitrus. Su masu faɗa a ji ne, kuma su ne suka ƙulla makirci don a kashe Yesu. Yanzu suna fushi don Bitrus ya warkar da wani mutum da aka haife shi gurgu. Suna son su san wanda ya ba Bitrus iko ya yi wannan warkarwar da kuma a sunan wa ya yi hakan. Manzon ya amsa da gaba gaɗi cewa: ‘Cikin sunan Yesu Kristi na Nazarat, wanda kuka [rataye a gungume, NW], wanda Allah ya tashe shi daga matattu, a cikinsa mutumin nan yana tsaye a gabanku lafiyayye.’—A. M. 4:5-10.

2 Kafin wannan lokacin, Bitrus ya tsorata kuma ya yi musun sanin Yesu sau uku. (Mar. 14:66-72) Me ya sa ya kasance da gaba gaɗi yanzu a gaban waɗannan shugabannin addini? Babbu shakka, ruhu mai tsarki ya taimaka masa. Ƙari ga haka, ya tabbata cewa an ta da Yesu daga matattu. Me ya tabbatar wa manzon cewa an ta da Yesu daga matattu? Kuma me ya sa muke da irin wannan tabbaci?

3, 4. (a) Su wane ne aka ta da daga matattu kafin zamanin manzannin Yesu? (b) Waɗanne mutane ne Yesu ya tayar daga matattu?

3 Manzannin Yesu sun san cewa ana iya ta da matattu domin kafin zamaninsu, an yi tashin matattu. Sun san cewa Allah ya ba annabi Iliya da Elisha ikon yin irin waɗannan mu’ujizai. (1 Sar. 17:17-24; 2 Sar. 4:32-37) Wani mutum da ya mutu ya tashi sa’ad da gawarsa ta taɓa ƙasusuwan Elisha a lokacin da aka jefa a cikin wani kabari. (2 Sar. 13:20, 21) Kiristoci na ƙarni na farko sun ba da gaskiya ga waɗannan labaran Littafi Mai Tsarki, kamar yadda muka ba da gaskiya cewa Kalmar Allah gaskiya ce.

4 Babu shakka, karanta labaran ta da matattu da Yesu ya yi ya motsa mu sosai. Sa’ad da ya ta da ɗa tilo na wata gwauruwa, babu shakka, ta yi mamaki sosai. (Luk 7:11-15) A wani lokaci kuma, Yesu ya ta da wata ’yar shekara 12. Ka yi tunanin irin farin ciki da kuma mamakin da iyayen suka yi sa’ad da aka ta da ’yarsu daga matattu! (Luk 8:49-56) Ƙari ga haka, a lokacin da Li’azaru ya fito da rai daga kogon dutse inda aka binne shi, mutane sun yi murna sosai!—Yoh. 11:38-44.

ABIN DA YA SA TASHIN YESU DAGA MATATTU YA BAMBANTA

5. Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya fi tashin matattu da aka yi kafin nasa?

5 Manzannin Yesu sun san cewa tashin Yesu daga matattu ya bambanta daga tashin matattu da aka yi kafin lokacin. Mutanen da aka ta da su daga matattu kafin lokacin sun sake rayuwa da gangan jikinsu kuma sun sake mutuwa. An ta da Yesu da jiki na ruhu wanda ba ya lalacewa. (Karanta Ayyukan Manzanni 13:34.) Bitrus ya ce game da Yesu: “An matar da shi cikin jiki, amma an rayar da shi cikin ruhu.” Ƙari ga haka, yana “hannun dama na Allah, ya rigaya ya hau sama; an sarayyar da mala’iku da mulkoki da ikoki ƙarƙashinsa.” (1 Bit. 3:18-22) Tashin matattu da aka yi kafin na Yesu sun sa mutane mamaki da kuma farin ciki, amma na Yesu ya fi duka waɗannan.

6. Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya shafi almajiransa?

6 Tashin Yesu daga matattu ya shafi almajiransa sosai. Maƙiyan Yesu sun gaskata cewa shi matacce ne har ila. Amma ya tashi. Yesu yana da rai kuma shi Mala’ika ne mai iko sosai kuma ɗan Adam ba zai iya yi masa illa ba. Tashinsa ya tabbatar cewa shi ɗan Allah ne, kuma sanin hakan ya ƙarfafa almajiransa, a dā suna baƙin ciki sosai, amma yanzu suna murna matuƙa. Ƙari ga haka, ya sa sun daina tsoro kuma sun kasance da gaba gaɗi. Tashin Yesu ya tabbatar da cikar nufin Jehobah kuma ya sa wa’azin bishara da almajiran suka yi ya kasance da ma’ana.

7. Mene ne Yesu yake yi yanzu, kuma waɗanne tambayoyi za mu iya yi?

7 A matsayinmu na bayin Jehobah, mun san cewa Yesu ba wani mai girma da ya rayu a dā ba ne kawai. Amma yana raye a yanzu kuma yana ja-gorar wani aikin da ya shafi kowa a duniya. A matsayinsa na Sarkin Mulkin sama, Yesu Kristi zai kawo ƙarshen mugunta a duniya ba da daɗewa ba kuma zai mai da ita aljanna inda mutane za su rayu har abada. (Luk 23:43) Waɗannan abubuwan ba za su yiwu ba idan ba a ta da Yesu daga matattu ba. Saboda haka, waɗanne dalilai ne muke da su na gaskata cewa an ta da Yesu daga matattu? Mene ne ma’anar tashinsa daga matattu a gare mu?

JEHOBAH YA NUNA IKO A KAN MUTUWA

8, 9. (a) Me ya sa shugabannin addinin Yahudawa suka ce a tsare kabarin Yesu? (b) Me ya faru a lokacin da mata suka zo wurin kogon?

8 Bayan an kashe Yesu, manyan malamai da Farisawa sun sami Bilatus suka ce: “Mai-girma, mun tuna tun wannan mai-yaudara yana da rai, ya ce, bayan kwana uku zan sake tashi. Ka umurta fa a tabbatar da kabarin har rana ta uku, domin kada almajiransa su zo su sace shi, su ce wa mutane, ya tashi daga matattu: ruɗani na ƙarshe shi fi na fari ɓarna.” Sai Bilatus ya ce masu: “Kuna da matsara: ku tafi, ku tabbatar da shi da iyakacin iyawarku.” Abin da suka yi ke nan.—Mat. 27:62-66.

9 An saka gangan jikin Yesu a wani kabarin da aka tona a cikin kogon dutse kuma aka rufe kogon da wani babban dutse. Shugabannin addinin Yahudawa sun so Yesu ya kasance matacce a cikin kabari har abada. Amma hakan ba nufin Jehobah ba ne ko kaɗan. Sa’ad da Maryamu Magadaliya da ɗayan maryamu sun je wurin kogon dutsen, sai suka tarar cewa an ture dutsen kuma mala’ika yana zaune a kai. Mala’ikun sun gaya wa matan su duba cikin kogon don ba kome a ciki. Mala’ikan ya ce: “Ba shi nan: gama ya tashi.” (Mat. 28:1-6) Hakika, Yesu yana da rai!

10. Wace hujja ce game da tashin Yesu daga matattu Bulus ya bayar?

10 Abubuwan da suka faru a cikin kwanaki 40 bayan haka sun ba da tabbaci cewa an ta da Yesu daga matattu. Manzo Bulus ya ba da hujjar sa’ad da ya rubuta wasiƙa ga Korintiyawa, ya ce: “Gama na bayar gareku tun da fari abin da ni kuma na karɓa, Kristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga littattafai; aka bizne shi; aka tashe shi kan rana ta uku bisa ga littattafai; ya bayyana ga Kefas; kāna ga su goma sha biyu; daga baya ya bayyana ga waɗansu ’yan’uwa, sun yi ɗari biyar, baki ɗaya, a cikinsu fa yawanci sun wanzu har wa yau, amma waɗansu sun rigaya sun yi barci; Kāna ya bayyana ga Yaƙub; kāna ga dukan manzannin; daga bayan duka kuma ya bayyana gare ni, kamar ga wanda an haife shi bakwaini.”—1 Kor. 15:3-8.

ABIN DA YA SA MUKA SAN CEWA AN TA DA YESU DAGA MATATTU

11. Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya faru “bisa ga littattafai”?

11 Dalili na ɗaya da ya sa muka san cewa an ta da Yesu daga matattu shi ne cewa hakan ya faru “bisa ga littattafai.” An annabta tashin Yesu daga matattu a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Dauda ya rubuta cewa Allah ba zai bar ‘mai-tsarkinsa’ a kabari ba. (Karanta Zabura 16:10.) A ranar Fentakos ta shekara ta 33 a zamaninmu, manzo Bitrus ya yi bayani cewa wannan annabcin ya cika a tashin Yesu daga matattu, ya ce: ‘[Dauda] ya rigaya ya ga wannan, zancen tashin Kristi ya yi da ya ce ba a bar shi cikin [Kabari, NW] ba, Jikinsa kuma ba ya ga ruɓa ba.’—A. M. 2:23-27, 31.

12. Su wane ne suka ga Yesu bayan ya tashi?

12 Dalili na biyu da ya sa muka san cewa an ta da Yesu daga matattu shi ne mutane da yawa sun gan shi bayan ya tashi. Sama da kwanaki arba’in bayan Yesu ya tashi, ya bayyana wa almajiransa a cikin lambun da aka binne shi, a hanya zuwa Immawus da kuma a wasu wurare. (Luk 24:13-15) A waɗannan lokatan, ya yi magana wa mutane dabam-dabam, wannan ya haɗa da Bitrus, da kuma jama’a da suka taru. Akwai lokacin da ya bayyana ga mutane fiye da 500! Babu shakka, mutane da yawa sun gan shi, kuma hakan hujja ce da ba za a iya yin musun ta ba.

13. Ta yaya ƙwazon almajiran Yesu ya nuna cewa sun tabbata cewa an ta da Yesu daga matattu?

13 Dalili na uku da ya sa muka san cewa Yesu ya tashi daga matattu shi ne ƙwazon da almajiransa suka nuna wajen yin shelar tashinsa. Yadda almajiran suka yi ƙwazo wajen yin wa’azi game da tashin Yesu daga matattu ya sa sun fuskanci tsanantawa da wahala da kuma mutuwa. Idan ba a ta da Yesu daga matattu ba, idan har hakan yaudara ce, da Bitrus ba yi kasada wajen yin shelar tashin Yesu a gaban waɗannan shugabannin addinin ba, don su ne suka sa a kashe shi saboda baƙin jini. Don Bitrus da sauran almajiran sun tabbata cewa Yesu yana da rai kuma yana ja-gorar aikin da Allah ya umurta a yi. Ƙari ga haka, tashin Yesu daga matattu ya tabbatar wa almajiransa cewa za a ta da su daga matattu idan suka mutu. Alal misali, Istifanus ya mutu da tabbaci cewa za a yi tashin matattu.—A. M. 7:55-60.

14. Me ya sa ka gaskata cewa an ta da Yesu daga matattu?

14 Dalili na huɗu da ya sa muka san cewa an ta da Yesu daga matattu shi ne tabbacin da muke da shi cewa yana sarauta yanzu kuma shi ne Shugaban ikilisiyar Kirista. Saboda haka, addinin Kirista na gaskiya yana yaɗuwa. Shin hakan zai yiwu ne idan ba a ta da Yesu daga matattu ba? Hakika, da a ce ba a ta da shi ba, da wataƙila ba za mu taɓa jin labarinsa ba. Amma muna da ƙwararan dalilai na gaskata cewa Yesu yana da rai kuma yana ja-gorarmu yayin da muke wa’azin bishara a faɗin duniya.

MA’ANAR TASHIN YESU DAGA MATATTU A GARE MU

15. Me ya sa tashin Yesu daga matattu yake ƙarfafa mu mu yi wa’azi?

15 Tashin Kristi daga matattu ya sa muna wa’azi da gaba gaɗi. Magabtan Allah sun yi shekara dubu biyu suna yin amfani da kowace irin dabara don su hana yaɗuwar bishara, hakan ya haɗa da ridda da ba’a da tarzoma da takunkumi da azaba da kuma kisa. Duk da haka, “ba makamin da aka ƙera” domin mu, da ya hana wa’azi da kuma almajirtarwa da muke yi. (Isha. 54:17, Littafi Mai Tsarki) Ba ma tsoron mabiyan Shaiɗan. Yesu yana tare da mu kuma yana goya mana baya kamar yadda ya yi alkawari. (Mat. 28:20) Za mu iya kasancewa da gaba gaɗi domin ko da mene ne maƙiyanmu suka yi ba za su iya hana mu yin wa’azi ba!

16, 17. (a) Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya tabbatar da abubuwan da ya koyar? (b) Bisa ga Yohanna 11:25, wane iko ne Allah ya ba wa Yesu?

16 Tashin Yesu daga matattu ya tabbatar da dukan abubuwan da ya koyar. Bulus ya ce idan har ba a ta da Kristi daga matattu ba, bangaskiyarmu da kuma wa’azin da muke yi banza ne. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan ba a ta da Kristi daga matattu ba, . . . an yaudari Kiristoci ba kaɗan ba kuma za su zama abin tausayi.” Idan ba a ta da Yesu daga matattu ba, da labarin Yesu ya zama labarin wani mutumin kirki da maƙiyansa suka kashe shi. Amma an ta da Yesu kuma hakan ya tabbatar da dukan abubuwan da ya koyar, haɗe da abubuwan da ya faɗa game da nan gaba.—Karanta 1 Korintiyawa 15:14, 15, 20.

17 Yesu ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu.” (Yoh. 11:25) Wannan furucin gaskiya ne kuma zai cika tabbas. Jehobah ya ba wa Yesu ikon rayar da waɗanda za su yi sarauta a sama da kuma biliyoyin waɗanda za su yi rayuwa har abada a duniya. Hadayar Yesu da kuma tashinsa daga matattu sun ba da tabbaci cewa za a kawar da mutuwa. Babu shakka, sanin haka yana ƙarfafa ka ka jimre kowane irin gwaji kuma ka kasance da gaba gaɗi ko a bakin mutuwa.

18. Mene ne tashin Yesu daga matattu ya tabbatar?

18 Tashin Yesu daga matattu ya ba mu tabbaci cewa za a bi ƙa’idodin adalci na Jehobah wajen yi wa mutanen duniya shari’a. Sa’ad da Bulus yake magana ga wasu rukunin maza da mata a birnin Atina na dā, ya ce: “[Allah] zai yi wa duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara; wannan fa ya bada shaidarsa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.” (A. M. 17:31) Hakika, Yesu ne Alƙalin da Allah ya naɗa, kuma muna da tabbaci cewa zai yi shari’a cikin adalci da ƙauna.—Karanta Ishaya 11:2-4.

19. Ta yaya tashin Yesu daga matattu yake shafanmu?

19 Ba da gaskiya ga tashin Yesu daga matattu yana motsa mu mu yi nufin Allah. In da ba don hadayar Yesu da kuma tashinsa daga matattu ba, da ba mu sami ’yanci daga hukuncin zunubi da kuma mutuwa ba. (Rom. 5:12; 6:23) Da ba a ta da Yesu daga matattu ba, za mu iya cewa: “Bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu.” (1 Kor. 15:32) Amma ba ma mai da hankali ga annashuwa. A maimakon haka, mun ɗauki begen tashin matattu da muhimmanci kuma muna marmarin bin ja-gorar Jehobah a dukan abu.

20. Ta yaya tashin Yesu daga matattu ya nuna cewa Allah mai girma ne?

20 Tashin Kristi daga matattu ya ba da shaida mai kyau cewa Jehobah mai girma ne kuma “mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.” (Ibran. 11:6) Hakika, Jehobah ya nuna iko da hikima wajen ta da Yesu da kuma ba shi rai marar mutuwa a sama! Ƙari ga haka, ta hakan, Allah ya nuna cewa zai cika dukan alkawuransa. Wannan ya haɗa da alkawarin da Allah ya yi cewa wani ‘zuriya’ zai taka rawar gani wajen raba gardama a kan batun ikon sarauta. Wajibi ne Yesu ya mutu kuma a ta da shi daga matattu don wannan alkawarin ya cika.—Far. 3:15.

21. Ta yaya begen tashin matattu yake shafan ka?

21 Shin ba ka godiya ga Jehobah saboda tabbataccen bege na tashin matattu? Littafi Mai Tsarki ya yi mana wannan alkawarin: “Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” Manzo Yohanna ne aka gaya wa wannan albishiri, kuma an ƙara ce masa: “Rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” Ta wurin wane ne Yohanna ya karɓi wannan hurarren wahayin? Ta wurin Yesu Kristi da aka ta da daga matattau.—R. Yoh. 1:1; 21:3-5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba