Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 11/15 pp. 13-17
  • Wajibi ne Mu Kasance da Tsarki a Dukan Al’amura

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wajibi ne Mu Kasance da Tsarki a Dukan Al’amura
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA GUJI BAUƊE WA IMANI
  • KA ƊAUKAKA JEHOBAH MAƊAUKAKIN SARKI
  • KA YI IYA ƘOƘARINKA A BAUTAR JEHOBAH
  • NAZARI DA KUMA HADAYUNMU NA YABO
  • “Ku Zama da Tsarki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Littafin Firistoci Ya Nuna Mana Yadda Za Mu Bi da Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Kasance da Tsarki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Taƙaici Daga Littafin Firistoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 11/15 pp. 13-17

Wajibi ne Mu Kasance da Tsarki a Dukan Al’amura

“Ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi.”—1 BIT. 1:15.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci na gaskiya su guji bauɗe wa imani?

  • Wace alaƙa ce sarautar Jehovah take da shi da halin ba ruwanmu na Kirista?

  • Bisa ga Ibraniyawa 5:7, 11-14, yaya ya kamata mu yi nazarin Kalmar Allah?

1, 2. (a) Wane irin hali ne Allah yake bukatar mutanensa su kasance da shi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifi?

JEHOBAH ya hure manzo Bitrus ya nuna cewa batun tsarki da aka nanata a littafin Levitikus yana da alaƙa da kasancewa da halaye masu kyau a matsayinmu na Kiristoci. (Karanta 1 Bitrus 1:14-16.) Jehobah “Mai-tsarki” ne kuma ya bukaci shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” su yi iya ƙoƙarinsu su zama masu tsarki a dukan al’amura ba a wasu kawai ba.—Yoh. 10:16.

2 A wannan talifin za mu koyi darussa daga littafin Levitikus da za su taimaka mana mu san ƙa’idodin Allah da kuma yadda za mu yi amfani da su don mu kasance masu tsarki a dukan al’amura. Za mu tattauna tambayoyi kamar su: Wane ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi idan muka fuskanci batun da zai sa mu bauɗe wa imani? Mene ne littafin Levitikus ya koya mana game da ɗaukaka sarautar Jehobah? Wane darasi ne za mu koya game da yin hadayu?

KA GUJI BAUƊE WA IMANI

3, 4. (a) Me ya sa ya kamata Kiristoci su guji ƙetare dokoki da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya sa bai kamata mu yi ramako ko kuma mu riƙe mutum a zuciya ba?

3 Idan muna so mu faranta wa Jehobah rai, wajibi ne mu ɗauki dokokinsa da kuma ƙa’idodinsa da muhimmanci. Kada mu ƙyale matsaloli su sa mu ƙetare dokokin Jehobah. Ko da yake ba ma bin Doka da aka ba da ta hannun Musa, amma dokokin suna ba mu ƙarin haske game da abin Allah yake so da kuma abin da ya tsana. Alal misali, an umurci Isra’ilawa: “Ba za ka ɗauka wa kanka fansa, ba kuwa za ka yi nukuran ’ya’yan jama’arka; amma sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka: ni ne Ubangiji.”—Lev. 19:18.

4 Jehobah ba ya so mu yi ramako da kuma riƙe mutane a zuciya. (Rom. 12:19) Shaiɗan zai yi farin ciki idan muka ƙi bin dokoki da kuma ƙa’idodin Allah, kuma hakan zai sa a ɓata sunan Jehobah. Ko da wani ya ɓata mana rai da gangan, bai kamata mu zama masu riƙe mutane a zuciya ba. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mu a matsayin ‘tukwanen ƙasa’ da ke ɗauke da dukiya. Wannan dukiyar ita ce hidimar da aka danƙa mana. (2 Kor. 4:1, 7) Saboda haka, fushi bai jitu da wannan hidimar da muke yi ba!

5. Mene ne za mu iya koya daga labarin Haruna da kuma mutuwar ’ya’yansa? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)

5 Levitikus 10:1-11 ya ba da wani labari mai ban tausayi game da iyalin Haruna. Babu shakka, sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da wuta ta sauka daga sama kuma ta halaka ’ya’yan Haruna, Nadab da Abihu a mazauni. An umurci Haruna da iyalinsa cewa kada su yi makokinsu. Babu shakka, hakan ya gwada bangaskiyarsu sosai! Kana nuna cewa kana da tsarki ta wajen bin umurnin da ya ce kada mu yi cuɗanya da dangi ko wasu da aka yi musu yankan zumunci?—Karanta 1 Korintiyawa 5:11.

6, 7. (a) Sa’ad da muke tsai da shawara ko za mu saka hannu a wani aure da za a yi a coci, waɗanne batutuwa masu muhimmanci ne ya kamata mu tuna? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) Ta yaya za mu bayyana wa dangi da ba Mashaidi ba abin da muka gaskata da shi a batun auren coci?

6 Wataƙila ba za mu fuskanci gwaji mai tsanani kamar wanda Haruna da iyalinsa suka fuskanta ba. Amma idan aka gayyace mu zuwa coci don mu halarci da kuma yi wasu ayyuka a auren wani dangi kuma fa? Ba wani takamaiman doka a cikin Littafi Mai Tsarki da ta ce kada mu halarta, amma shin da akwai wasu ƙa’idodi ne da za su taimaka mana mu tsai da shawara da ta dace?a

7 Shawarar da muka tsai da na faranta wa Jehobah rai da kuma na kasancewa da tsarki a wannan yanayin zai iya sa danginmu da ba Shaidu ba mamaki. (1 Bit. 4:3, 4) Hakika, ba za mu so mu ɓata musu rai ba, amma zai dace mu yi musu bayani dalla-dalla amma cikin ladabi. Yana da kyau mu yi hakan tun da wuri kafin lokacin bikin. Muna iya gode musu kuma mu ce mun yi farin ciki sosai da suka ba mu gatan saka hannu a hidimomin bikin. Sai mu bayyana musu cewa ba za mu iya saka hannu ba don ba ma son mu ɓata ransu da waɗanda suka zo bikin da yake hidimomin sun shafi addini. Wannan hanya ɗaya ce da za mu guji saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma imani.

KA ƊAUKAKA JEHOBAH MAƊAUKAKIN SARKI

8. Ta yaya littafin Levitikus ya nuna cewa Jehobah Maɗaukakin Sarki ne?

8 Littafin Levitikus ya sha nuna cewa Jehobah Maɗaukakin Sarki ne. Fiye da sau 30, mun karanta cewa Allah ne ya ba da dokokin da ke cikin littafin Levitikus. Musa ya amince da hakan kuma ya yi abin da Jehobah ya umurce shi ya yi. (Lev. 8:4, 5) Hakazalika, ya kamata mu riƙa yin abin da Maɗaukakin Sarki Jehobah yake son mu yi. Ƙungiyar Allah tana taimaka mana mu yi hakan. Amma, muna iya fuskantar gwaji sa’ad da muke mu kaɗai kamar yadda Yesu ya fuskanci gwaji sa’ad da yake cikin jeji shi kaɗai. (Luk 4:1-13) Idan muka tuna cewa Allah shi ne Maɗaukaki kuma muka dogara gare shi, babu wanda zai iya sa mu bauɗe wa imani saboda tsoro.—Mis. 29:25.

9. Me ya sa aka tsani mutanen Allah a dukan ƙasashe?

9 A matsayinmu na mabiyan Kristi da Shaidun Jehobah, ana tsananta mana a ƙasashe dabam-dabam a faɗin duniya. Hakan ba abin mamaki ba ne domin Yesu ya gaya wa almajiransa: “Za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Mat. 24:9) Duk da wannan tsanantawar, muna ci gaba da wa’azi da kuma kasancewa da tsarki a gaban Jehobah. Shin me ya sa aka tsane mu duk da cewa ba ma ƙarya, ba ma rashin ɗa’a da kuma ƙetare doka? (Rom. 13:1-7) Domin mun ɗauki Jehobah a matsayin Sarkinmu! Muna bauta masa “shi kaɗai” kuma ba za mu taɓa bauɗe wa dokokinsa da ƙa’idodinsa ba.—Mat. 4:10.

10. Mene ne ya faru a lokacin da wani ɗan’uwa ya bauɗe wa imani?

10 Ƙari ga haka, mu “ba na duniya ba ne.” Saboda haka, ba ruwanmu da yaƙe-yaƙe da siyasar wannan duniya. (Karanta Yohanna 15:18-21; Ishaya 2:4.) Wasu da suka ba da kai don yin nufin Allah sun bauɗe wa imani. Da yawa cikinsu sun tuba kuma sun sake ƙulla dangantaka da Ubanmu na sama mai jin-ƙai. (Zab. 51:17) Kalilan cikinsu sun ƙi tuba. Alal misali, a lokacin Yaƙin Duniya na biyu, a ƙasar Hungary, wasu ’yan’uwanmu guɗa 160 masu shekaru ƙasa da 45 ne aka saka a kurkuku ba gaira ba dalili. Daga baya, ma’aikata sun tara su daga dukan fursunonin da ke ƙasar a wani gari kuma aka umurce su su shiga aikin soja. Yawanci cikinsu sun yi tsayin daka, amma guɗa tara sun yi rantsuwa kuma suka shiga aikin soja. Shekaru biyu bayan haka, ɗaya daga cikinsu ya tarar da kansa a cikin rukunin sojoji da aka ba su umurni su harbe wasu amintattun Shaidun Jehobah har mutuwa. Yayansa yana cikin waɗanda aka ce ya kashe! Daga baya, ba a harbe su ba.

KA YI IYA ƘOƘARINKA A BAUTAR JEHOBAH

11, 12. Ta yaya tsarin Jehobah game da ba da hadayu a Isra’ila ta dā ya shafi Kiristoci a yau?

11 Bisa ga Dokar da aka ba da ta hannun Musa, an bukaci Isra’ilawa su miƙa takamaiman hadayu. (Lev. 9:1-4, 15-21) Hadayun ba za su kasance da aibi ba domin suna nuni ga kamiltaccen hadayar Yesu. Ƙari ga haka, kowace hadaya na da tsarin da ake bi kafin a bayar. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ake bukata daga uwa da ta haifi jariri. Levitikus 12:6 ya ce: “Sa’anda kwanakin tsarkakewarta sun cika, domin namiji, ko ɗiya mace, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da ɗan tantabara, ko kurciya, domin hadaya ta zunubi, har zuwa ƙofar tent na taruwa, wurin firisti.” Ko da yake Allah ya ba da takamammun umurni, Dokar ta nuna sarai cewa shi mai ƙauna ne kuma yana nuna sanin ya kamata. Idan mahaifiyar ba za ta iya ba da ɗan rago ba, tana iya ba da kurciyoyi biyu ko ’yan tantabaru guda biyu. (Lev. 12:8) Ko da yake talaka ce, amma Allah yana ƙaunarta kamar yadda yake ƙaunar wadda ta miƙa hadaya mai tsada. Mene ne za mu koya daga wannan?

12 Manzo Bulus ya aririce ’yan’uwa masu bi su miƙa “hadaya ta yabo” ga Allah. (Ibran. 13:15) Ya kamata mu yi shelar suna mai tsarki na Jehobah da bakinmu. ’Yan’uwa maza da mata kurame suna amfani da yaren kurame don su yabi Allah. Kiristoci da ba sa iya fita daga gidajensu suna yabonsa ta wurin rubuta wasiƙu da wa’azi ta tarho da yi wa masu kula da su da kuma baƙi wa’azi. Ya kamata yabon da muke yi wa Jehobah ya dace da lafiyar jikinmu da ƙwazonmu. Amma ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu.—Rom. 12:1; 2 Tim. 2:15.

13. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa ba da rahoton wa’azi?

13 Hadayu na yabo su ne abubuwan da muke yi wa Allah da yardar rai domin muna ƙaunarsa. (Mat. 22:37, 38) Amma an ce mu riƙa ba da rahoton aikin wa’azi da muka yi. Wane irin hali ne ya kamata mu kasance da shi game da wannan tsarin? Rahoton wa’azin da muke bayarwa a kowane wata yana da alaƙa da ibada. (2 Bit. 1:7) Hakika, bai kamata mu ji cewa sai mun yi sa’o’i da yawa a wa’azi don kawai mu ba da rahoto mai kyau ba. Shi ya sa mai shela zai iya ba da minti 15 idan rashin lafiya ko tsufa ya hana shi fita wa’azi. Jehobah yana farin ciki don waɗannan mintocin da mai shelar ya ba da don hakan ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah kuma ya ɗauki gatan bauta masa da muhimmanci. Bayin Jehobah da yanayinsu ya hana su fita wa’azi ma za su iya ba da rahoto, kamar waɗannan Isra’ilawa da yanayinsu ya hana su yin hadaya da dabbobi masu tsada. Ana harhaɗa rahotannin da kowannenmu yake bayarwa don sanin adadin rahoto a faɗin duniya, kuma hakan yana taimaka wa ƙungiyar Jehobah ta shirya da wuri don cim ma bukatun da suka taso a wa’azi. Shin wannan ba ƙwaƙƙwaran dalili ba ne na ba da rahoto sa’ad da muka fita wa’azi?

NAZARI DA KUMA HADAYUNMU NA YABO

14. Ka bayyana dalilin ya sa ya kamata mu sake bincika yadda muke nazari.

14 Tattauna waɗannan ’yan darussan daga littafin Levitikus zai iya sa ka ce, ‘Oho, yanzu ne na fahimci dalilin ya sa aka saka littafin Levitikus a cikin Littafi Mai Tsarki.’ (2 Tim. 3:16) Yanzu ne za ka kuɗiri aniyyar kasancewa da tsarki, ba wai kawai don Jehobah yana bukatarmu mu yi hakan ba, amma domin yana son mu yi iya ƙoƙarinmu wajen faranta masa rai. Wataƙila abin da ka koya daga littafin Levitikus a waɗannan talifofi biyu sun ƙara sa ka kasance da sha’awar yin nazarin Nassosi sosai. (Karanta Misalai 2:1-5.) Ka yi addu’a cikin natsuwa don ka san dalilin da ya sa kake nazari. Babu shakka kana son Jehobah ya amince da hadayun yabo da kake yi. Kana ganin kamar kana ƙyale shirye-shiryen telibijin da wasannin motsa jiki da na bidiyo ko kuma wasu abubuwa su hana ka samun ci gaba a ibada? Idan haka ne, za ka iya amfana daga yin bimbini a kan wasu furuci da manzo Bulus ya yi da aka rubuta a littafin Ibraniyawa.

15, 16. Me ya sa Bulus bai yi ɓoye-ɓoye ba sa’ad da yake rubuta wasiƙa ga Kiristoci Ibraniyawa?

15 Bulus ya yi bayani dalla-dalla a lokacin da yake rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa wasiƙa. (Karanta Ibraniyawa 5:7, 11-14.) Manzon bai yi ɓoye-ɓoye ba! Ya gaya musu cewa sun “zama masu nauyin” ji. Me ya sa Bulus ya yi magana kai tsaye haka? Kamar Jehobah, Bulus yana ƙaunarsu kuma ya damu cewa sun dangana kawai ga abubuwan da suka koya da farko. Sanin waɗannan abubuwan yana da muhimmanci don su ne ainihin ginshiƙin koyarwar Kirista. Amma, suna bukatar “abinci mai-ƙarfi,” koyarwa mai zurfi don su manyanta.

16 Maimakon su manyanta don su koyar da wasu, Ibraniyawa suna bukatar wani ya koyar da su. Me ya sa? Domin sun guji “abinci mai-ƙarfi” ko kuma koyarwa mai zurfi. Ka tambayi kanka: ‘Ina ɗaukan abinci, wato koyarwa mai zurfi da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa da muhimmanci kuwa? Ina marmarin yin nazarinsu kuwa? Ko kuma ba na son yin addu’a da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai ne? Idan haka ne, yadda nake yin nazari yana cikin dalilan ne? Wajibi ne mu koyar da mutane kuma mu sa su zama almajirai, ba kawai mu yi musu wa’azi ba.—Mat. 28:19, 20.

17, 18. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa nazarin koyarwar mai zurfi da ke kama da abinci mai ƙarfi? (b) Wane ra’ayi ya kamata mu kasance da shi game da giya sa’ad da muke son mu halarci taro?

17 Yin nazarin Littafi Mai Tsarki bai da sauƙi ga da yawa a cikinmu. Hakika, Jehobah ba ya matsa wa mutanensa su yi nazari. Duk da haka, ko mun daɗe da yin baftisma ko da kwanan nan ne muka yi hakan, ya kamata mu ci gaba da yin nazarin koyarwa masu zurfi da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa. Yin hakan yana da muhimmanci idan muna so mu ci gaba da kasancewa da tsarki.

18 Idan muna son mu kasance da tsarki, wajibi ne mu yi tunani sosai a kan Nassosi kuma mu riƙa yin abin da Allah ya umurce mu. Ka tuna da ’ya’yan Haruna, Nadab da Abihu da suka “miƙa wuta irin da ba a saba” yi a lokacin da wataƙila suna maye. (Lev. 10:1, 2) Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya gaya wa Haruna bayan haka. (Karanta Levitikus 10:8-11.) Shin wannan labarin yana nufin cewa kada mu taɓa giya kafin mu halarci taro ba? Ka yi tunani a kan waɗannan batutuwan: Ba ma bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa. (Rom. 10:4) A wasu ƙasashe, ’yan’uwa sukan ɗan taɓa giya daidai wa daida sa’ad da suke cin abinci kafin su halarci taro. A lokacin Idin Ƙetarewa, an yi amfani da kofi huɗu na giya. Lokacin da Yesu ya soma yin taron Tunawa da Mutuwarsa, ya sa manzanninsa sun sha giya da ke wakiltar jininsa. (Mat. 26:27) Littafi Mai Tsarki ya haramta shan giya da yawa da kuma maye. (1 Kor. 6:10; 1 Tim. 3:8) Lamirin wasu Kiristoci da yawa ba zai bar su sha giya kafin su yi wasu abubuwa da suka shafi bautar Jehobah ba. Ko da yake yanayin Kiristoci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, abin da ya fi muhimmanci ga Kiristoci shi ne su “bambamta tsakanin masu-tsarki da marasa-tsarki” don su riƙa yin abubuwan da ke faranta wa Allah rai.

19. (a) Me ya kamata mu tuna game da yin ibada ta iyali da kuma nazari na kai? (b) Me ka kuɗiri niyyar yi don ka kasance da tsarki?

19 Akwai darussa da yawa da za mu koya idan muka bincika Kalmar Allah da kyau. Ka yi amfani da kayan bincike don ka sa ibada ta iyali da kuma nazarin da kake yi kai kaɗai ya daɗa amfanar ka. Ka ƙara iliminka game da Jehobah da nufinsa. Ka kusace shi da kyau. (Yaƙ. 4:8) Ka yi addu’a kamar yadda marubucin zabura ya yi cewa: “Ka buɗe mini idanuna, domin in duba al’ajibai daga cikin shari’arka.” (Zab. 119:18) Kada ka ƙetare dokoki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka yi biyayya da dokar Jehobah “Mai-tsarki,” kuma ka yi ƙwazo a hidima mai tsarki na “bisharar Allah.” (1 Bit. 1:15; Rom. 15:16) Ka kasance mai tsarki a waɗannan miyagun kwanaki na ƙarshe. Bari dukanmu mu kasance da tsarki a al’amuranmu kuma mu ɗaukaka Jehobah, Allah Maɗaukakin Sarki.

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2007, shafuffuka na 15-17, sakin layi na 10-15.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba