‘Mutane Waɗanda Ubangiji Ne Allahnsu’
“Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.”—ZAB. 144:15.
1. Mene ne wasu suka gaskata game da masu kirki da ke addinai dabam-dabam?
MUTANE da yawa a yau sun yarda cewa manyan addinai ba sa taimaka wa mutane. Wasu sun amince cewa koyarwar waɗannan addinai da kuma halayen mabiyansu ba su jitu da nufin Allah ba, don haka, Allah bai amince da su ba. Amma sun yarda cewa akwai mutane masu kirki a dukan addinai kuma Allah yana amincewa da bauta da suke masa. Suna gani cewa ba wajibi ba ne waɗannan mutane su ware kansu daga addinan ƙarya don su bauta wa Allah a matsayin rukuni. Shin hakan gaskiya ce? Bari mu bincika amsar ta wajen tattauna wasu labaran Littafi Mai Tsarki game da waɗanda suka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.
MUTANE DA SUKA ƊAUKI ALKAWARI DA ALLAH
2. Waɗanne mutane ne suka zama mutanen Jehobah na musamman, kuma wace alama ce ta bambanta su da sauran mutane? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)
2 Wajen shekaru 4,000 da suka shige, Jehobah ya keɓe wasu mutane a duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim, shugaban iyali da ya ƙunshi ɗarurruwan mutane shi ne “uban masu-bada gaskiya duka.” (Rom. 4:11; Far. 14:14) A wajen sarakunan ƙasar Kan’ana, shi “ba-sarauce ne mai-girma” kuma sun ɗauke shi da mutunci sosai. (Far. 21:22; 23:6) Allah ya yi alkawari da Ibrahim da kuma zuriyarsa. (Far. 17:1, 2, 19) Allah ya gaya wa Ibrahim: “Wannan shi ne alkawarina, wanda za ku kiyaye, tsakanina da ku da zuriyarka daga bayanka; za a yi ma kowane namiji a cikinku kāciya. . . . Za ya zama shaidar alkawari tsakanina da ku.” (Far. 17:10, 11) Hakika, an yi wa Ibrahim da dukan mazajen gidansa kāciya. (Far. 17:24-27) Kāciyar alama ce da ta nuna cewa zuriyar Ibrahim ce kaɗai take da dangantaka ta musamman da Jehobah.
3. Ta yaya zuriyar Ibrahim suka yawaita?
3 Jikar Ibrahim mai suna Yakubu ko kuma Isra’ila, yana da ’ya’ya maza 12. (Far. 35:10, 22b-26) Da shigewar lokaci, waɗannan ’ya’yan sun zama ubannin iyali na kabilu 12 na Isra’ila. (A. M. 7:8) Saboda yunwa, Yakubu da iyalinsa sun yi gudun hijira zuwa Masar. A lokacin, wani ɗansa mai suna Yusufu ne mai kula da harkar abinci ƙasar kuma yana da farin jini a gaban Fir’auna. (Far. 41:39-41; 42:6) Zuriyar Yakubu suka yi yawa sosai kuma aka kira su “taron al’ummai.”—Far. 48:4; karanta Ayyukan Manzanni 7:17.
JEHOBAH YA CECI MUTANENSA
4. Da farko, wace dangantaka ce ke tsakanin mutanen Masar da zuriyar Yakubu?
4 ’Ya’yan Yakubu sun yi shekaru fiye da 200 a ɓangaren Masar da ake kira Goshen. (Far. 45:9, 10) Kamar dai kusan rabin waɗannan shekarun sun yi zaman lafiya da mutanen Masar. Sun zauna a ƙananan garuruwa kuma suna kiwon tumakinsu da garkunansu. Wani Fir’auna da ya ɗauki Yusufu da mutunci ne ya amince su zauna a ƙasar. (Far. 47:1-6) Mutanen Masar sun tsani makiyaya. (Far. 46:31-34) Duk da haka, wajibi ne su yi biyayya ga Fir’auna kuma su bar Isra’ilawa su zauna a ƙasar.
5, 6. (a) Ta yaya yanayin mutanen Allah ya canja a ƙasar Masar? (b) Me ya sa ba a kashe Musa ba, kuma mene ne Jehobah ya yi wa dukan mutanensa?
5 Amma, da shigewar lokaci, yanayin ya canja. “Ananan wani sarki sabo ya ci sarauta a Masar, wanda ba ya san Yusufu ba. Ya kuwa ce da mutanensa, Ga mutanen nan ’ya’yan Isra’ila sun yi mana yawa, sun fi ƙarfinmu kuma: Sai Masarawa suka sa ’ya’yan Isra’ila su yi bauta da wuya: Suka baƙanta masu rai kuma da bauta mai-wuya, aikin kwaɓi da tubula, da kowane irin aiki a gonaki, watau dukan aikinsu, inda suka sa su su yi bauta mai-wuya.”—Fit. 1:8, 9, 13, 14.
6 Ƙari ga haka, Fir’auna ya ba da umurni cewa a kashe dukan jariran Ibraniyawa sa’ad da aka haife su. (Fit. 1:15, 16) A wannan lokacin ne aka haifi Musa. Sa’ad da yake wata uku, mahaifiyarsa ta ɓoye shi a cikin kyauraye na kogin Nilu, inda ’yar Fir’auna ta samo shi kuma ta ɗauke shi a matsayin ɗanta. A cikin rashin sani, ta yarda mahaifiyarsa Jochebed ta yi rainonsa, saboda haka, ya zama amintaccen bawan Jehobah. (Fit. 2:1-10; Ibran. 11:23-25) Jehobah ya lura da wahalar da mutanensa suke sha kuma ya yi amfani da Musa don ya cece su daga masu wulaƙanta su. (Fit. 2:24, 25; 3:9, 10) Ta hakan suka zama mutanen da Jehobah ya “fanshe” su.—Fit. 15:13; karanta Kubawar Shari’a 15:15.
MUTANE SUN ZAMA AL’UMMA
7, 8. Ta yaya mutanen Jehobah suka zama al’umma mai tsarki?
7 Ko da yake a lokacin, Allah bai mai da su al’umma ba tukuna, amma ya ɗauke su a matsayin mutanensa. Saboda haka, an umurci Musa da Haruna su faɗa wa Fir’auna cewa: “In ji Ubangiji, Allah na Isra’ila, Ka saki mutanena, domin su kiyaye idi a gareni cikin jeji.”—Fit. 5:1.
8 Jehobah ya yi amfani da annoba goma kuma ya halaka Fir’auna da rundunarsa a cikin Jar Teku don ya ceci ’ya’yan Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar. (Fit. 15:1-4) A cikin watannin uku, Jehobah ya yi alkawari da Isra’ilawa a Dutsen Sinai kuma ya ce musu: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya; . . . al’umma mai-tsarki.”—Fit. 19:5, 6.
9, 10. (a) Bisa ga Kubawar Shari’a 4:5-8, ta yaya Dokar ta bambanta Isra’ilawa da sauran mutane? (b) Mene ne Isra’ilawa suke bukata su yi don su nuna cewa su “al’umma mai-tsarki ga Ubangiji” ne?
9 Kafin Isra’ilawa su zama bayi a ƙasar Masar, an tsara su cikin ƙabilu dabam-dabam kuma shugabannin iyalai ne suke musu ja-gora. Kamar bayin Jehobah da suka rayu kafin zamaninsu, waɗannan shugabannin iyalai sun yi hidima a matsayin masu mulki, alkalai da kuma firistoci a madadin iyalansu. (Far. 8:20; 18:19; Ayu. 1:4, 5) Jehobah ya yi amfani da Musa don ya ba Isra’ilawa tsarin dokoki da ya bambanta su da sauran al’ummai. (Karanta Kubawar Shari’a 4:5-8; Zab. 147:19, 20.) Ta wannan tsarin dokoki, an keɓe wasu mutane musamman don hidimar firist, “datiɓai” suna gudanar da shari’a kuma ana girmama su don fahimi da kuma hikimarsu. (K. Sha 25:7, 8) Tsarin dokar ya tanadar wa wannan sabuwar al’ummar umurni game da bauta da kuma harkokin yau da kullum.
10 Sa’ad da Isra’ilawa suke gab da shiga Ƙasar Alkawari, Jehobah ya sake maimaita musu dokokinsa, ƙari ga haka, Musa ya gaya musu cewa: “Yau kuma Ubangiji ya shaida kai ne al’ummarsa keɓaɓiya ga kansa, kamar yadda ya alkawarta maka, za ka kuma kiyaye dukan dokokinsa; za ya maishe ka maɗaukaki bisa ga dukan al’ummai waɗanda ya halitta, cikin yabo, da suna, da girma; domin kuma ka zama al’umma mai-tsarki ga Ubangiji Allahnka.”—K. Sha 26:18, 19.
BAƘI ZA SU IYA BAUTA WA JEHOBAH
11-13. (a) Su waye ne suka soma ibada tare da mutanen Allah? (b) Mene ne baƙo zai iya yi idan yana son ya bauta wa Jehobah?
11 Ko da yake Jehobah ya zaɓi Isra’ilawa su zama al’ummarsa a duniya, amma ya ba wa baƙi dama su zauna a cikin mutanensa. Ya amince “taron tattarmuka” na mutane da ba Isra’ilawa ba, haɗe da wasu Masarawa, su tafi tare da mutanensa sa’ad da ya cece su daga ƙasar Masar. (Fit. 12:38) Sa’ad da Jehobah yake addabar Masar da annoba ta bakwai, wasu a cikin “bayin Fir’auna” sun ji tsoron maganar Jehobah kuma saboda haka, sun kasance cikin wannan babban taron mutanen da suka bar ƙasar Masar tare da Isra’ilawa.—Fit. 9:20.
12 Sa’ad da Isra’ilawa suna gab da haye Kogin Urdun don su mamaye ƙasar Kan’ana, Musa ya gaya musu cewa wajibi ne su “ƙaunaci baƙo” da ke zama a cikinsu. (K. Sha 10:17-19) Idan baƙin sun amince su bi takamammun dokokin da aka ba da ta hannun Musa, wajibi ne mutanen Allah su karɓe su da hannu bibbiyu. (Lev. 24:22) Wasu baƙi sun zama masu bauta wa Jehobah, kuma sun kasance da irin ra’ayin da Ruth ’yar Mowab ta kasance da shi sa’ad da ta gaya wa Naomi cewa: “Danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.” (Ruth 1:16) Waɗannan baƙin sun soma bauta wa Jehobah kuma an yi wa mazansu kaciya. (Fit. 12:48, 49) Jehobah ya amince su kasance a cikin al’ummarsa.—Lit. Lis. 15:14, 15.
13 Addu’ar da Sulemanu ya yi sa’ad da aka yi bikin keɓe haikalin Jehobah ya nuna cewa an tsara wa masu bauta wa Jehobah da ba Isra’ilawa ba wuri a cikin haikalin, ya ce: “Ga kuma zancen baƙo, wanda ba na jama’arka Isra’ila ba ne, sa’anda ya zo daga ƙasa mai-nisa sabili da jin labarin sunanka mai-girma, da hannunka mai-iko, da zira’arka miƙaƙiya; sa’anda sun zo, sun yi addu’a, suna fuskanta gidan nan: sai ka ji daga sama, i, wurin zamanka, ka yi bisa ga dukan abin da baƙo ya ke biɗa gareka; domin dukan al’umman duniya su san sunanka, su ji tsoronka, kamar yadda jama’arka Isra’ila su ke yi, su kuma sani wannan gidan da na gina ana kiransa da sunanka.” (2 Laba. 6:32, 33) Kamar yadda ya kasance a lokacin Yesu, duk wani baƙo da yake so ya bauta wa Jehobah zai iya yin hakan tare da mutanen Allah.—Yoh. 12:20; A. M. 8:27.
AL’UMMA DA SUKA ƘUNSHI SHAIDU
14-16. (a) A wace hanya ce Isra’ilawa suka kasance al’umma da ke ba da shaida a madadin Jehobah? (b) Mene ne ya wajaba mutanen Jehobah a yau su yi?
14 Isra’ilawa sun bauta wa Allahnsu Jehobah, alhali sauran al’ummai sun bauta wa allolinsu. A zamanin annabi Ishaya, Jehobah ya kwatanta yanayin duniya da shari’ar kotu. Ya ƙalubalance allolin al’ummai su tanadar da shaidu don a tabbata cewa su alloli ne, ya ce: ‘Bari dukan al’ummai su taru, danguna kuma su tattaru; wanene daga cikin [allolinsu] ya iya bayana wannan, ya nuna mana al’amuran da sun rigaya sun wuce? Bari su kawo shaidunsu domin su barata: ko kuwa su ji, su ce, Gaskiya ce.’—Isha. 43:9.
15 Allolin al’ummai ba su iya sun nuna cewa su alloli ne da gaske ba. Hakan ya nuna cewa su gumaka ne da ba za su iya magana da kuma tafiya ba sai wani ya yi yawo da su. (Isha. 46:5-7) Akasin haka, Jehobah ya gaya wa mutanensa Isra’ila cewa: “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, barana kuma wanda na zaɓa; domin ku sani ku ba ni gaskiya kuma, ku fahimta kuma ni ne shi; gabana ba a kamanta wani Allah ba, bayana kuma ba za a yi ba. Ni dai, ni ne Ubangiji: banda ni kuma babu wani mai-ceto. . . . Domin wannan fa ku ne shaiduna, . . . ni ne Allah.”—Isha. 43:10-12.
16 Isra’ilawa suna matsayin shaidu a gaban al’umman duniya game da batun wanda ya cancanci ya kasance Allah Maɗaukaki. Jehobah ya zaɓe su don su ba da shaida cewa shi ne Allah na gaskiya. Ya ce game da su: “Mutanen da na yi domin kaina, su ne za su bayyana yabona.” (Isha. 43:21) Su ne mutanen da aka san su da sunansa. Da yake Jehobah ne ya cece su daga ƙasar Masar, wajibi ne su ba da shaida wa mutanen duniya game da sarautarsa. Ya kamata matsayinsu ya kasance kamar yadda Annabi Mikah ya kwatanta game da mutanen Allah a sa’ad da ya ce: “Dukan kabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—Mi. 4:5.
MUTANEN DA BA SA JIN GARI
17. Ta yaya Isra’ila ta zama lalatacen dashe na baƙuwar kuringa a gaban Jehobah?
17 Abin baƙin ciki, mutanen Isra’ila sun ɓata sunan Allahnsu, Jehobah. Sun ƙyale al’umman da suke bauta wa allolin da aka yi da itace da duwatsu su rinjaye su. Wajen shekaru 2,800 da suka shige, annabi Hosiya ya ce Isra’ila tana kamar kuringa marar amfani, sai ya ƙara cewa Isra’ila tana yawaita bagadanta, kuma “zuciyarsu ta rabu biyu; yanzu laifinsu za ya tabbata.” (Hos. 10:1, 2) Kusan shekaru 150 bayan haka, Irmiya ya rubuta abin da Jehobah ya faɗa game da mutanensa marasa aminci: “Na dasa ka kuringa mai-daraja, iri mai-kyau ƙwarai: yaya fa ka juya ka zama mini lalatacen dashe na wata baƙuwar kuringa? . . . Ina allolinka da ka yi su ke? su tashi mana! idan za su iya cetonka cikin lokacin wahalarka . . . Mutanena sun manta da ni.”—Irm. 2:21, 28, 32.
18, 19. (a) Ta yaya Jehobah ya annabta cewa zai samar da sabon rukunin mutane da aka san su da sunansa? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
18 A maimakon Isra’ilawa su ba da ’ya’ya masu kyau ta wajen yin ibada ta gaskiya a matsayinsu na shaidun Jehobah masu aminci, sun bauta wa gumaka kuma suka ba da munanan ’ya’ya a sakamako. Yesu ya gaya wa munafukan shugabannin Yahudawa na zamaninsa cewa: “Za a amshe mulkin Allah daga hannunku, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Mat. 21:43) Waɗanda suke cikin “sabon alkawari” da Irmiya ya yi annabcinsa ne kawai za su iya kasancewa cikin wannan sabuwar al’umma, wato Isra’ila na Allah. Jehobah ya yi annabci game da Isra’ila na Allah da aka yi sabon alkawari da su, ya ce: Zan “zama Allahnsu, su zama mutanena.”—Irm. 31:31-33.
19 Bayan Isra’ila ta yi rashin aminci kuma kamar yadda muka ambata, Jehobah ya zaɓi Isra’ila na Allah don su zama mutanensa a ƙarni na farko. Amma, su wane ne mutanensa a yau? Ta yaya za mu iya gane waɗanda suke wa Allah ibada da gaske? Za mu tattauna wannan batun a talifi na gaba.