An Haife Su A Cikin Al’ummar Da Allah Ya Zaɓa
“Ubangiji Allahnka ya zaɓe ka ka zama al’umma keɓaɓiya a gareshi.”—KUBAWAR SHARI’A 7:6.
1, 2. Waɗanne ayyuka masu girma ne Jehobah ya aikata a madadin mutanensa, kuma wane dangantaka ne Isra’ilawa suka soma da Allah?
ASHEKARA ta 1513 K.Z., Jehobah ya shiga sabuwar dangantaka da bayinsa a duniya. A wannan shekarar, Jehobah ya kunyatar da mai iko da duniya kuma ya ceci Isra’ilawa daga bauta. Da haka, ya zama Mai Cetonsu kuma Mai Su. Kafin ya ɗauki mataki, Allah ya gaya wa Musa: “Ka ce ma ’ya’yan Isra’ila, Ni ne Ubangiji, kuma zan fishe ku daga ƙalƙashin nawayya ta Masarawa, kuma zan tsame ku daga bautassu, in panshe ku da zira’a a miƙe, da manyan hukumce hukumce: zan ɗauke ku gareni al’umma, zan zama Allah gareku.”—Fitowa 6:6, 7.
2 Ba da daɗewa ba bayan sun fito daga Masar, Isra’ilawa suka yi alkawari na dangantaka da Allahnsu, Jehobah. Maimakon ya soma sha’ani da mutane ɗaɗɗaya, iyalai, ko kuwa danguna, Jehobah ya tsara mutane, wato al’umma a duniya. (Fitowa 19:5, 6; 24:7) Ya yi tanadin dokokin da za su yi wa mutanensa ja-gora a rayuwarsu ta yau da kullum, kuma mafi muhimmanci a bautarsu. Musa ya ce musu: “Ina babbar al’umma wadda ta ke da Allah kusa da ita haka, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya ke a kowane yayin da mu ke kiransa? Ina kuma al’umma mai-girma wadda ta ke da farillai da shari’u masu-adalci haka kamar dukan wannan shari’a, wadda na sanya a gabanku yau?”—Kubawar Shari’a 4:7, 8.
An Haife Su a Cikin Al’umma ta Shaidu
3, 4. Wane dalili ne mai muhimmanci ya sa Isra’ila ta wanzu a matsayin al’umma?
3 Ƙarnuka bayan haka, Jehobah ya tuna wa Isra’ilawa ta bakin annabinsa Ishaya, game da muhimmancin wanzuwarsu a matsayin al’umma. Ishaya ya ce: “Amma yanzu, in ji Ubangiji, wanda ya halicce ka, ya Yaƙub, shi wanda ya sifanta ka, ya Isra’ila; kada ka ji tsoro, gama na panshe ka, na yi kiranka da sunanka, kai nawa ne. Gama ni ne Ubangiji Allahnka, Mai-tsarki na Isra’ila, mai-cetonka; . . . a kawo ’ya’yana daga iyakar nesa, ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya; kowanne da a ke kiransa da sunana, wanda na halicce shi kuma domin ɗaukakata; na sifanta shi, i, na yi shi. Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, barana kuma wanda na zaɓa; . . . mutanen da na yi domin kaina, su ne za su bayyana yabona.”—Ishaya 43:1, 3, 6, 7, 10, 21.
4 Don sune mutanen da aka kira da sunan Jehobah, Isra’ilawa za su zama shaidu ga ikon mallakarsa ga al’ummai. Za su zama mutanen da aka ‘halicce su domin ɗaukakar Jehobah.’ Ya kamata ‘su bayyana yabon Jehobah,’ su faɗi ayyukansa na ceto masu ban mamaki kuma su ɗaukaka sunansa mai tsarki. A taƙaice, za su zama al’ummar shaidu ga Jehobah.
5. Ta yaya ne Isra’ila ta zama al’umma keɓaɓɓiya?
5 A ƙarni na 11 K.Z., Sarki Sulemanu ya bayyana cewa Jehobah ya keɓe al’ummar Isra’ila. A cikin addu’a ga Jehobah, ya ce: “Ka keɓe su daga cikin dukan al’umman duniya su zama gādonka.” (1 Sarakuna 8:53) Kowane Ba’isra’ile yana da dangantaka mai muhimmanci da Jehobah. Musa ya taɓa gaya musu cewa: “Ku ’ya’yan Ubangiji Allahnku ne: . . . Gama kai al’umma mai-tsarki ne ga Ubangiji Allahnka.” (Kubawar Shari’a 14:1, 2) Saboda haka, Isra’ilawa matasa ba sa bukatar su keɓe rayuwarsu ga Jehobah. An haife su ne cikin keɓaɓɓun mutanen Allah. (Zabura 79:13; 95:7) Ana koyar da kowace tsara dokokin Jehobah kuma dole ne su bi ta domin alkawarin da ke tsakanin Isra’ila da Jehobah.—Kubawar Shari’a 11:18, 19.
Suna da ’Yancin Zaɓe
6. Wane zaɓi ne kowane Ba’isra’ile zai yi?
6 Ko da yake an haifi Isra’ilawa a cikin keɓaɓɓiyar al’umma, kowannensu ne zai yanke shawarar bauta wa Allah. Kafin su shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya ce musu: “Ina kira sama da ƙasa su shaida a kanku yau, na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyakka: garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka, ka ji muryatasa, ka manne masa: gama shi ne ranka, da tsawon kwanakinka: domin ka zauna cikin ƙasa wadda Ubangiji ya rantse ma ubanninka, Ibrahim, da Ishaku, da Yakub, za ya ba su ita.” (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Saboda haka, kowane Ba’isra’ile ne zai zaɓi ya ƙaunaci Jehobah, ya saurari muryarsa, kuma ya manne masa. Tun da Isra’ilawa suna da ’yancin zaɓe, za su ɗauki hakkin sakamakon zaɓin da suka yi.—Kubawar Shari’a 30:16-18.
7. Menene ya faru bayan mutuwar tsararrakin Joshuwa?
7 Zamanin Alkalai ya bayyana misali mai kyau na sakamakon aminci da rashin aminci. Kafin wannan lokacin, Isra’ilawa sun bi misali mai kyau na Joshuwa kuma an albarkace su. “Jama’ar suka bauta ma Ubangiji dukan kwanakin Joshua, da kuma dukan kwanakin datiɓai da suka wanzu bayan zamanin Joshua, waɗanda sun ga manyan ayukan Ubangiji da ya aika domin Isra’ila.” Amma bayan mutuwar Joshuwa, “sai kuma wata tsara ta tashi a bayansu, waɗanda ba su san Ubangiji ba, ko aikin da ya aika domin Isra’ila. ’Ya’yan Isra’ila fa suka aika mugunta a idanun Ubangiji.” (Alƙalawa 2:7, 10, 11) Babu shakka, wannan tsarar da ba su san komi ba sun ƙi su daraja gadōnsu na keɓaɓɓun mutane, waɗanda a madadinsu ne Jehobah Allah ya yi manyan ayyuka a dā.—Zabura 78:3-7, 10, 11.
Cika Keɓewar Kansu
8, 9. (a) Wane tsari ne zai sa Isra’ilawa su nuna keɓewarsu ga Jehobah? (b) Menene waɗanda suka yi hadaya ta son rai suke samu?
8 Jehobah ya yi wa mutanensa tanadin damar cika keɓewarsu a matsayin al’umma. Alal misali, Dokarsa ta yi tanadin yin hadayu, ko baiko, wanda wasu sun wajaba, wasu kuma son rai ne. (Ibraniyawa 8:3) Irin waɗannan hadayun sun haɗa da hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kuma hadaya ta salama waɗanda ake ba da wa da son rai, wato kyauta ga Jehobah don samun tagomashinsa da kuma nuna godiya.—Leviticus 7:11-13.
9 Waɗannan hadayu da son rai suna faranta wa Jehobah rai. An ce hadayar konawa da ta gari “shesheƙi mai-ƙamshi ke nan ga Ubangiji.” (Leviticus 1:9; 2:2) A hadaya ta salama, ana miƙawa Jehobah jini da kitsen dabbar, bayan haka, firistoci da wanda ya yi hadayar za su cinye sauran naman. Wannan abinci ne ta alama wadda ke nuna dangantaka ta salama da Jehobah. Dokar ta ce: “Sa’anda za ku miƙa sacrifice na hadayu na salama ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓe ku.” (Leviticus 19:5) Ko da yake dukan Isra’ilawa sun keɓe kansu ga Jehobah ta wajen haihuwa, waɗanda suke son su zaɓi Jehobah ya zama Allahnsu ta wajen hadaya ta son rai, suna samun ‘karɓuwa’ kuma an albarkace su.—Malachi 3:10.
10. Ta yaya ne Jehobah ya bayyana ɓacin ransa a zamanin Ishaya da Malachi?
10 Sau da yawa, keɓaɓɓiyar al’ummar Isra’ila ta yi wa Jehobah rashin aminci. Ta bakin annabinsa Ishaya, Jehobah ya gaya musu: “Ba ka ɗebo mani yan raguna domin hadayu na ƙonawa ba, ba ka girmama ni kuma da hadayunka ba. Ni ban sa ka ka yi bauta da hadaya ta gari ba.” (Ishaya 43:23) Ƙari ga haka, hadayun da aka yi don dole wadda ba ƙauna ce ta motsa wanda ya yi ta ba, ba ta da tamani a idanun Jehobah. Alal misali, ƙarnuka uku bayan mutuwar Ishaya, a zamanin annabi Malachi, Isra’ilawa suna yin hadaya da dabbobi masu aibi. Amma Malachi ya gaya musu: “Ba na jin daɗinku, in ji Ubangiji mai-runduna, ba ni kuwa karɓan baiko daga hannunku ba. . . . Kun kawo abin da kuka ƙwace da ƙarfi, da gurgu, da mara-lafiya; haka ku ke kawo hadaya; zan karɓi wannan gareku? in ji Ubangiji.”—Malachi 1:10, 13; Amos 5:22.
An Ƙi Su a Matsayin Keɓaɓɓiyar Al’umma
11. Wace dama ce aka ba Isra’ila?
11 A lokacin da Isra’ilawa suka zama keɓaɓɓiyar al’umma ga Jehobah, ya yi musu alkawari: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gareni daga cikin dukan al’umman duniya; gama dukan duniya tawa ce. Za ku zama mulki na priests a gareni, al’umma mai-tsarki.” (Fitowa 19:5, 6) Almasihun da aka yi alkawari, zai bayyana a cikinsu kuma zai ba su zarafi na farko na zama masu mulki a gwamnatin Allah. (Farawa 22:17, 18; 49:10; 2 Samuila 7:12, 16; Luka 1:31-33; Romawa 9:4, 5) Amma yawancin ’yan al’ummar Isra’ila sun ƙi su cika keɓewarsu. (Matta 22:14) Sun ƙi Almasihu kuma sun kashe shi.—Ayukan Manzanni 7:51-53.
12. Waɗanne kalamai ne na Yesu suka nuna cewa an ƙi Isra’ila a matsayin keɓaɓɓiyar al’ummar Jehobah?
12 ’Yan kwanaki kafin a kashe shi, Yesu ya gaya wa shugabannin addinin Yahudawa: “Ba ku taɓa karantawa cikin Litattafai ba, Dutsen da magina suka ƙi, shine aka maishe shi kan ƙusurwa. Wannan daga wurin Ubangiji ne, abin al’ajibi ne kuwa a idanunmu? Domin wannan ina ce muku, Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Matta 21:42, 43) Don ya nuna musu cewa Jehobah ya ƙi su a matsayin al’ummar da aka keɓe masa, Yesu ya ce: “Ya Urushalima, Urushalima, wanda ki ke kisan annabawa, kina jejjefe waɗanda an aiko a gareki! So nawa ina so in tattara ’ya’yanki, kamar yadda kaza ta kan tattara ’yan tsākinta ƙarƙashin fikafikanta, amma ba ku yarda ba! Ga shi, an bar muku gidanku kango.”—Matta 23:37, 38.
Sabuwar Al’umma Keɓaɓɓiya
13. Wane annabci ne Jehobah ya yi a zamanin Irmiya?
13 A zamanin annabi Irmiya, Jehobah ya annabta wani sabon abu game da mutanensa. Mu karanta: “Ga kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, inda zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila, da gidan Yahuda: ba dai bisa ga alkawarin da na yi da ubanninsu ba a ran nan da na kama hannunsu garin in fito da su daga ƙasar Masar: wa’adin da suka warware ko da shi ke ni ubangijinsu ne, in ji Ubangiji. Amma ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan waɗannan kwanaki, in ji Ubangiji; zan sa shari’ata a cikinsu, zan rubuta ta a cikin zuciyarsu: in zama Allahnsu, su zama mutanena.”—Irmiya 31:31-33.
14. A yaushe ne kuma don menene sabuwar keɓaɓɓiyar al’ummar Jehobah ta soma wanzuwa? Mecece sabuwar al’ummar?
14 An kafa tushen wannan sabon alkawarin sa’ad da Yesu ya mutu kuma daga baya ya miƙa jininsa mai tamani da aka zubar ga Ubansa, a shekara ta 33 A.Z. (Luka 22:20; Ibraniyawa 9:15, 24-26) Wannan sabon alkawarin ya soma aiki sa’ad da aka zubo ruhu mai tsarki a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., da kuma haihuwar sabuwar al’umma, wato “Isra’ilan gaske na Allah.” (Galatiyawa 6:16; Romawa 2:28, 29; 9:6; 11:25, 26) Sa’ad da ya rubuta wa shafaffun Kiristoci, manzo Bitrus ya ce: “Ku zaɓaɓen iri ne, priesthood basarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi: ku da ba jama’a ba ne a dā ba ku sami jinƙai ba, amma yanzu kun sami jinƙai.” (1 Bitrus 2:9, 10) Dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Isra’ila na jiki ta ƙare. A shekara ta 33 A.Z., tagomashin Jehobah ya bar Isra’ila ta duniya zuwa Isra’ila ta ruhaniya, ikilisiyar Kirista, ‘al’umma mai-fitowa da ’ya’yan’ Mulkin Almasihu.—Matta 21:43.
Keɓe Kan Kowane Mutum
15. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., wane baftisma ne Bitrus ya umurci masu sauraronsa su yi?
15 Bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., kowane mutum, Bayahude ko ɗan Al’umma, na bukatar ya keɓe kansa ga Allah kuma ya yi baftisma “cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.”a (Matta 28:19) A ranar Fentakos, manzo Bitrus ya gaya wa Yahudawa da shigaggu: “Ku tuba, a yi ma kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma.” (Ayukan Manzanni 2:38) Waɗannan Yahudawa da shigaggu suna bukatar su nuna ta baftismarsu cewa sun keɓe rayuwarsu ga Jehobah kuma sun karɓi Yesu a matsayin hanyar da Jehobah zai gafarta wa zunubansu. Suna bukatar su yarda cewa shi ne Babban Firist na Jehobah kuma shi ne Shugabansu, wato Shugaban ikilisiyar Kirista.—Kolossiyawa 1:13, 14, 18.
16. A zamanin Bulus, ta yaya ne mutane masu so, wato Yahudawa da ’Yan Al’ummai suka zama sashen Isra’ila ta ruhaniya?
16 Shekaru da yawa bayan haka, manzo Bulus ya ce: “Amma dafari ga waɗanda ke na Dimashka, da cikin Urushalima, da ko’ina cikin dukan ƙasar Yahudiya, har ga Al’ummai kuma, na furta masu su tuba, su juyo wajen Allah, su yi ayyuka waɗanda sun cancanta tubarsu.” (Ayukan Manzanni 26:20) Bayan ya rinjayi mutanen, wato Yahudawa da ’Yan Al’ummai cewa Yesu shi ne Kristi, Almasihu, Bulus ya taimaka musu su keɓe kansu kuma su yi baftisma. (Ayukan Manzanni 16:14, 15, 31-33; 17:3, 4; 18:8) Ta wajen juya wa ga Allah, waɗannan sababbin almajiran sun zama ’yan Isra’ila ta ruhaniya.
17. Wane aikin hatimci ne yake gab da ƙarewa, kuma wane aiki ne ke ci gaba cikin sauri?
17 A yau, an kusan kammala zaɓan sauran Isra’ila ta ruhaniya. Sa’ad da aka gama, za a umurci ‘mala’iku huɗun’ da suke riƙe da iskokin halaka na ‘babban tsanani’ su sake su. A yanzu, tattarawar “taro mai-girma” waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya na faruwa cikin sauri. “Waɗansu tumaki” sun yi wannan zaɓin ne da son ransu su ba da gaskiya ga “jinin Ɗan ragon” kuma su yi baftisma a alamar keɓe kansu ga Jehobah. (Ru’ya ta Yohanna 7:1-4, 9-15; 22:17; Yohanna 10:16; Matta 28:19, 20) A cikinsu akwai matasa masu yawa da iyayensu Kiristoci ne. Idan kana cikin waɗannan matasan, za ka yi marmarin karanta talifi na gaba.
[Hasiya]
a Ka dubi Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu, 2003, shafuffuka na 30-31.
A Maimaitawa
• Me ya sa ƙananan ’yan Isra’ila ba sa bukatar su keɓe kansu ga Jehobah?
• Ta yaya ne Isra’ilawa za su iya bayyana cewa suna cika keɓewarsu?
• Me ya sa Jehobah ya ƙi Isra’ilawa a matsayin keɓaɓɓiyar al’ummarsa, kuma ta yaya aka sake ta?
• Daga Fentakos na shekara ta 33 A.Z., menene Yahudawa da ’Yan Al’umma suke bukatar su yi idan suna son su zama ’yan Isra’ila ta ruhaniya?
[Hoto a shafi na 21]
An haifi ƙananan Isra’ilawa a matsayin zaɓaɓɓiyar al’ummar Allah
[Hoto a shafi na 23]
Kowane Ba’isra’ile ne zai yanke shawarar bauta wa Allah
[Hoto a shafi na 23]
Hadaya ta kyauta na ba Isra’ilawa zarafin nuna ƙaunarsu ga Jehobah
[Hoto a shafi na 25]
Bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., mabiyan Kristi sun keɓe kansu ga Allah kuma sun bayyana hakan ta baftisma