Yanzu, Ku “Jama’ar Allah Ne”
“Ku da ba jama’a ba ne a dā, amma yanzu jama’ar Allah ne.”—1 BIT. 2:10.
1, 2. Wane canji ne aka samu a Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu, kuma su waye ne suka zama sabuwar jama’ar Jehobah? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)
A FENTAKOS ta shekara ta 33 a zamaninmu, wani abu mai muhimmanci ya faru a tarihin mutanen Jehobah a duniya. An yi wani gagarumin canji. Da taimakon ruhu mai tsarki, Jehobah ya samar da wata sabuwar al’umma, wato “Isra’ila na Allah” a wannan ranar. (Gal. 6:16) Wannan ne karo na farko tun daga zamanin Ibrahim, da ba a bukaci mutanen Allah su yi kaciya da aka saba yi wa mazansu a lokacin ba. A maimakon haka, Bulus ya rubuta cewa kowanne da ke cikin wannan sabuwar al’ummar kaciyarsa “kuwa ta zuciya ce, cikin ruhu.”—Rom. 2:29.
2 Waɗanda suka soma kasancewa cikin sabuwar al’ummar nan su ne manzannin Kristi da kuma almajiransa fiye da ɗari da suka taru a gidan bene a Urushalima. (A. M. 1:12-15) Sun sami ruhu mai tsarki kuma sun zama ’ya’yan Allah shafaffu. (Rom. 8:15, 16; 2 Kor. 1:21) Hakan ya tabbatar da cewa an soma aiki da sabon alkawari da Yesu ne matsakaici kuma jinin Yesu ne ya inganta sabon alkawarin. (Luk 22:20; karanta Ibraniyawa 9:15.) Saboda haka, waɗannan almajiran ne suka zama sabuwar al’ummar Allah, wato sabuwar jama’arsa. Ruhu mai tsarki ya taimaka musu su su yi wa’azi a harsuna dabam-dabam wa Yahudawa da kuma baƙi daga Daular Roma da suka zo Urushalima don su yi Idin Fentakos. Waɗannan mutanen sun ji shafaffun nan suna wa’azi game da “ayyuka masu-girma na Allah” a harsunansu kuma sun fahimta.—A. M. 2:1-11.
SABUWAR AL’UMMAR ALLAH
3-5. (a) Mene ne Bitrus ya gaya wa Yahudawa a ranar Fentakos? (b) Ta yaya sabuwar al’ummar nan ta sami ci gaba a waɗannan shekarun?
3 Jehobah ya yi amfani da manzo Bitrus wajen taimaka wa Yahudawa da kuma baƙi masu bin addinin Yahudawa su kasance cikin wannan sabuwar al’umma, wato ikilisiyar Kirista. Bitrus ya gaya wa Yahudawa kai tsaye a ranar Fentakos cewa wajibi ne su karɓi Yesu da suka rataye bisa gungume don “Allah ya maishe shi Ubangiji da Kristi.” Sa’ad da mutane suka tambaye shi me ya kamata su yi, Bitrus ya amsa cewa: “Ku tuba, a yi wa kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi ruhu mai-tsarki kyauta kuma.” (A. M. 2:22, 23, 36-38) A wannan ranar, an sami ƙarin mutane wajen 3,000 da suka kasance cikin wannan sabuwar al’ummar, wato Isra’ila na Allah. (A. M. 2:41) Daga baya, manzannin sun ci gaba da wa’azi da ƙwazo kuma suka ci gaba da samun sakamako mai kyau. (A. M. 6:7) Ta hakan, sabuwar al’ummar ta ci gaba da samun ƙaruwa.
4 Bayan haka, an kai saƙon bishara ga Samariyawa kuma aka sami sakamako mai kyau a wurin. Filibus ya yi wa mutane da yawa baftisma amma ba su sami ruhu mai tsarki nan da nan ba. Hukuma da ke kula da ayyukan Kirista da ke Urushalima ta aika Bitrus da Yohanna zuwa ga waɗannan Samariyawan da suka zama Kiristoci kuma “suka ɗibiya masu hannuwa, suka karɓi ruhu mai-tsarki.” (A. M. 8:5, 6, 14-17) Ta haka, waɗannan Samariyawan suka zama cikin shafaffun Isra’ila na Allah.
5 A shekara ta 36 a zamaninmu, an sake yin amfani da Bitrus don ya taimaka wa wasu kuma su kasance cikin wannan sabuwar al’umma ta Isra’ila na Allah. Hakan ya faru ne sa’ad da ya yi wa wani shugaban sojojin Roma da danginsa da kuma abokansa wa’azi. (A. M. 10:22, 24, 34, 35) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bitrus yana cikin faɗin waɗannan . . . , sai ruhu mai-tsarki ya fāɗo ma dukan [’yan Al’ummai] waɗanda suna jin magana. Na kaciya kuwa da ke masu-ba da gaskiya, iyakar wanda ya zo tare da Bitrus, suka yi mamaki domin aka zuba ruhu mai-tsarki kyauta a bisa Al’ummai kuma.” (A. M. 10:44, 45) Tun daga lokacin har zuwa yanzu, an ba wa Al’ummai marasa kaciya dama su kasance cikin Isra’ila na Allah.
JAMA’A DOMIN SUNANSA
6, 7. A waɗanne hanyoyi ne waɗanda suke cikin sabuwar al’ummar suka zama jama’a ‘domin sunan’ Jehobah, kuma ta yaya suka yi hakan?
6 A wani taron da hukuma da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko suka yi a shekara ta 49 a zamaninmu, almajiri Yaƙub ya ce: “Siman [Bitrus] ya ba da labari yadda Allah ya fara ziyarci Al’ummai, domin shi ciro wata jama’a daga cikinsu domin sunansa.” (A. M. 15:14) Wannan sabuwar al’umma da aka san ta da sunan Jehobah ta ƙunshi masu bi Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba. (Rom. 11:25, 26a) Bayan haka, Bitrus ya rubuta cewa: “Ku da ba jama’a ba ne a dā, amma yanzu jama’ar Allah ne.” Bitrus ya bayyana manufar wannan sabuwar al’ummar cewa: “Amma ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.” (1 Bit. 2:9, 10) An bukace su su ɗaukaka Jehobah kuma su sanar da sunansa ga jama’a. Ƙari ga haka, an bukace su kuma su yi ƙwazo a sanar da mutane game da Jehobah, Allah Maɗaukakin Sarki.
7 Kamar yadda yake da al’ummar Isra’ila ta dā, Jehobah ya ce game da Isra’ila na Allah: “Mutanen da na yi domin kaina, su ne za su bayyana yabona.” (Isha. 43:21) Ta wurin yin shela kai tsaye cewa Jehobah ne Allah na gaskiya, waɗannan Kiristoci na farko sun fallasa allolin ƙarya na zamani. (1 Tas. 1:9) Sun yi shela game da Jehobah da kuma Yesu a “cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.”—A. M. 1:8; Kol. 1:23.
8. Wane gargaɗi ne Bulus ya yi wa mutanen Allah a ƙarni na farko?
8 Manzo Bulus, wani jarumi ne da ya kasance cikin wannan jama’a ‘domin sunan’ Jehobah. A lokacin da Bulus yake magana a gaban arna ’yan ussan ilimi, ya ba shaida da gaba gaɗi game da Jehobah Allah Maɗaukakin Sarki, ya ce: “Allah wanda ya yi duniya da abin da ke ciki duka, da ya ke Ubangijin sama da ƙasa ne.” (A. M. 17:18, 23-25) Sa’ad da Bulus yake gab da kammala tafiyarsa ta uku a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje, ya gargaɗi mutanen Allah, wato Kiristoci cewa: “Na sani bayan tashina kerketai masu-zafin hali za su shiga wurinku, ba za su kewaye wa garke ba; daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (A. M. 20:29, 30) Wannan annabcin game da ’yan ridda ya cika a ƙarshen ƙarni na farko.—1 Yoh. 2:18, 19.
9. Game da mutanen da suke amsa sunan Allah, mene ne ya faru bayan mutuwar manzanni?
9 Bayan da manzanni suka mutu, ’yan ridda sun yaɗu kuma hakan ya haifar da cococin Kiristendam. Maimakon su zama ‘jama’a . . . domin sunan’ Jehobah, waɗannan ’yan ridda sun cire sunan Allah daga juyin Littafi Mai Tsarki da yawa da suka fassara. Sun soma bin al’adun arna kuma suka ɓata sunan Allah ta wajen yaɗa koyarwar ƙarya da yaƙe-yaƙe da lalata da kuma wasu ayyuka marasa ɗa’a. Saboda haka, a shekaru da yawa bayan da ’yan ridda suka bayyana, amintattun bayin Allah kaɗan ne kawai a duniya kuma babu jama’a “domin sunansa.”
MUTANEN ALLAH SUN FARFAƊO
10, 11. (a) Mene ne Yesu ya annabta a almararsa na alkama da zawan? (b) Ta yaya almarar Yesu ta sami cika bayan shekara ta 1914, kuma wane sakamako aka samu?
10 A almararsa na alkama da zawan, Yesu ya yi annabci game da yadda ridda za ta yaɗu kuma saboda da haka, ba za a gane addini na gaskiya ba. Ya ce a “lokacin da mutane suna barci,” Shaiɗan zai shuka zawan a gonar da Ɗan mutum ya shuka alkama. Dukansu za su girma tare har “matuƙar zamani.” Yesu ya bayyana cewa “iri mai-kyau” suna wakiltar “’ya’yan Mulki,” kuma “zawan” suna wakiltar “’ya’yan mugun.” A ƙarshen zamani, Ɗan mutum zai aika “masu-girbi,” wato mala’iku, su ware alkama daga zawan. A lokacin ne za a tattara ’ya’yan Mulkin. (Mat. 13:24-30, 36-43) Ta yaya aka yi hakan, kuma ta yaya hakan ya shafi zaman mutanen Jehobah a duniya?
11 “Matuƙar zamani” ya soma a shekara ta 1914. A lokacin da yaƙin ya ɓarke a shekarar nan, shafaffun Kiristoci ko kuma “’ya’yan Mulki,” wajen dubu biyar ne kawai a lokacin, kuma Babila Babba ta hana su yin ibada. A shekara ta 1919 ne Jehobah ya ceci mutanensa kuma ya ware su daga “zawan,” ko kuma Kiristoci na ƙarya. Ya tattara “’ya’yan Mulki” ya sa suka zama rukuni kuma hakan ya cika annabcin da Ishaya ya yi cewa: “Da rana guda ɗaya ta wahalar haifuwa za a haifi ƙasa? Farat ɗaya za a haifi al’umma? Gama Sihiyona da fārin wahalarta, sai haifuwar ’ya’ya.” (Isha. 66:8) Sihiyona, wato ƙungiyar Jehobah da ta ƙunshi mala’iku ta tattara ’ya’yanta shafaffu kuma ta mai da su al’umma.
12. Ta yaya shafaffu suka nuna cewa su jama’a “domin sunan” Jehobah ne?
12 Kamar Kiristoci na farko, an bukaci shafaffu “’ya’yan Mulki” su zama shaidun Jehobah. (Karanta Ishaya 43:1, 10, 11.) Sun kasance dabam da sauran mutane don halinsu mai kyau na Kirista da kuma wa’azin “bishara . . . ta Mulki . . . domin shaida ga dukan al’ummai” da suka yi. (Mat. 24:14; Filib. 2:15) Ta hakan ne suka jawo mutane da yawa, wato miliyoyin mutane don su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.—Karanta Daniyel 12:3.
“ZA MU TAFI TARE DA KU”
13, 14. Mene ne ya wajaba waɗanda ba sa cikin Isra’ila na Allah su yi don su bauta wa Allah a hanyar da ta dace, kuma ta yaya aka annabta wannan a cikin Littafi Mai Tsarki?
13 Mun koya a talifin da ya gabata cewa a Isra’ila ta dā, baƙi za su iya bauta wa Jehobah, amma wajibi ne su yi tarayya da mutanen Allah. (1 Sar. 8:41-43) Hakazalika a yau, wajibi ne waɗanda ba sa cikin Isra’ila na Allah su yi tarayya da mutanen Jehobah, “’ya’yan Mulki” da suka ƙunshi shafaffun Shaidun Jehobah.
14 Annabawa biyu a dā sun annabta cewa mutane da yawa za su yi ibada tare da mutanen Jehobah a kwanaki na ƙarshe. Annabi Ishaya ya ce: “Dangogi da yawa kuwa za su tafi su ce, Ku zo, mu hau zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub; shi ma za ya koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa: gama daga cikin Sihiyona doka za ta fito, maganar Ubangiji kuma daga cikin Urushalima.” (Isha. 2:2, 3) Hakazalika, annabi Zakariya ya ce, “dangogi da yawa da al’ummai masu-ƙarfi za su zo domin biɗan Ubangiji mai-runduna a cikin Urushalima, su roƙi alherin Ubangiji.” Ya kwatanta su a matsayin “mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai” da za su yi ibada tare da Isra’ila na Allah, suna cewa: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”—Zak. 8:20-23.
15. Wane aiki ne “waɗansu tumaki” suke yi “tare da” Isra’ila na Allah?
15 “Waɗansu tumaki” suna ‘tafiya tare da’ Isra’ila na Allah ta wajen yin wa’azin bisharar Mulkin Allah. (Mar. 13:10) Ta hakan, sun zama jama’ar Allah da kuma “garke ɗaya” da shafaffu a ƙarƙashin Kristi Yesu, “makiyayi mai-kyau.”—Karanta Yohanna 10:14-16.
KA NEMI MAFAKA TARE DA MUTANEN JEHOBAH
16. Mene ne Jehobah zai yi da zai kai ga sashen ƙarshe na “ƙunci mai-girma”?
16 Bayan an halaka Babila Babba, za a kai wa mutanen Jehobah farmaki, kuma a lokacin za mu bukaci kāriyar da Jehobah zai tanadar wa bayinsa. Da yake wannan farmakin zai kai ga sashen ƙarshe na “ƙunci mai-girma,” Jehobah ne da kansa zai tsara yadda abubuwa za su faru kuma zai yi hakan a lokacin da ya dace. (Mat. 24:21; Ezek. 38:2-4) A wannan lokacin, Gog zai kai farmaki wa “mutanen da aka tattara daga cikin al’umman duniya,” wato mutanen Jehobah. (Ezek. 38:10-12) Wannan farmakin ne zai sa Jehobah ya hukunta Gog da magoya bayansa. Jehobah zai nuna cewa shi ne yake da ikon yin sarauta kuma zai tsarkake sunansa. Ya ce: “Zan . . . bayyana kaina a fili a gaban al’ummai da yawa; za su kuwa sakankance ni ne Ubangiji.”—Ezek. 38:18-23.
17, 18. (a) Waɗanne umurnai ne mutanen Jehobah za su samu a lokacin da Gog zai kai musu farmaki? (b) Idan muna son Jehobah ya kāre mu, mene ne ya wajaba mu yi?
17 Sa’ad da Gog ya soma kai farmaki, Jehobah zai gaya wa mutanensa: “Ku zo, mutanena, ku shiga cikin ɗakunanku, ku rufe ma kanku ƙofofi: ku ɓuya kaɗan, har fushin ya wuce.” (Isha. 26:20) A wannan lokaci mai muhimmanci, Jehobah zai ba mu umurnan da za su ceci rayukanmu kuma wataƙila waɗannan ‘ɗakuna’ da aka ambata suna da alaƙa da ikilisiyoyinmu.
18 Saboda haka, idan muna son Jehobah ya kāre mu a lokacin ƙunci mai girma, wajibi ne mu fahimta cewa Jehobah yana da jama’a a nan duniya kuma suna masa ibada a cikin ikilisiyoyi. Ya kamata mu ci gaba da goya musu baya kuma mu riƙa halartar taro a ikilisiyoyinmu. Kamar marubucin zabura, bari dukanmu mu ce: “Ceto ga Ubangiji yake: albarkarka ta zauna bisa mutanenka.”—Zab.3:8.