Gabatarwa
Mene Ne Ra’ayinka?
Shin Littafi Mai Tsarki tsohon yayi ne? Zai iya amfanarmu a yau kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane Nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne.”—2 Timotawus 3:16, 17.
Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ya bayyana yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana da kuma yadda za mu ji daɗin karanta shi.