Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 5 pp. 4-5
  • Bayani na Gaskiya Game da Mala’iku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bayani na Gaskiya Game da Mala’iku
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ku Yi Koyi da Malaꞌikun Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 5 pp. 4-5
Shugaban mala’iku da kuma wasu miliyoyin mala’iku

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?

Bayani na Gaskiya Game da Mala’iku

Za ka so ka san gaskiya game da mala’iku da inda suka fito da kuma abin da suke yi? Littafi Mai Tsarki ne zai iya ba mu amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyin. (2 Timotawus 3:16) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan?

  • Kamar yadda Allah Ruhu ne, haka ma mala’iku su ma halittun ruhu ne kuma ba su da “nama da ƙasusuwa.” Mala’iku masu aminci suna zama a sama kuma suna da gatan zuwa gaban Allah.​—Luka 24:39; Matta 18:10; Yohanna 4:24.

  • A dā, mala’iku suna canja kamaninsu zuwa na mutane don su zo su yi aikin da Allah ya ba su a duniya. Amma bayan sun gama aikin, suna canja jikinsu kuma su koma sama.​—Alƙalawa 6:11-23; 13:15-20.

  • Ko da yake Littafi Mai Tsarki yana yawan nuna cewa mala’iku maza ne, amma babu namiji ko tamace a cikinsu. Ba sa aure kuma ba sa haifan yara. Ba a haifan mala’iku kamar yadda ’yan Adam suke yi. Jehobah ne da kansa ya halicce su, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira su “’ya’yan Allah.”​—Ayuba 1:6; Zabura 148:2, 5.

  • Littafi Mai Tsarki ya ambata “harsunan mutane da na mala’iku,” kuma hakan ya nuna cewa mala’iku ma suna da nasu yaren. Ko da yake a dā Allah ya yi magana da mutane ta wurin mala’iku, amma bai amince mu bauta ko kuma mu yi addu’a ga mala’iku ba.​—1 Korintiyawa 13:1; Ru’ya ta Yohanna 22:8, 9.

  • Da akwai dubun dubban mala’iku, wataƙila sun kai biliyoyi.​—Daniyel 7:10; Ru’ya ta Yohanna 5:11.

  • Mala’iku halittu ne da suke da “iko” sosai kuma sun fi ’yan Adam ƙarfi da kuma fahimi. Suna tafiya da saurin gaske fiye da yadda za mu iya tsammani.​—Zabura 103:20; Daniyel 9:20-23.

  • Duk da cewa mala’iku suna da iko da kuma fahimi sosai, da akwai wasu abubuwan da ba su sani ba kuma ba za su iya yi ba.​—Matta 24:36; 1 Bitrus 1:12.

  • An halicci mala’iku da halaye masu kyau sosai, kuma kamar ’yan Adam suna da ’yancin yin abu mai kyau ko marar kyau. Abin baƙin ciki shi ne, wasu mala’iku sun yi tawaye da Allah kuma suka daina bauta masa.​—Yahuda 6.

Yadda Aka Tsara Mala’iku

Mika’ilu shi ne shugaban mala’iku, kuma ya fi su iko sosai. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mika’ilu wani suna ne da ake kiran Yesu Kristi.​—1 Tasalonikawa 4:16; Yahuda 9.

Seraphim suna da girma da kuma gata fiye da duka sauran mala’ikun. Suna hidima kusa da kursiyin Allah.—Ishaya 6:1-3.

Kerub ma suna da babban gata kuma suna yin ayyukan da suka jitu da halayen Allah. Suna yi wa Allah hidima.—Farawa 3:24; Ezekiyel 9:3; 11:22.

Sauran miliyoyin mala’iku su ne suke aikata duk abin da Allah Maɗaukaki ya ce su yi.a​—Ibraniyawa 1:7, 14.

a Don ƙari bayani, ka duba babi na 10 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? da kuma ratayen nan “Mika’ilu Shugaban Mala’iku,” Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi. Za ka kuma iya samunsa a www.pr418.com/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba