TARIHI
Za Mu Sami Albarka Idan Muka Yi Abin da Jehobah Yake So
Ni da mijina tare da yayana da matarsa mun ce “za mu yi hidimar!” a lokacin da aka tura mu yin wata hidima dabam. Me ya sa muka yarda mu yi wannan hidimar, kuma ta yaya Jehobah ya albarkace mu? Bari in gaya muku labarin iyalinmu.
AN HAIFE ni a garin Hemsworth da ke yankin Yorkshire a ƙasar Ingila a shekara ta 1923 kuma ina da yaya mai suna Bob. Sa’ad da nake ’yar shekara tara babanmu ya karɓo wasu littattafai da suka fallasa addinin ƙarya don ba ya son munafunci da ake yi a addinai. Abin da ya karanta ya burge shi sosai. Bayan wasu shekaru, wani mutum mai suna Bob Atkinson ya zo gidanmu kuma ya saka mana faifai da ke ɗauke da wani jawabi na Ɗan’uwa Rutherford. Sai muka gano cewa rukunin da suka wallafa waɗannan littattafan ne suka yi wannan jawabin. Iyayena kuma suka gaya wa Ɗan’uwa Atkinson ya zo ya riƙa cin abinci da yamma a gidanmu don ya riƙa amsa tambayoyinmu. Ƙari ga haka, aka gayyace mu mu riƙa halartan taro a gidan wani ɗan’uwa da ke da nisan wasu miloli kaɗan. Kuma muka yi hakan nan da nan, sai aka kafa wata ƙaramar ikilisiya a Hemsworth. Ba da daɗewa ba, masu kula da da’ira suka soma sauƙa a gidanmu kuma mukan gayyaci wasu majagaba zuwa gidanmu cin abinci. Yin tarayya da su ya taimaka mini sosai.
Da muke ƙoƙari mu soma sana’a iyalinmu, sai mahaifina yana gaya wa yayana cewa “Idan kana so ka soma hidimar majagaba, za mu daina wannan sana’ar.” Bob ya amince da hakan kuma ya soma hidimar majagaba a wani wuri sa’ad da yake shekara 21. Bayan shekara biyu, a lokacin da nake shekara 16, sai ni ma na soma hidimar majagaba. A ranar Asabar da Lahadi ina samun waɗanda muke zuwa wa’azi tare, amma a sauran ranakun, ni kaɗai nake zuwa wa’azi kuma ina amfani da katin wa’azi da kuma garmaho. Amma Jehobah ya taimaka mini kuma na sami ɗaliba da na yi nazari da ita har ta yi baftisma. Ban da haka ma, mutane da yawa a iyalinsu sun zama Shaidun Jehobah. Shekara ɗaya bayan haka, na soma hidimar majagaba ta musamman tare da Mary Henshall. An tura mu zuwa yankin Cheshire da ba a yawan yin wa’azi a wurin.
Kuma a wannan lokacin ne ake Yaƙin Duniya na Biyu kuma an bukaci mata su goyi bayan yaƙin da ake yi. Da yake mu masu hidima ne ta cikakken lokaci, mun yi zaton ba za a bukace mu mu yi hakan ba da yake wasu addinai ma ba sa hakan. Amma kotu ba ta yarda ba, kuma aka tura ni fursuna na wata ɗaya. Bayan shekara ɗaya, sa’ad da na kai shekara 19, sai na saka sunana a cikin waɗanda ba sa shiga soja saboda imaninsu. An kai ƙara na sau biyu a kotu, amma ba a same ni da laifi ba. A lokacin da nake cikin wannan yanayin na san cewa Jehobah ya taimaka mini da ruhunsa mai tsarki don in kasance da ƙarfin hali.—Isha. 41:10, 13.
NA SAMI ABOKIN YIN WA’AZI
A shekara ta 1946 ne ni da Arthur Matthews muka haɗu. Bayan ya yi wata uku a fursuna don ya ƙi shiga soja saboda imaninsa, sai ya je hidima da ƙaninsa mai suna Dennis wanda yake hidimar majagaba ta musamman a birnin Hemsworth. Tun suna yara, mahaifinsu ya koya musu game da Jehobah kuma suka yi baftisma a lokacin da suke matasa. Bai daɗe ba aka tura Dennis yin wa’azi a ƙasar Ireland kuma ya bar abokin wa’azinsa Arthur. Da yake wannan matashin yana da ƙwazo da kuma halin kirki, sai iyayena suka faɗa masa ya zo ya zauna a gidanmu. Kuma idan na ziyarci iyayena, ni da Arthur ne muke wanke kwanuka bayan an gama cin abinci. Daga nan sai muka soma rubuta wa juna wasiƙa. A shekara ta 1948 an sake tura Arthur fursuna na watanni uku. Mun yi aure a watan Janairu a shekara ta 1949 kuma muka ƙudiri aniyar yin hidima ta cikakken lokaci muddar ranmu. Mun mai da hankali don kada mu riƙa kashe kuɗi a banza kuma muna yin amfani da lokacin hutu wajen yin aiki a lambu don mu samu kuɗin da zai taimaka mana mu ci gaba da hidimar majagaba.
A birnin Hemsworth bayan aurenmu a shekara ta 1949
Bayan fiye da shekara ɗaya, an tura mu yin hidima a arewacin ƙasar Ireland, da farko mun je garin Armagh bayan hakan muka je birnin Newry, kuma ’yan Katolika ne suke zama a garuruwan. Mutanen ba sa son wasu addinai don haka, muna mai da hankali sosai kafin mu yi wa’azi. Muna yin taro ne a gidan wasu ma’aurata kuma daga gidanmu zuwa wurin taron kilomita 16 ne. Mutane takwas ne suke halartan taron. A wasu lokuta muna kwana a wurin, kuma a ƙasa muke kwana, idan gari ya waye, sai mu ci abinci. Muna farin ciki yanzu don akwai Shaidun Jehobah da yawa a wurin.
“ZA MU YI HIDIMAR!”
Ƙanina da matarsa mai suna Lottie sun kwan biyu suna hidimar majagaba ta musamman a arewancin Ireland. Kuma a shekara ta 1952 mu huɗun muka halarci taron yanki a birnin Belfast. Mun zauna a gidan wani ɗan’uwa tare da Pryce Hughes wanda a lokacin shi ne mai kula da ofishin Shaidun Jehobah da ke Birtaniya. Akwai wata rana daddare da muka tattauna game da wata sabuwar ƙasida mai suna God’s Way Is Love kuma an wallafa wannan ƙasidar ne musamman don mutanen Ireland. Ɗan’uwa Hughes ya faɗa cewa yana da wuya a yi wa ’yan Katolika da suke Jamhuriyar Ireland wa’azi. Ana koran ’yan’uwa daga gidajensu kuma firistocin suna zuga mutane su riƙa tsananta wa Shaidun Jehobah. Ɗan’uwa Pryce ya ce “muna bukatar ma’aurata masu mota don su je kamfen na rarraba wannan ƙasidar a ƙasar gabaki ɗaya.”a Mu kuma muka amsa muka ce “Za mu yi hidimar!” Wannan yanayin ne ya sa muka yi furucin da aka ambata ɗazu.
Tare da wasu majagaba a kan wata babur
A birnin Dublin, gidan da majagaba suke yawan zama shi ne gidan Mama Rutland wata ’yar’uwa mai aminci da ta bauta wa Jehobah na shekaru da yawa. Mu ma mun je gidan kuma muka zauna na ɗan lokaci kuma muka sayar da wasu kayakinmu. Bayan haka, mu huɗu muka hau babur na Bob don mu je neman motar da za mu saya, mun sami wata tsohuwar mota sai muka saya. Bayan haka, muka gaya wa mutumin ya kawo mana motar don ba mu iya tuƙa mota ba. Arthur bai yi barci ba a wannan daren, don ya zauna a kan gado yana ta tunanin yadda zai riƙa ja da kuma canja giyar motar. Da wayewar gari, Arthur yana ƙoƙarin ya fito da motar daga gareji sai Mildred Willett wadda take hidima a ƙasar waje (daga baya ita ce ta auri ɗan’uwa John Barr) ta zo. Kuma ta iya tuƙa mota, sai ta taimaka mana mu koyi tuƙa mota kuma bayan haka muna shirye mu tafi!
Motarmu da kuma gidanmu mai kama da tirela
Bayan wannan, mun bukaci wurin kwana. ’Yan’uwa sun gargaɗe mu kada mu riƙa kwana a cikin tirela don masu tsananta mana suna iya cinna masa wuta. Saboda haka, mun yi iya ƙoƙarinmu don mu samu gidan haya amma ba mu samu ba. A wannan daren mu huɗun mun kwana a cikin mota. Washe gari, gidan da muka samu shi ne wata tirela da aka saka gadaje biyu a ciki. A gonar wasu abokanmu muke faka tirelar wato gidan namu. Muna yin wa’azi har zuwa wurare masu nisan kilomita 16 zuwa 24. Bayan mun komo, sai mu yi nazari da mutanen da muka faka tirela a gonarsu.
Mun ziyarci duka gidajen da suke kudu maso gabashin ƙasar ba tare da tashin hankali ba. Kuma mun rarraba littattafai fiye da 20,000. Bayan haka, muna tura sunayen mutanen da suke son a yi nazari da su zuwa ofishinmu da ke Birtaniya. Muna farin ciki sosai cewa yanzu akwai Shaidu da yawa a wurin.
MUN KOMA INGILA DAGA BAYA MUKA JE SCOTLAND
Bayan wasu shekaru, an tura mu yin hidima a kudancin Landan. Bayan wasu makonni, an kira Arthur daga ofishinmu da ke Birtaniya kuma aka ce masa gobe zai soma hidimar mai kula da da’ira! Bayan an horar da shi na mako ɗaya, sai muka tafi zuwa yankin da za mu yi hidimar a ƙasar Scotland. Don haka, Arthur bai samu lokacin shirya jawabansa ba. Amma ya kasance a shirye ya yi duk wani abin da aka ce masa ya yi a hidimar Jehobah. Mun ji daɗin hidimar da muka yi sosai. Mun yi shekaru muna yin wa’azi a yankin da babu masu wa’azi, amma yanzu muna farin cikin kasancewa tare da ’yan’uwa.
A lokacin da aka gayyaci Arthur zuwa makarantar Gilead a shekara ta 1962, abin ya ƙulle mana kai don makarantar na watanni goma ne kuma shi kaɗai ne zai je. Mun yanke shawara cewa zai dace ya halarci makarantar. Sai aka tura ni yin hidimar majagaba ta musamman a birnin Hemsworth da yake Arthur ba ya nan. Da ya dawo bayan shekara ɗaya, an tura mu hidimar mai kula da gunduma a ƙasar Scotland da arewacin Ingila da kuma na Ireland.
MUN SOMA WATA SABUWAR HIDIMA A IRELAND
A shekara ta 1964, an ce Arthur ya soma hidima a matsayin mai kula da ofishin Shaidun Jehobah da ke Jamhuriyar Ireland. Da farko na ji tsoron zuwa Bethel don ina son hidimar da muke yi na masu ziyara. Amma yanzu ina farin ciki cewa na yi hidima a Bethel. Babu shakka, idan ka amince ka yi duk wata hidima da Jehobah ya ba ka, zai albarkace ka sosai. A Bethel na yi aiki a ofishi da aikin tsabtacce wurare da aikin jera littattafai da kuma dafa abinci. Ban da haka ma, mun yi hidimar mai kula da gunduma na ɗan lokaci kuma hakan ya taimaka mana mu haɗu da ’yan’uwa da yawa a ƙasar. Haɗuwa da su da kuma ganin yadda ɗaliban da muka yi nazari da su suke samun ci gaba a ibadarsu ga Jehobah, ya sa mu farin ciki sosai. Babu shakka, mun sami albarka sosai!
LOKACI MAI MUHIMMANCI A TARIHIN MUTANEN JEHOBAH A IRELAND
A shekara ta 1965 ne aka yi taro na ƙasashe na farko a ƙasar Ireland a birnin Dublin.b Ko da yake an tsananta mana sosai, amma Jehobah ya albarkaci taron. Mutane 3,948 ne suka halarci taron kuma mutane 65 ne suka yi baftisma. An tura wa duka ’yan’uwan da suka karɓi baƙi 3,500 a gidajensu wasiƙu don a gode musu. Kuma mutanen da suka ba da gidajensu sun yaba wa baƙin don hali mai kyau da suka nuna. Wannan lokaci ne mai muhimmanci a tarihin mutanen Jehobah a Ireland.
Arthur yana gai da ɗan’uwa Nathan Knorr sa’ad da ya halarci taron da aka yi a shekara ta 1965
Arthur yana sanar da fitowar Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki a yaren Gaelic a shekara ta 1983
A shekara ta 1966, an haɗa ofishin Shaidun Jehobah da ke arewa da kuma kudancin Ireland a ƙarƙashin ofishin da ke ƙasar Dublin. Wannan abin da ya faru ya nuna cewa mu Shaidun Jehobah ba ma nuna bambanci. Amma siyasa da addini ta sa mutanen wurin ba su da haɗin kai. Ban da haka ma, mun yi farin cikin ganin yadda ’yan Katolika da yawa suka soma bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwan da a dā ’yan Furotestan ne.
AN CANJA HIDIMARMU GABAKI ƊAYA
Rayuwarmu ta canja a shekara ta 2011 a lokacin da aka haɗa ofishin da ke Birtaniya da na Ireland kuma aka ce mu je hidima a ofishinmu da ke Landan. A lokacin na damu sosai saboda Arthur yana rashin lafiya. An gano cewa yana da cutar da ake kira Parkinson. A ranar 20 ga watan Mayu na shekara ta 2015 ne mijina da muka yi shekara 66 tare ya rasu.
A shekarun da suka shige, na yi baƙin ciki sosai da kuma makoki. Ina kewar Arthur sosai, domin a dā shi yake ƙarfafa ni. Amma irin wannan yanayi da na sami kaina a ciki ya sa na kusaci Jehobah sosai. Kuma sanin cewa mutane da yawa sun yi ƙaunar Arthur ya ƙarfafa ni sosai. Abokanmu da ke Ireland da Birtaniya har ma da Amirka sun turo mini wasiƙu don su ƙarfafa ni. Ban da hakan ma, ɗan’uwan Arthur mai suna Dennis da matarsa mai suna Mavis da kuma yaran yayana masu suna Ruth da kuma Judy sun taimaka mini sosai.
Amma nassin da ya fi ƙarfafa ni shi ne Ishaya 30:18. Wurin ya ce: “Ubangiji fa za ya yi sauraro, domin shi yi maku alheri, za ya fa ɗaukaka, domin shi yi maku jinƙai: gama Ubangiji Allah mai-shari’a ne; masu-albarka ne dukan waɗanda ke sauraronsa.” Sanin cewa Jehobah yana jiran lokacin da zai magance matsalolin ’yan Adam ya kuma ba mu wata hidima a sabuwar duniya yana ƙarfafa ni sosai.
Idan na yi tunanin irin rayuwar da muka yi, ina ganin yadda Jehobah ya ja-goranci hidimar da muka yi a Ireland kuma ya albarkace ta. Gata ce babba da na kasance cikin mutane da suka yi hidima a ƙasar nan. Babu shakka, idan muka yi duk wata hidima da Jehobah ya ba mu, zai albarkace mu sosai.
a Ka duba 1988 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 101-102.
b Ka duba 1988 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 109-112.