Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w21 Oktoba pp. 29-31
  • 1921​—Shekaru Dari da Suka Shige

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1921​—Shekaru Dari da Suka Shige
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MASU WA’AZI DA ƘARFIN ZUCIYA
  • YADDA AKA TAIMAKI MUTANE SU YI NAZARI DA IYALINSU KO KUMA SU KAƊAI
  • WANI SABON LITTAFI!
  • AIKIN DA KE GABA
  • Za Mu Sami Albarka Idan Muka Yi Abin da Jehobah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • 1922​—Shekaru Dari da Suka Shige
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Abin da Tsara Bakwai na Iyalinmu Suka Gāda
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • 1923​—⁠Shekaru Dari da Suka Shige
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
w21 Oktoba pp. 29-31

1921 Shekaru Ɗari Da Suka Shige

GA TAMBAYAR da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1921 ta yi wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, ta ce: “Wane aiki ne musamman yake jiranmu a wannan shekarar?” Sai hasumiyar tsaron ta ba da amsa ta wajen yin ƙaulin Ishaya 61:​1, 2, don ta tuna musu aikin da aka ba su na yin wa’azi. Nassin ya ce: “Ubangiji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta, . . .  in yi shelar shekara ta alherin Ubangiji, da ranar sakaiya ta Allahnmu.”

MASU WA’AZI DA ƘARFIN ZUCIYA

Ƙarfin zuciya ne ya taimaka wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su yi wa’azi. Ƙari ga “shelar bishara,” sun bukaci su yi shelar “ranar sakaiya” ga mugaye.

Wani ɗan’uwa mai suna J. H. Hoskin wanda ya zauna a Kanada, ya yi wa’azi da ƙarfin zuciya duk da cewa an yi hamayya da shi. A farkon shekara ta 1921, ya haɗu da wani mai bishara na cocin Methodist. Ɗan’uwa Hoskin ya soma zancensa da cewa: “Bari mu tattauna Kalmar Allah ba tare da gardama ba. Kuma ko da ba mu amince da juna a kan wasu abubuwa ba, ba sai mun yi faɗa ba.” Amma hakan bai faru ba. Ɗan’uwa Hoskin ya faɗi abin da ya faru, ya ce: “Jim kaɗan bayan mun soma tattaunawa, sai ya bugi ƙofa da ƙarfi, har na ɗauka cewa gilashin ƙofar zai fashe.”

Sai mai bisharar ya yi ihu ya ce: “Me ya sa ba za ka je ka yi wa arna wa’azi ba?” Ɗan’uwa Hoskin bai tanka masa ba. Amma da ya kama hanya, sai ya gaya wa kansa cewa, ‘Ai na ɗauka da arne ne nake magana!’

Washegari da mai bisharar yake wa’azi a cocinsa, sai ya soma zagin Ɗan’uwa Hoskin. Ɗan’uwa Hoskin ya tuna da abin da ya faru, kuma ya ce: “Ya ce ni ɗan zamba ne kuma ya kamata a kashe ni.” Hakan bai sa ɗan’uwanmu ya daina yin wa’azi ba, amma ya yi wa’azi ga mutane da yawa. Ya ce: “Na ji daɗin yin wa’azi a wurin sosai. Har wasu mutane ma sukan ce mini, ‘Mun san kana aikin Allah ne,’ kuma sukan ce za su iya taimaka mini da abubuwan da nake bukata.”

YADDA AKA TAIMAKI MUTANE SU YI NAZARI DA IYALINSU KO KUMA SU KAƊAI

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sukan wallafa tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki da amsoshinsu a cikin mujallar da yanzu muke kiransa Awake!, don su taimaka wa mutane su daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki. An tsara wasu tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki don iyaye su tattauna su da yaransu. Iyaye za su yi wa yaransu tambayoyin, sa’an nan su taimaka musu su bincika amsoshin daga Littafi Mai Tsarki. Wasu tambayoyi kamar “Littattafai nawa ne a cikin Littafi Mai Tsarki?,” sun koyar da wasu abubuwa game da tsarin Littafi Mai Tsarki. Wasu tambayoyi kuma kamar “Ya kamata kowane Kirista ya sa rai cewa za a tsananta masa?,” sun taimaka wa matasa su riƙa yin wa’azi da ƙarfin zuciya.

Akwai kuma tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki da amsoshin da aka shirya don waɗanda suka fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. An saka amsoshin a cikin kundi na farko na littafin nan Studies in the Scriptures. Mutane da yawa sun amfana daga tambayoyin. Amma daga baya, an yi sanarwa cewa za a daina wallafa tambayoyin. Me ya sa aka daina wallafa tambayoyin?

WANI SABON LITTAFI!

Littafin nan The Harp of God

Wani kati ɗauke da inda aka ce mutum ya karanta

Katin da ke ɗauke da tambayoyi

’Yan’uwa da suke ja-goranci sun gano cewa mutane za su fi amfana idan aka koya musu batutuwa ɗaya bayan ɗaya. Don haka, an wallafa littafin nan The Harp of God a watan Nuwamba, 1921. An ba waɗanda suka karɓi littafin damar bin tsarin nazari da za su iya yi da kansu. Wannan tsarin bincike ya taimaka wa mutane su koyi game da alkawarin da Allah ya yi na ba wa ’yan Adam rai na har abada. Yaya ake yin nazari da littafin?

Idan mutum ya karɓi littafin, za a haɗa masa da wani ƙaramin kati da zai nuna masa inda zai karanta a cikin littafin. Bayan mako ɗaya, sai a aika masa wani kati kuma da ke ɗauke da tambayoyi a kan abin da ya karanta. A ƙarshen katin, zai ga wurin da zai karanta a mako na gaba.

Kowane mako har tsawon makonni 12, ikilisiyar da ke kusa da ɗalibin za ta riƙa tura masa kati. A yawancin lokuta, tsofaffi da waɗanda ba za su iya zuwa wa’azi gida-gida ba ne suke rarraba katin. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Anna K. Gardner daga garin Millvale, a Pennsylvania na ƙasar Amirka, ta ce: “Sa’ad da aka fitar da littafin nan The Harp of God, ’yar’uwata mai suna Thayle wadda gurguwa ce, ta sami damar aika wa mutane katunan da ke ɗauke da tambayoyi kowane mako.” Idan mutum ya gama nazari da katin, sai wani daga ikilisiya da ke kusa da shi ya ziyarce shi don ya taimaka masa ya daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki.

Thayle Gardner a kan keken guragu

AIKIN DA KE GABA

A ƙarshen shekarar, Ɗan’uwa J. F. Rutherford ya rubuta wasiƙa ga dukan ikilisiyoyi. A cikin wasiƙar, ya ce: “A wannan shekarar ne aka fi yin wa’azi, kuma wa’azin ya taimaka wa mutane sosai.” Sai ya daɗa da cewa: “Da sauran aiki sosai da ya kamata a yi. Ku ƙarfafa wasu su ma su saka hannu a wannan hidima mai albarka.” A bayyane yake cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun bi wannan shawarar, domin a 1922, sun yi wa’azin Mulkin Allah yadda ba a taɓa yi ba.

Abokai Masu Ƙarfin Zuciya

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun nuna ƙauna ta wajen taimaka wa juna. ’Yan’uwa sun nuna cewa ba sa jin tsoro a “kwanakin masifa” kamar yadda za mu gani a wannan labarin da ke gaba.​—K. Mag. 17:17.

A ranar Talata, 31 ga Mayu, 1921, a birnin Tulsa da ke Oklahoma a Amirka, an kama wani mutum baƙin fata aka saka shi a kurkuku domin ana zargin shi da kai ma wata Baturiya hari. Bayan haka, wasu Bature fiye da 1,000 sun yi faɗa da baƙaƙen fata da ba su kai su yawa ba. Ba da daɗewa ba, faɗar ta yaɗu zuwa wani unguwar da ake kira Greenwood inda baƙaƙen fata ne suka fi yawa. An yi sata a gidaje da kuma shaguna fiye da 1,400, kuma bayan hakan aka ƙona su ƙurmus. Rahotanni sun ce mutane 36 ne suka mutu, amma gaskiyar ita ce wataƙila mutane wajen 300 ne aka kashe. Daga baya an kira wannan rikicin Tulsa Race Massacre.

Wani Ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai suna Richard J. Hill, wanda baƙin fata ne kuma yana zama a Greenwood ya ba da labarin abin da ya faru. Ya ce: “Kafin a soma faɗa da daren, mun yi taron ikilisiya kamar yadda muka saba yi. Bayan mun gama taron, sai muka ji ana harbe-harbe a cikin unguwar. An ci gaba da yin hakan har tsakar dare.” Washegari ranar Laraba da safe, wato 1 ga Yuni, yanayin ya daɗa muni. “Wasu mutane sun zo sun ce mana idan muna so mu tsira, gwamma mun kama hanya nan tāke zuwa wani ginin gwamnati da ake kira Convention Hall.” Hakan ya sa Ɗan’uwa Hill da matarsa da yaransu biyar sun gudu zuwa ginin Convention Hall. A wurin, sojojin da gwamnati ta tura sun kāre baƙaƙen fata wajen 3,000.

A daidai lokacin, Ɗan’uwa Arthur Claus ya ɗauki matakin da ya nuna cewa yana da ƙarfin zuciya. Ɗan’uwa Claus ya ce: “Da na ji cewa ana ƙona gidaje da shagunan mutane a Greenwood, sai na ce bari in je in ga yadda abokina Ɗan’uwa Hill yake.”

Ɗan’uwa Arthur Claus ya yi amfani da littafin nan The Harp of God, wajen koya ma yara 14 game da Littafi Mai Tsarki

Sa’ad da Ɗan’uwa Claus ya isa gidan, sai ya haɗu da wani Bature maƙwabcin Ɗan’uwa Hill yana riƙe da bindiga. Maƙwabcin wanda shi ma abokin Ɗan’uwa Hill ne ya ɗauka cewa Ɗan’uwa Claus yana cikin masu faɗan. Mutumin ya daka wa Ɗan’uwa Claus tsawa ya ce: “Me ya kawo ka nan?”

Ɗan’uwa Claus ya tuna abin da ya faru kuma ya ce: “Da a ce ban ba shi amsar da ta dace ba, da ya harbe ni. Na gaya masa cewa ni abokin Ɗan’uwa Hill ne kuma na saba zuwa gidan shi.” Ɗan’uwa Claus da mutumin sun kāre gidan Ɗan’uwa Hill.

Ba da daɗewa ba, Ɗan’uwa Claus ya gano cewa Ɗan’uwa Hill da iyalinsa suna Convention Hall. An gaya wa Ɗan’uwa Claus cewa babu wani baƙin fatan da zai iya barin wurin sai da izinin sojan da ke kula da wurin, wato janar Barrett. Ɗan’uwa Claus ya ce: “Da ƙyar na samu na ga janar ɗin. Da na gaya masa cewa zan so in ɗauki iyalin daga wurin, sai ya tambaye ni, ya ce: ‘Za ka kāre iyalinsa kuma ka biya bukatunsu?’ Hakika da farin ciki na ce masa e.”

Sa’ad da Ɗan’uwa Claus ya sami izinin, sai ya je Convention Hall ba tare da ɓata lokaci ba. Da ya nuna ma wani hafsan soja izinin, sai mutumin ya ce: “Kai, janar da kansa ne fa ya sa hannu! Ka san cewa kai ne mutum na farko da ya soma fitar da mutane daga nan?” Sai Ɗan’uwa Claus da hafsan ɗin suka nemi Ɗan’uwa Hill da iyalinsa kuma suka same su. Ɗan’uwa Hill da iyalinsa suka shiga motar Ɗan’uwa Claus kuma ya kai su gida.

“Babu wani ɗan’uwa da ya ɗauka cewa ya fi wani”

Ɗan’uwa Claus ya tabbatar cewa Ɗan’uwa Hill da iyalinsa sun sami kāriya. Da mutane suka ga yadda Ɗan’uwa Claus ya nuna ƙarfin zuciya da kuma ƙauna, sai hakan ya burge su sosai. Ɗan’uwa Claus ya ce: “Maƙwabcin da ya kāre gidan Ɗan’uwa Hill ya soma daraja Shaidun Jehobah fiye da dā. Mutane da yawa sun fara son saƙon Mulkin Allah domin sun ga cewa ba mu bar bambancin launin fata ya raba kanmu ba, kuma babu wani ɗan’uwa da ya ɗauka cewa ya fi wani.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba