Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp18 Na 1 pp. 12-13
  • 3 Zai Sa Ka Jimre da Matsaloli

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 3 Zai Sa Ka Jimre da Matsaloli
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • CUTA MAI TSANANI
  • BAƘIN CIKI
  • Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Yin Addu’a
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su
    Labarai
  • Ta Karfafa Mutane duk da Rashin Lafiyarta
    Labarai
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
wp18 Na 1 pp. 12-13
Wata mata tana kuka a makabarta; wata mata a keken guragu tana saurarar wa’azi

3 Zai Sa Ka Jimre da Matsaloli

Akwai wasu matsalolin ba za mu iya guje musu ba balle ma mu magance su. Alal misali, idan wani ɗan’uwanka ya rasu ko kuma kana fama da cuta mai tsanani, ba abin da za ka iya yi sai dai ka jimre kawai. Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka a irin wannan yanayi mai wuya?

CUTA MAI TSANANI

Rose ta ce: “Ina da wata cuta da na gāda daga iyayena, don haka, kullum ina cikin ƙunci. Ba na jin daɗin rayuwa yadda ya kamata.” Abin da ya fi damunta shi ne, a wasu lokuta ba ta iya mai da hankali wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suka shafi ibada. Amma furucin Yesu da ke Matta 19:26 ya taimaka mata sosai. Wurin ya ce: “Ga Allah dukan abu ya yiwu.” Rose ta fahimci cewa akwai hanyoyi da yawa na yin nazari. Da yake ciwon da take da shi yana sa a wasu lokuta ba ta iya nazarin Littafi Mai Tsarki, sai ta soma sauraron sautin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu.a Ta ce: “Da a ce ban yi hakan ba, da ban san yadda zan iya kyautata dangantakata da Jehobah ba.”

Furucin da ke 2 Korintiyawa 8:12 ya ƙarfafa Rose a lokacin da take baƙin ciki don ba ta iya yin ayyukan da take yi a dā. Ayar ta ce: “Gama idan nufi yana nan, abin karɓa ne gwargwadon abin da ke wurin mutum, ba gwargwadon abin da ba shi da shi” ba. Waɗannan kalaman sun tuna wa Rose cewa Allah yana jin daɗin abin da take yi domin tana yin iya ƙoƙarinta.

BAƘIN CIKI

Delphine da aka ambata a baya ta ce: “Bayan da ’yata mai shekara 18 ta rasu, na yi baƙin ciki sosai domin ban taɓa sanin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ita ba. Amma abubuwa ba za su taɓa kasancewa yadda suke a dā ba.” Furucin da ke Zabura 94:19 ya ƙarfafa ta sosai. A wurin marubucin zabura ya ce wa Allah: “A cikin yawan tunani da ke cikina ta’aziyyarka suna ji wa raina daɗi.” Ta ce, “Na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in san abubuwan da zan riƙa yi da za su taimaka mini in daina baƙin ciki.”

Sai ta soma ba da kai don ta taimaka a hidimar Jehobah. Bayan wani lokaci, ta kwatanta kanta da kala da yara suke amfani da ita. Za a iya yin amfani da kala ko da ta karye. Haka ma yake da yanayinta, ko da yake tana ganin ta naƙasa amma ta fahimci cewa za ta iya taimaka ma wasu. Ta ce: “Na fahimci cewa idan na yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da shawarar da ke cikinsa don in ƙarfafa ɗalibaina, Jehobah yana amfani da wannan hanyar don ya ƙarfafa ni.” Sai ta rubuta sunayen wasu a Littafi Mai Tsarki da su ma suka yi baƙin ciki sosai. Kuma ta ce: “Babu shakka, dukansu sun yi addu’a sosai ga Jehobah.” Ƙari ga haka, ta fahimci cewa, “ba za mu iya samun taimako ba idan ba ma karanta Littafi Mai Tsarki.”

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Delphine ta fahimci wani abu kuma. Me ke nan? Ta fahimci muhimmancin mai da hankali ga abin da zai faru a nan gaba ba abin da ya riga ya faru ba. Begen da muke da shi a littafin Ayyukan Manzanni 24:15 ya ƙarfafa ta sosai. Wurin ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.” Shin tana da tabbaci cewa Jehobah zai tayar da ’yarta ne? Delphine da kanta ta ba da amsar: “Ina ganin ’yata a sabuwar duniya. Kuma ina da tabbaci cewa Jehobah zai tayar da ita a daidai lokacinsa. Ina ganin mu biyun a lambunmu a aljanna kuma ina ƙaunar ta kamar lokaci na farko da na gan ta.”

a Muna da irin waɗannan sautin a dandalinmu na jw.org.

Littafi Mai Tsarki zai ƙarfafa ka a lokacin da kake baƙin ciki

TA YAYA ALLAH ZAI TAIMAKA MANA?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa dalla-dalla. Ya ce: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira bisa gare shi, ga dukan waɗanda suke kira gare shi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.” (Zabura 145:​18, 19) Shin wannan furucin ba abin ƙarfafa ba ne? To, ta yaya Jehobah yake jin addu’ar waɗanda suke bukatar taimako?

TA WURIN BA MU ƘARFI:

Matsaloli suna iya sa mu sanyin gwiwa kuma mu ji ba mu da wani ƙarfi. Hakan yana iya shafan lafiyarmu da tunaninmu da kuma ibadarmu. (Misalai 24:10) Amma Jehobah “yana ba da ƙarfi ga masu-kasala: ga wanda ba shi da iko.” (Ishaya 40:29) Manzo Bulus da ya fuskanci matsaloli da yawa ya ce: “Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafa ni.” (Filibiyawa 4:13) Ruhu mai tsarki ne ya ƙarfafa Bulus. Kai ma za ka iya yin addu’a don Allah ya ba ka ruhu mai tsarki.​—Luka 11:13.

TA WURIN BA MU HIKIMA:

Me za ka yi idan kana bukatar taimako wajen fahimtar Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za ka iya yin amfani da shawarar da ke ciki? Almajiri Yaƙub ya ce: “Amma idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) Za ka iya yin abin da ka yi addu’a a kai idan kana karanta Littafi Mai Tsarki kuma kana yin amfani da abin da ka karanta. (Yaƙub 1:​23-25) Idan ka yi hakan, za ka fahimci cewa shawararsa tana sa mutum ya kasance da hikima.

YANA SA MU KASANCE DA SALAMA:

Jehobah zai iya kwantar maka da hankali ko da kana baƙin ciki sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filibiyawa 4:​6, 7) Zai dace ka yi addu’a don Jehobah ya sa ka kasance da salama, ko ba haka ba?

Wane mataki ne za ka ɗauka idan ba a iya magance matsalolinka nan da nan ba? Kada ka riƙa tunani cewa Allah ya manta da kai. Ko da matsalolinka suna daɗa muni, Jehobah zai ƙarfafa ka kuma ya ba ka ƙarfin da zai sa ka jimre. (1 Korintiyawa 10:13) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa jim kaɗan, za a kawo ƙarshen dukan matsalolin da muke fama da su!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba