Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 1 pp. 14-15
  • Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • GWAMNATI MAI ADALCI
  • ƘOSHIN LAFIYA
  • CIKAKKIYAR SALAMA
  • DUNIYA ZA TA CIKA DA MUTANEN KIRKI
  • DUNIYA ZA TA ZAMA ALJANNA
  • Mene Ne Mulkin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na Karshe”?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Abin da Mulkin Allah Zai Yi
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 1 pp. 14-15
Mutane suna jin dadin rayuwa a aljanna

Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba

Ka taɓa tunanin yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba? Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimman abubuwan da za su faru da za su shafi dukan mutane.

Yesu ya bayyana yadda za mu gane cewa “Mulkin Allah ya yi kusa.” (Luka 21:31) Ya annabta cewa, wasu daga cikin abubuwan da za su faru su ne, za a yi yaƙe-yaƙe, da girgizar ƙasa, da matsananciyar yunwa, kuma cututtuka za su bazu. Abubuwan da muke gani a yau ke nan, ko ba haka ba?​—Luka 21:​10-17.

Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a “kwanakin ƙarshe,” halayen mutane za su daɗa muni. Za ka iya karanta yadda aka kwatanta hakan a 2 Timoti 3:​1-5. Idan ka yi la’akari da halayen mutane da kuma abubuwan da suke faruwa a yau, ba shakka za ka yarda cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ne yake cika.

Me hakan yake nufi? Lokaci ya kusa da Mulkin Allah zai gyara duniya. (Luka 21:36) A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya yi alkawari cewa zai gyara dukan abubuwan da suka lalace a duniya, kuma zai albarkaci bayinsa da suke duniya. Ga wasu daga cikin albarkun da za su samu.

GWAMNATI MAI ADALCI

“Aka kuwa ba shi [Yesu] sarauta, da ɗaukaka da mulki, domin dukan ƙabilu, da al’ummai, da yare dabam-dabam su [“yi masa hidima,” NW]. Sarautarsa ta har abada ce, mulki ne wanda ba zai ƙare ba. Mulkinsa ba za a taɓa halakar da shi ba.”​—DANIYEL 7:14.

Yadda za ka amfana: Za ka ji daɗin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Allah wadda za ta yi sarauta bisa dukan duniya. Kuma Yesu ne Sarkin.

ƘOSHIN LAFIYA

Wata karamar yarinya ta tashi daga keken gurgu da take zama tana takawa

“Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’”​—ISHAYA 33:24.

Yadda za ka amfana: Ba za ka ƙara yin rashin lafiya ko ka zama mai naƙasa ba kuma za ka rayu har abada.

CIKAKKIYAR SALAMA

An kakkarye bindiga

‘Zai tsai da yaƙe-yaƙe a dukan duniya.’​—ZABURA 46:9.

Yadda za ka amfana: Ba za ka ƙara jin tsoro cewa za a yi yaƙi ba, balle a ce mutane za su wahala saboda yaƙi.

DUNIYA ZA TA CIKA DA MUTANEN KIRKI

“Mugaye za su [“shuɗe,” NW ] . . . amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar.”​—ZABURA 37:​10, 11.

Yadda za ka amfana: Mugaye ba za su kasance a duniya a lokacin ba, mutanen da suke yi wa Allah biyayya ne kaɗai za su kasance.

DUNIYA ZA TA ZAMA ALJANNA

“Za su gina gidaje, su zauna a cikinsu, za su shuka gonakin inabi, su ci amfaninsu.”​—ISHAYA 65:​21, 22.

Yadda za ka amfana: Duniya gaba ɗaya za ta yi kyau sosai. Allah zai amsa addu’ar da muke yi cewa a yi nufinsa “a cikin duniya.”​—Matiyu 6:10.

Mutane suna jin dadin rayuwa a aljanna
    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba