Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/10 p. 3
  • Kana Jinkirin Cika Ta Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Jinkirin Cika Ta Kuwa?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Shiri don Jinyar Gaggawa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Kun San Zaɓin da Kuke da Shi?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Yi Shiri Yanzu Don Jinyar Gaggawa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Me Ya Sa Ba Ku Yarda da Karin Jini?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 1/10 p. 3

Kana Jinkirin Cika Ta Kuwa?

Jinkirin cika me? Cika katin DPA (takardar izinin kula da jinya) wanda ake ba wa Shaidu da suka yi baftisma. Tun da “ba ku san abin da za ya faru gobe ba,” yana da muhimmanci ka yanke shawara tun da wuri kuma ka rubuta irin jinyar da za ka so idan da jinyar gaggawa. (Yaƙ. 4:14; A. M. 15:28, 29) Don a taimake ka, an yi bidiyon nan Transfusion-Alternative Health Care—Meeting Patient Needs and Rights. Ka kalli bidiyon idan kana jin Turanci, tun da za ka iya samun bidiyon ne kawai a harshen Turanci, sai ka yi bitar abin da ka koya tare da addu’a ta wajen yin amfani da bayanan da aka yi a ƙasa.—Abin lura: Domin bidiyon yana ɗauke da wasu hotunan da ya nuna yadda ake yi wa mutane fiɗa, iyaye su yi amfani da sanin ya kamata sa’ad da suke kallon bidiyon tare da yaransu ƙanana.

(1) Wasu masu ba da magani suna sake bincika yin amfani da ƙarin jini domin yawancin majiyyata suna ƙin ƙarin jini. Waɗannan masu ba da maganin sun canja ra’ayinsu ne domin haɗarurrukan da ke tattare da ba da ƙarin jini da kuma tsadar jini. (2) Likitoci sun yi fiɗa masu wuya ba tare da ba da ƙarin jini ba. Misalai guda uku na fiɗa masu wuya da aka yi kamar yadda aka nuna a cikin bidiyon su ne: Fiɗar zuciyar yara, na hanta, da kuma na ƙashi. (3) Fiye da likitoci 100,000 a ƙasashe 150 a dukan duniya ne suka yarda cewa za su yi jinyar majiyyata ba tare da ƙarin jini ba. Me ya sa suke son yin haka? Domin girmama zaɓen waɗanda suke jinya.

(4) Nazarin kwanan bayan nan ya nuna yawan tabbaci na cewa ba a bukatar ƙarin jini. An tabbatar da cewa rashin ƙarin jini yana kyautata rayuwar masu jinya da suka rasa jini da yawa. (5) Wasu haɗarurrukan da ke cikin ƙarin jini sun haɗa da gurɓatarwar ƙwayoyin cuta, cutar da za ta iya kama wani, rage ƙarfin iya yaƙi na ƙwayoyin rai na cikin jiki, da kuma kuskuren da mutane suke yi. (6) Game da fa’idodin abubuwan taimako maimakon ƙarin jini, gwanaye da yawa sun ga cewa yana taimakawa wajen kula da majiyyata kuma yana rage tsadar jinya. Wani abu na musamman shi ne sanin cewa akwai magunguna marar lahani, masu amfani kuma marar tsada. (7) Raguwar adadin jajayen ƙwayoyin jini shi ne ke jawo cutar rashin isashen jini a jiki. Mutumin da ke da wannan cutar yana da ƙanƙanin jajayen ƙwayoyin rai idan aka haɗa da jininsa. Mutumi zai iya kasance da rai cikin yanayin nan kuwa? ’Yan Adam suna iya zama da rashin isasshen himoglobin fiye da yadda ake tsammani a dā. Don ya ƙaru a cikin jiki, ƙwararrun likitoci sun ce a yi amfani da abubuwan da za su ƙara jini a jiki. (8)  Ta yaya za a daɗa yawan jajayen ƙwayoyin jini a jikin majiyyaci? Ta wajen shan maganin jini. A wasu yanayi, maganin da ake kira erythropoietin (EPO) zai iya gyara yanayin jinin. A wasu ƙasashe EPO yana ɗauke da abubuwan da ake samu daga jini. Zaɓen Kirista ne ko zai amince da irin wannan jinyar bisa ga lamirinsa. (9) Ta waɗanne hanyoyi ne ake iya rage zubar da jini a lokacin fiɗa? Idan an mai da hankali sosai a fiɗa, idan an yi amfani da electrocautery (na’urar da ke rage zuban jini); maganin da ke rage zuban jini; da kuma intraoperative cell salvage (tsarin kiyaye ƙwayoyin rai). Mutum zai yi amfani da lamirinsa ne wajen amincewa da waɗannan abubuwan da kuma tsarin.

(10) Abubuwan taimako maimakon ƙarin jini suna taimaka wa yara ko kuwa mutanen da suke yanayi na gaggawa? E. An ba da misalin wani yaro, ɗan shekara huɗu da aka haife shi da ciwon zuciya, da aka yi masa fiɗa masu wuya dabam-dabam ba tare da ƙarin jini ba. A wani asibitin da ake yawan kai batun gaggawa a Amirka da suke wa Shaidun Jehobah da ba sa yarda da ƙarin jini ɗarurruwan manyan fiɗa kowacce shekara, an ce mutuwar mutane ta ragu a wajen. (11) Wata ƙa’ida ta musamman game da magani mai kyau shi ne daraja abin da majiyyaci ya ke so ne, cewa yana da iko ya yarda ko kuma ya ƙi da wani irin magani. A ƙarshe, yana da muhimmanci Kiristoci su zaɓi jinya marar jini tun da wuri.

Ka riga ka yanke shawara game da irin hanyar jinya da za ka amince a yi wa kai da yaranka kuma ka cika katin DPA kuwa? Don cikakken tattaunawa na wannan batun, ka yi bitar babi na 7 na littafin nan Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah da kuma wuraren bincike da aka ambata a ciki. Ka kuma duba ’yar cikin nan “How Do I View Blood Fractions and Medical Procedures Involving My Own Blood?” [Yaya Nake Ɗaukan Ɓangarorin Jini da Kuma Hanyoyin Jinya da Suka Shafi Jinina?] a cikin Hidimarmu Ta Mulki ta Disamba 2006 na Turanci. A ƙarshe, ka tabbata cewa ka cika dukan zaɓin da ka yi cikin katin DPA ɗinka. Waɗanda ka zaɓa su zama malaman kiwon lafiyarka da kuma wani a cikin iyalinka da ba Mashaidi ba ne da ka zaɓa ya kamata su san zaɓin da ka yi sosai.

[Hoton da ke shafi na 3]

• Ka riga ka yanke shawara game da irin hanyar jinya da kai da yaranka za ku so a yi muku kuwa?

• Shin kana ɗaukar katin DPA wanda ka riga ka cika kuwa saboda jinyar gaggawa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba