Kun San Zaɓin da Kuke da Shi?
Asibitoci masu yawa yanzu a dukan duniya suna fiɗa ba tare da ƙarin jini ba. Ka san dukan zaɓi da kake da su a yanzu a wajen neman magani kuwa? Kana bukatar ka sani domin ka yi zaɓi da ya dace wajen neman magani da kuma fiɗa. Ka kalli bidiyon nan No Blood—Medicine Meets the Challenge. “Tun da an yi bidiyon da Turanci kawai, ka kalla idan ka fahimci Turanci kuma ka yi amfani da bayanin da ke ƙasa don yin bitar abin da ka koya.” Abin lura: Domin bidiyon ya ƙunshi inda ake fiɗa, iyaye suna bukatar su mai da hankali sa’ad da suke kallon bidiyon tare da yaransu.
(1) Shaidun Jehobah suna ƙin ƙarin jini domin umurnin Littafi Mai Tsarki da ke Ayyukan Manzanni 15:28, 29. Wurin ya ce mu ‘guji jini.’ (2) Idan ya zo ga magani, Shaidun Jehobah suna son magani mafi kyau, amma ba tare da ƙarin jini ba. (3) Kowanne majiyyaci yana da ’yancin zaɓi, wato, ’yancin zaɓan abin da za a yi da jikinsa ko jikinta.
(4) Ya dace kuma daidai ne a zaɓa hanyoyin maganin da ba su ƙunshi ƙarin jini ba domin sun fi kyau sosai. Ana iya ɗaukan cututtuka kamar su ciwon huhu, ƙanjamau da sauransu idan aka yi ƙarin jini. Hakkin majiyyaci ne ya zaɓi irin maganin da yake so. (5) Sa’ad da jini mai yawa ya zuba, likitoci za su iya yin abubuwa biyu, wato, su hana jinin da ke zuba da kuma sa yawan jinin majiyyacin ya ƙaru cikin jikinsa.
(6) Mizanai huɗu na wasu hanyoyin magani ba tare da ƙarin jini ba su ne, a rage zuban jini, a adana jajayen ƙwayoyin jini, a sa jiki ya fito da jini, da kuma cike jinin da ya zuba.
(7) Likitoci su yi ƙoƙari su (a) rage zuban jini, (b) kāre jajayen ƙwayoyin jini, (c) su motsa jiki ya yi jini, da kuma (d) samo jini da aka yi hasararsa ta wajen yin abubuwa na gaba: (1) Hanyoyin fiɗa da suka haɗa da yin amfani da Electrocautery, argon-beam coagulator, da fibrin glue, (2) hemodilution; (3) erythropoietin (EPO); (4) cell salvage. (8) A lokacin fiɗa, ana karkata hanyar jinin daga jikin mutum zuwa cikin jaka, kuma a sake jinin da ruwan magani. A lokacin fiɗa ko kuma bayan fiɗa, ana mai da jinin zuwa jikin majiyyacin. Ana kiran wannan tsarin Hemodilution. (b) Ana samun jini a lokacin fiɗa daga ciwo ko kuma wani rami na jiki. Ana tsabtace shi ko kuma a tace shi, sai a mai da shi cikin jikin majiyyacin. Ana kiran wannan tsarin cell salvage. (9) Mu gaya wa kowanne likita da ke ba mu magani ya sanar da mu game da amfanin da kuma haɗari da ke tattare da duk wata hanyar magani da za a yi mana maimakon ƙarin jini.
(10) Za a iya yin fiɗa mai wuya mai tsanani ba tare da ƙarin jini ba. An nuna misalai biyu a cikin bidiyon da ya ƙunshi wata yarinya da aka yi mata fiɗa domin a gyara tanƙwasa a kashin bayanta da kuma ta tsohuwa da aka yi wa fiɗa domin a gyara jijiya a tumbinta. (11) Wani abu mai kyau yana faruwa a tsakanin likitoci, wato, likitoci masu kula suna amfani da hanyoyin magani na zamani wajen yi wa Shaidun Jehobah magani ba tare da ƙarin jini ba.
Karɓan wasu cikin hanyoyin magani da aka nuna a bidiyon abin da mutum zai zaɓa da kansa ne bisa ga lamirinsa da aka koyar da Littafi Mai Tsarki. Ka riga ka zaɓi irin hanyar magani da kai da ’ya’yanka za ku so ku karɓa, kuma ka cika katin DPA? Domin cikakken bayani a kan wannan batun, ka mai da hankali a kan “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2004, da kuma 15 ga Oktoba, 2000. Sai kuma ka yi amfani da abin da ke ’yar ciki na Hidimarmu Ta Mulki ta Turanci na Disamba 2006, “How Do I View Blood Fractions and Medical Procedures Involving My Own Blood?,” [“Yaya Nake Ɗaukan Kashin Jini da kuma Yadda Za a Yi Amfani Da Jinina?”] domin ka yanke shawara game da irin hanyar magani da za ka karɓa ko ba za ka karɓa ba. A ƙarshe, ka tabbata cewa ka rubuta zaɓin da ka yi cikin katin DPA naka. Ya kamata ka sanar da mutumin da ka zaɓa da kuma wani danginka da ba Mashaidin Jehobah ba ne game da shawarar da ka tsai da.