Gabatarwa
Don Soma Nazarorin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Yuni
“Sau da yawa mukan ji mugun labarai. Kana tsammani cewa za mu iya jin labari mai daɗi a yau kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wannan kalami mai ban ƙarfafa.” Ka karanta kuma ka tattauna bayanin da ke tambaya ta biyu a shafi na 14 na Hasumiyar Tsaro ta Afrilu-Yuni kuma ka karanta nassin. Ka ba da mujallar, kuma ka shirya ka koma ziyara don ka amsa tambaya da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Afrilu-Yuni
“Yayin da yaro yake girma, yana fuskantar abubuwa da yawa da zai bukaci ya tsai da shawara a kai. Mene ne kake tsammani cewa iyaye za su iya yi don su taimaki yara su tsai da shawarwari masu kyau? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Misalai 22:6.] Yana da muhimmanci a riƙa tattaunawa da yara tun suna ƙanana. Talifin nan da ya soma daga shafi na 18 ya tattauna yadda iyaye za su iya taimaki matasa su yanki shawarwari masu kyau.”
Awake! Yuni
“Ta’addanci ya zama matsala a dukan duniya. Kana ganin mene ne yake jawo hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Waɗannan kalamai daga Littafi Mai Tsarki sun ba mu bege. [Karanta Zabura 72:7, 14.] Wannan mujallar ta bayyana wasu dalilai da suka sa ake ta’addanci da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ta’addanci da kuma sa’ad da ta’addanci ba zai kasance kuma ba.”