Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Afrilu
“Tarzoma da gurguncewar tattalin arziki, har ma da mummunar ɗabi’a suna ci gaba da ƙaruwa a dukan duniya. Kana ganin cewa hakan cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ne kuwa? [Ka bari ya amsa.] Dubi abinda mujallar nan ta ce.” Ka ba mutumin Hasumiyar Tsaron Afrilu-Yuni, kuma ku tattauna ƙaramin jigo na uku da ke shafi na 23 tare. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Afrilu-Yuni
“Zan so in karanta maka wannan nassin. [Ka karanta Ishaya 65:17.] Mene ne sababbin sammai da sabuwar duniya da aka ambata a nan? Waɗanne abubuwa ne ba za a sake tunawa da su ba? Za ka sami amsoshin tambayoyin nan a shafi na 29 a cikin wannan mujallar.”
Awake! Yuni
“Kowace shekara, miliyoyin mutane a duniya suna rashin lafiya domin cin abincin da bai da kyau da jiki. A ganinka, abincin da muke ci yana da kyau kuwa? [Ka bari ya amsa.] Wannan mujallar ta bayyana hanyoyi huɗu da za mu iya kāre iyalinmu daga cutar da ake samu a cikin abinci. Ta kuma tattauna alkawarin da Allah ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki cewa ba da daɗewa ba kowa zai more abinci mai kyau mai yawa.” Karanta Zabura 104:14, 15.