An Shirya Mujallunmu don Mutane Da Yawa Su Yi Marmarin Karanta Su
1. Ta yaya rukunin bawan nan mai aminci, mai hikima yake yin koyi da manzo Bulus?
1 Kamar yadda manzo Bulus ya daidaita yadda yake gabatar da bishara don ya rinjayi ko waɗanne irin “mutane,” rukunin bawan nan mai aminci, mai hikima yana amfani da mujallunmu don ya rinjayi mutane daga wurare da kuma imani dabam-dabam. (1 Kor. 9:22, 23) Domin mu yi amfani da Hasumiyar Tsaro da Awake! da kyau, ya kamata mu fahimci da kuma tuna waɗanda aka shirya wa waɗannan mujallun.
2. An shirya Awake! don ya jawo hankali waɗanne irin mutane?
2 Awake!: An shirya wannan mujallar don ta rinjayi irin mutanen da manzo Bulus ya yi wa magana sa’ad da yake tattaunawa da “mutanen Atina.” (A. M. 17:22) Waɗannan mutanen ba Kiristoci ba ne, kuma ba su san Nassosi ba. Haka nan ma, mutanen da aka shirya wa Awake! ba su san Littafi Mai Tsarki ba. Wataƙila ba su san koyarwar Kirista ba, kuma ba su amince da addini ba ko kuma ba su sani ba cewa Littafi Mai Tsarki yana da amfani ba. Ainihin abin da ya sa aka shirya mujallar Awake! shi ne don a tabbatar wa masu karanta ta cewa Allah na gaskiya na wanzuwa. An kuma wallafa wannan mujallar don a sa mutane su ba da gaskiya ga Littafi Mai Tsarki kuma a taimaka wa masu karatunta su fahimci cewa Shaidun Jehobah sun yi dabam da sauran rukunin addinai.
3. Su wane ne ake rubuta wa talifin Hasumiyar Tsaro na wa’azi da na nazari?
3 Hasumiyar Tsaro: Waɗanda aka shirya wa Hasumiyar Tsaro na wa’azi suna ɗan daraja Allah da kuma Nassosi. Sun ɗan san game da Littafi Mai Tsarki amma ba su fahimci koyarwarsa sosai ba. Suna kama da mutanen da Bulus ya kira “masu-tsoron Allah.” (A. M. 13:14-16) An rubuta talifin Hasumiyar Tsaro na nazari musamman don Shaidun Jehobah. Bulus ya yi tsammani cewa waɗanda suke karanta wasiƙunsa sun san Nassosi kuma suna da cikakken sani na gaskiya. (1 Kor. 1:1, 2) Haka nan ma, an rubuta talifofin Hasumiyar Tsaro na nazari don waɗanda suke halartan tarurrukanmu kuma sun san kalamai da ra’ayoyi na Shaidu.
4. Me ya sa ya kamata mu san kowane fitowar mujallu da muke amfani da su a hidimar fage?
4 Ko da yake muna ba da mujallun bibbiyu, muna gabatar da ɗaya kawai a cikinsu. Saboda haka, ka sa sanin kowanne cikin fitowar ya zama maƙasudinka. Da hakan za ka ƙware sosai wajen gabatar da talifin da mutanen da ka haɗu da su za su yi marmarin karantawa.