Bidiyon nan Jehovah’s Witnesses—Organized to Share the Good News
Shaidun Jehobah suna wa’azin bishara, fiye da shekara 100. An kira wannan aikin wa’azi mafi girma da aka taɓa yi a dukan duniya, kuma muna yin amfani da harsuna ɗarurruwa a ƙasashe fiye da 230. (Mat. 24:14) Me ya sa wannan aikin yake da muhimmanci? Ta yaya ake cim ma wannan aikin a dukan duniya? Bidiyon nan Jehovah’s Witnesses—Organized to Share the Good News ya amsa waɗannan tambayoyin da suka bayyana aikinmu na dukan duniya dalla-dalla. Bayan kun kalli wannan bidiyon, ku yi la’akari da waɗannan tambayoyi na gaba.
Ta yaya bidiyon ya kyautata godiyarka ga (1) ƙoƙarin da ƙungiyar Jehobah take yi don yaɗa bishara? (2 Tim. 4:2) (2) iyalin Bethel a dukan duniya? (3) koyarwa da ake wa masu wa’azi a ƙasashen waje da masu kula? (2 Tim. 2:2) (4) amfanin tattauna nassosin yini kullum da safe da shirya tarurruka na ikilisiya duk mako? (A. M. 17:11) (5) amfanin halartar tarurrukan Kirista? (Ibran. 10:24, 25) (6) albarkar da za ka samu a nan gaba sa’ad da dukan duniya ta zama Aljanna? (Isha. 11:9) (7) gatar da kake da shi na saka hannu a wannan aikin girbi da ake yi?—Yoh. 4:35.
Wannan bidiyon ya zama kayan aiki mai kyau na sa masu zukatan kirki su san aikin da Shaidun Jehobah suke yi a dukan duniya. (8) A wane lokaci ne zai fi dacewa mu nuna wa ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki da danginmu da kuma wasu wannan bidiyon? (9) Yaya mutane suka ji sa’ad da ka nuna musu wannan bidiyon?
Yayin da muke tunani a kan abin da Jehobah yake cim ma wa, mun motsa mu furta waɗannan kalamai na marubucin wannan zaburar: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.” (Zab. 40:5) Bari mu yi amfani da wannan bidiyon yadda ya dace don taimaka wa mutane su nuna godiya ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa!