Tafiya A Hanya Da Ke Ƙara Haskaka
Jehobah shi ne Tushen gaskiyar da muke koya. (Zab. 43:3) Ko da yake duniya tana cikin duhu sosai, Allah na gaskiya yana ci gaba da ba mutanensa haske. Mene ne sakamakon hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” (Mis. 4:18) Ƙarin haske daga wurin Jehobah yana ci gaba da haskaka tafarkin mutanensa. Yana gyara koyarwarsu da ɗabi’arsu kuma yana yi musu gyara a matsayin ƙungiya. Bari mu tattauna yadda hakan ya faru a tarihin masu bauta wa Jehobah a yau.
Babu shakka, duniya da ke kewaye da mu tana cikin duhu sosai. Yayin da Jehobah yake ci gaba da haskaka mutanensa, bambancin da ke tsakanin su da mutanen duniya yana ƙara faɗi. Mene ne wannan hasken yake yi mana? Kamar yadda haske a saman ramin da ke hanya mai duhu ba zai kawar da ramin ba, hakazalika haske daga Kalmar Allah ba zai kawar da haɗarurruka ba. Amma haske daga wurin Allah yana taimaka mana mu guji haɗarurrukan nan don mu ci gaba da yin tafiya a tafarkin hasken da ke ƙaruwa. Saboda haka, bari mu ci gaba da mai da hankali ga kalmar Jehobah, wadda take “kama da fitilla mai-haskakawa cikin wuri mai-duhu.”—2 Bit. 1:19.