Haske Daga Allah Na Korar Duhu!
A cikin Littafi Mai Tsarki, an kamanta haske da gaskiya, shi kuwa duhu, an kamanta shi da ƙarya. (Zab. 43:3; Isha. 5:20) Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Allah haske ne, a wurinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.” (1 Yoh. 1:5) Ka ga bambancin da ke tsakanin haske da duhu. Jehobah ne tushen hasken gaskiya, kuma ba ruwan shi da duhun da ke kai ga halaka. To, wane ne tushen duhu? Tattaunawarmu da yamman nan za ta taimaka mana mu gano tushen duhun da ke jawo halaka da kuma yadda za mu guje shi. Za mu kuma tattauna yadda za mu nuna godiya domin hasken da muke morewa daga Allah.
Muna bukatar mu yaba wa Jehobah, wanda ya ba mu hasken gaskiyarsa. Kamar Sarki Dauda, mun ce: “Kai ne fitillata, ya Ubangiji, Ubangiji kuma za ya haskaka duhuna.” (2 Sam. 22:29) Duk da haka, ba ma sakaci, domin hakan yana iya sa mu komawa duhun da aka ceto mu daga ciki. A cikin duniyar nan da ke cike da rashin tsoron Jehobah, bari mu zama masu yaɗa haske da gaba gaɗi da kuma himma. Bari mu “yi tafiya kamar ’ya’yan haske.”—Afis. 5:8.