Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/11 p. 1
  • Ka Taimaki Mai Gidan Ya Yi Tunani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaki Mai Gidan Ya Yi Tunani
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Bi da Masu Ba da Hujja don Kada Su Saurare Mu
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Ba da Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 10/11 p. 1

Ka Taimaki Mai Gidan Ya Yi Tunani

1. Wace mahawwara a hidima ce ta fi kyau?

1 Wace mahawwara a hidima ce ta fi kyau, nacewa da abin da muka sani ko kuma taimaka wa mai gidan ya yi tunani kuma ya yi kammalawar da ta dace? Manzo Bulus ya sa Yahudawa da ke Tasalonika su yi tunani sa’ad da yake tattaunawa da su kuma “waɗansu a cikinsu suka rinjayu.” (A. M. 17:2-4) Mene ne sa mutane su yi tunani ya ƙunsa?

2. Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Bulus sa’ad da muke wa’azin bishara?

2 Ka Yi La’akari da Yadda Mutane Suke Ji da Kuma Al’adarsu: Don ka taimaka wa mutane da suke yankinku su yi tunani, dole ne ka yi la’akari da yadda suke ji. Bulus ya soma tattaunawa da Helenawa da ba masu bi ba ne a Tudun Arasa ta wajen ambata abubuwa da suka sani da kuma amince da su. (A. M. 17:22-31) Saboda haka, sa’ad da kake shirya gabatarwa da za ka yi, ka yi la’akari da abin da mutane a yankinku suka yi imani da shi da kuma ra’ayinsu. (1 Kor. 9:19-22) Idan mai gidan bai yarda da abin da ka faɗa ba, ka yi ƙoƙari ka nemi abin da ku biyu kuka yi imani da shi, kuma ka soma tattauna a kan wannan.

3. Ta yaya yin amfani da tambayoyi a hanyar da ta dace za ta taimaka mana mu tattauna da mutane?

3 Ka Ya Amfani da Tambayoyi da Kyau: Ba za mu iya nuna wa matafiyi hanya ba sai dai mun san inda zai je. Haka nan ma, ba za mu iya taimakon mai gida ba ya kai ga kammalawa da ta dace sai dai mun san ra’ayinsa. Kafin Yesu ya tattauna da mai sauraro, sau da yawa yakan yi tambayoyi don ya san ra’ayin mutumin. Alal misali, sa’ad da wani ya tambayi Yesu, “Me zan yi domin in gāji rai na har abada?,” Yesu ya nemi ya san ra’ayin mutumin kafin ya ba da amsa. (Luk 10:25-28) A wani lokaci sa’ad da Bitrus ya ba da amsar da ba daidai ba, Yesu ya yi amfani da tambayoyi don ya daidaita tunaninsa. (Mat. 17:24-26) Saboda haka, idan mai gida ya yi tambaya ko kuma ya furta ra’ayin da ba daidai ba, muna iya yin amfani da tambayoyi don mu taimaka masa ya yi tunani a kan batutuwa.

4. Me ya sa za mu yi ƙoƙari mu taimaka wa mai gida ya yi tunani?

4 Idan muka taimaka wa mai gida ya yi tunani, muna yin koyi da Yesu, Babban Malami, da kuma waɗanda suka ƙware a wa’azin bishara a ƙarni na farko. Muna daraja mai gidan da kuma nuna masa ladabi. (1 Bit. 3:15) Saboda haka, zai fi kasancewa a shirye ya ƙyale mu mu dawo.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba