Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 5/15 pp. 11-15
  • Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • WANE NE NAKE YI WA WA’AZI?
  • A INA NAKE YI WA MUTANE WA’AZI?
  • WANE LOKACI NE YA FI DACEWA IN YI WA MUTANE WA’AZI?
  • TA YAYA YA KAMATA IN YI WA MUTANE WA’AZI?
  • KA RIƘA BI DA MUTANE A HIDIMARKA YADDA KAKE SO SU BI DA KAI
  • Yaya Yesu Ya Ce Mu Rika Bi da Mutane?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Taimaki Mai Gidan Ya Yi Tunani
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Kada Ka Gaji da Yin Wa’azi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 5/15 pp. 11-15

Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai

“Dukan abu . . . da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.”—MAT. 7:12.

MECE CE AMSARKA?

  • Yaya ya kamata mu bi da kowane mutum da muke yi masa wa’azi?

  • Mene ne muka koya daga Matta 7:12 game da inda za mu yi wa’azi da lokacin da za mu yi hakan da kuma yadda za mu soma tattaunawa da mutane?

  • Wace shawara ce da aka tattauna a wannan talifin ka shirya za ka bi?

1. Yadda muke bi da mutane sa’ad da muke wa’azi yana da muhimmanci kuwa? Ka ba da misali. (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)

’YAN shekarun da suka shige a wani kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu, wasu Kiristoci ma’aurata suna wa’azi wa wata mata kusa da gidanta sai aka soma ruwan sama. Sai ɗan’uwan ya ba wa matar laimarsa don ta rufe kanta da shi kuma shi da matarsa suka yi amfani da ɗayan laimar. Hakan ya burge matar har ya sa ta halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu. Matar ta ce ta manta da abin da ma’auratan suka faɗa mata, amma ba ta manta da alherin da suka yi mata ba. Me ya sa aka sami wannan sakamako mai kyau? Don waɗannan ma’auratan sun bi wani sanannen umurni game da yadda za mu bi da mutane.

2. Wane umurni ne Yesu ya bayar game da yadda za mu bi da mutane, kuma ta yaya za mu bi wannan umurnin?

2 Wane umurni ke nan? Wannan shi ne umurnin da Yesu ya bayar sa’ad da ya ce: “Dukan abu . . . da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” (Mat. 7:12) Ta yaya za mu bi wannan umurnin? Da farko, ka tambayi kanka, ‘Da a ce ni ne mutumin, yaya zan so ya bi da ni?’ Na biyu, ka yi iya ƙoƙarinka ka bi da mutumin yadda za ka so ya bi da kai.—1 Kor. 10:24.

3, 4. (a) Ka bayyana dalilin da ya sa bin wannan umurnin Yesu ya shafi yadda muke bi da kowa. (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Shin Yesu ya ce mu bi wannan umurnin sa’ad da muke sha’ani da ’yan’uwanmu masu bi ne kawai? A’a. Yesu ya yi magana ne game da yadda za mu bi da kowa, har da magabtanmu. (Karanta Luka 6:27, 28, 31, 35.) Hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci mu bi umurnin sa’ad da muke wa’azi, don mutane da yawa da muke yi musu wa’azi za su ba da gaskiya kuma su sami “rai na har abada.”—A. M. 13:48.

4 Yanzu, za mu tattauna tambayoyi huɗu da ya kamata mu yi la’akari da su sa’ad da muke wa’azi: Wane ne nake yi wa wa’azi? A ina ne nake yi wa mutane wa’azi? Wane lokaci ne ya fi dacewa in yi wa mutane wa’azi? Ta yaya ya kamata in yi wa mutane wa’azi? Idan muka yi hakan, za mu fahimci yadda mutane za su so mu bi da su da kuma hanyar da ta fi dacewa mu yi wa’azi ga kowane mutum.—1 Kor. 9:19-23.

WANE NE NAKE YI WA WA’AZI?

5. Waɗanne irin tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu?

5 Yanayi da matsalolin kowane mutum da muke haɗuwa da shi sa’ad da muke wa’azi sun bambanta. (2 Laba. 6:29) Sa’ad da kake so ka yi wa wani wa’azi, ka tambayi kanka: ‘Idan ni ne wannan mutum, yaya zan so a bi da ni? Shin zan ji daɗi idan ya ɗauke ni kamar mutum marar amfani ne kawai da ke zama a unguwar? Ko kuma zan so ya san ni da halayena masu kyau?’ Yin tunani a kan waɗannan tambayoyin zai taimaka mana mu ɗauki mutumin da muhimmanci.

6, 7. Mene ne ya kamata mu yi idan wani ya yi fushi da mu sa’ad da muke masa wa’azi?

6 Ba wanda zai so a ɗauke shi kamar mutum “mai rashin hankali.” Alal misali, a matsayin Kiristoci, muna iya ƙoƙarinmu don mu bi umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce: ‘Bari zancenmu kullum ya kasance tare da alheri.’ (Kol. 4:6) Amma da yake mu ajizai ne, wani lokaci mukan yi wa wani magana kuma mu yi da-na-sani daga baya. (Yaƙ. 3:2) Idan hakan ya faru wataƙila domin muna baƙin ciki a ranar, ba za mu so ya ɗauka cewa mu “marasa hankali” ne ko marasa “sanin ya kamata,” a maimakon haka, za mu so mutumin ya fahimci yanayinmu. Sanin hakan zai sa mu fahimci cewa wani lokaci, mutane sukan yi mana baƙar magana ba da son su ba.

7 Idan kana wa’azi kuma wani ya nuna maka rashin hankali ko ya fusata, zai dace ka yi ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa yake fushi. Shin wata matsala a wajen aiki ko a makaranta ce ta sa yake fushi? Yana wani rashin lafiya mai tsanani ne? A yawancin lokaci, mutanen da suka yi fushi da farko sun saurari wa’azi sa’ad da Shaidun Jehobah suka bi da su cikin haƙuri da ladabi.—Mis. 15:1; 1 Bit. 3:15.

8. Me ya sa ya dace mu yi wa’azi ga “kowaɗanne irin mutane”?

8 Muna wa’azi ga mutane dabam-dabam. A cikin ’yan shekarun da suka shige, an wallafa labarai sama da 60 a cikin Hasumiyar Tsaro a ƙarƙashin jerin talifin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane.” Mutanen da aka ba da labarinsu sun haɗa da ɓarayi da masu shaye-shaye da ’yan ƙungiyar asiri ne da kuma masu shan ƙwaya a dā. Wasu labaran game da ’yan siyasa da shugabannin addinai da kuma waɗanda suka mai da dukan hankalinsu ga biɗan sana’arsu ne. Har ila, wasu waɗanda suka yi rayuwar lalata ne. Amma dukansu sun bar waɗannan abubuwan da suke yi sa’ad da aka yi musu wa’azin bishara kuma suka amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, suka yi canje-canje a rayuwarsu kuma suka zama Shaidun Jehobah. Saboda haka, bai kamata mu yi tunani cewa wasu mutane ba za su iya amincewa da saƙon Mulkin ba. (Karanta 1 Korintiyawa 6:9-11.) A maimakon haka, zai dace mu fahimci cewa “kowaɗanne irin mutane” za su iya zama masu bauta wa Jehobah.—1 Kor. 9:22, Littafi Mai Tsarki.

A INA NAKE YI WA MUTANE WA’AZI?

9. Me ya sa ya kamata mu daraja gidajen mutane?

9 A ina ne muke samun mutane don mu yi musu wa’azi? A yawancin lokaci, muna samun su a gidajensu. (Mat. 10:11-13) Mukan ji daɗi sa’ad da mutane suka daraja gidanmu don yana da muhimmanci a gare mu. Muna samun rufin asirin da kuma kwanciyar hankali a gidanmu. Idan haka ne, ya kamata mu daraja gidajen maƙwabtanmu kamar yadda za mu so su daraja namu. Sa’ad da muke wa’azi gida-gida, ya kamata mu yi tunanin yadda za mu daraja gidajensu.—A. M. 5:42.

10. Ta yaya za mu guji ɓata ran mutane sa’ad da muke wa’azi?

10 Muna rayuwa a zamanin da ake yawan yin mugunta kuma saboda haka, mutane suna tsoron baƙi. (2 Tim. 3:1-5) Bai kamata mu yi wani abin da zai sa mutane su ji tsoronmu ba. Alal misali, a ce mun ƙwanƙwasa kofar gida kuma wani bai zo ya amsa mana ba, za mu iya ce bari mu leƙa cikin gidan ko maigidan yana nan. Amma a yankinku yin hakan zai ɓata ran maigidan ne? Shin mene ne maƙwabtansa za su yi tunaninsa? Gaskiya ne cewa muna so mu yi wa mutane da yawa wa’azi. (A. M. 10:42) Muna ɗokin faɗa wa mutane albishir don muna so mu taimaka musu su san Allah. (Rom. 1:14, 15) Duk da haka, zai dace mu guji yin wani abin da zai ɓata ran mutane a yankinmu. Manzo Bulus ya ce: “Kada mu bada dalilin tuntuɓe cikin komi, domin kada a yi zargin hidimarmu.” (2 Kor. 6:3) Sa’ad da muka daraja gidaje da kuma kayan waɗanda suke yankinmu, halinmu zai sa wasu su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki.—Karanta 1 Bitrus 2:12.

WANE LOKACI NE YA FI DACEWA IN YI WA MUTANE WA’AZI?

11. Me ya sa muke jin daɗi idan mutane ba su ɓata mana lokaci ba?

11 Dukanmu muna da hidimomi da yawa da muke yi kullum kuma saboda haka, muna kasafin lokacinmu da kyau don mu cim ma burinmu. (Afis. 5:16; Filib. 1:10) Idan wani abu ya katse mana harka, ba ma jin daɗi. Saboda haka, muna son mutane su san da haka kuma kada su ci lokacinmu sosai sa’ad da suka katse mana aiki. Ta yaya bin wannan sanannen umurnin Yesu zai taimaka mana wajen yin la’akari da lokaci sa’ad da muke yi wa mutane wa’azi?

12. Ta yaya za mu san lokacin da ya fi dacewa don yi wa mutane wa’azi a yankinmu?

12 Ya kamata mu yi tunanin lokacin da ya fi dacewa mu ziyarci mutane. A wane lokaci ne ake samun mutane a gida a yankinmu? A wane lokaci ne za su so su saurare mu? Idan muka san hakan, zai dace mu daidaita harkokinmu don mu fita wa’azi a irin waɗannan lokatan. A wasu wurare, wa’azi gida-gida ya fi dacewa da rana zuwa yamma. Idan haka yake a yankinku, shin za ku iya yin shiri don ku yi wa’azi gida-gida a waɗannan lokatan? (Karanta 1 Korintiyawa 10:24.) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu don sadaukarwar da muka yi don mu yi wa mutane da ke yankinmu wa’azi a lokutan da suka fi dacewa.

13. Ta yaya za mu girmama waɗanda muke wa wa’azi?

13 Mene ne kuma za mu yi don mu girmama mutane? Idan wani ya saurare mu, ya kamata mu yi masa wa’azi da kyau amma kada mu cinye masa lokaci. Wataƙila mutumin ya shirya cewa zai yi wani abu da ke da muhimmanci a gare shi. Idan ya ce yana da ayyuka a gabansa, za mu iya ce ba za mu daɗe ba, kuma mu cika alkawarinmu. (Mat. 5:37) Sa’ad da muke kammala tattaunawar, za mu iya tambayarsa lokacin da zai fi dacewa mu sake ziyararsa. Wasu masu shela sukan ce: “Zan so in sake ziyararka. Za ka so in yi maka waya ko in aika maka saƙo kafin in zo?” Idan muka daidaita lokacinmu don ya jitu da na mutanen da suke yankinmu, muna bin misalin Bulus, wanda ya ce: “Ba biɗa wa kaina amfani na ke yi ba, amma abin da zai amfana masu-yawa, su tsira.”—1 Kor. 10:33.

TA YAYA YA KAMATA IN YI WA MUTANE WA’AZI?

14-16. (a) Me ya sa ya kamata mu bayyana wa maigida dalilin zuwanmu? Ka ba da misali. (b) Ta yaya wani mai kula mai ziyara yake soma tattaunawa da mutane?

14 A ce an kira ka a waya amma ba ka gane muryar wanda ya kira ba. Ba ka san mutumin ba, amma ya tambaye ka game da irin abincin da kake so. Babu shakka, za ka so ka san ko wane ne wannan mutum kuma dalilin da ya sa ya kira ka. Wataƙila cikin ladabi za ka tattauna da shi na ɗan lokaci, amma za ka so ka katse maganar, ko ba haka ba? Amma idan ya ce yana aiki a sashen ilimin tsara abinci masu gina jiki kuma yana so ya ba da wata shawara da za ta amfane ka. Mai yiwuwa za ka saurare shi don muna son mutane su nuna mana ladabi kuma su bayyana kansu sa’ad da suke yi mana magana. Ta yaya za mu nuna irin wannan ladabin sa’ad da muke yin wa’azi?

15 A yankuna da yawa, ya kamata mu bayyana wa mutane dalla-dalla dalilin da ya sa mun ziyarce su. Gaskiya ne cewa muna da saƙo mai muhimmanci da zai amfani mutumin. Amma a ce ba mu bayyana dalilin zuwanmu ba sai muka soma wa’azinmu da wannan tambayar: “Idan za ka iya magance kowace matsala a duniya, wanne ne za ka magance?” Mun yi tambayar ne don mu san abin da ke zuciyar mutumin kuma mu nuna masa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Amma mutumin zai iya soma tunani: ‘Wai wane ne wannan mutumin kuma me ya sa yake yi min irin wannan tambayar? Me ya kawo haka?’ Saboda haka, ya kamata mu bi da mutumin a yadda hankalinsa zai kwanta. (Filib. 2:3, 4) Ta yaya za mu yi hakan?

16 Ga abin da wani mai kula mai ziyara ya saba yi: Bayan ya gai da mai gidan, sai ya ba shi warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? kuma ya ce: “Muna rarraba wannan wa dukan mutane da ke unguwarku a yau. Yana ɗauke da tambayoyi guda shida da mutane da yawa suke yi. Ga naka kofin.” Ɗan’uwan ya ce hakan yana sa mutane su ɗan sake jikinsu da zarar sun san dalilin zuwanmu. A wannan lokacin, tattaunawa da su zai zama da sauki. Bayan haka, mai kula mai ziyarar sai ya tambayi mai gidan: “Ka taɓa yin tunani a kan ɗaya daga cikin waɗannan tambayoyin?” Idan maigidan ya zaɓi tambaya ɗaya, sai ɗan’uwan ya buɗe warƙar kuma ya tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tambayar. Amma idan bai zaɓa ba, sai ɗan’uwa ya ci gaba da tattaunawar don kada maigidan ya takura. Hakika, za mu iya soma tattaunawa da mutane a hanyoyi dabam-dabam. A wasu wurare mutane za su so mu yi musu gaisuwa bisa ga al’adarsu kafin mu gaya musu dalilin da ya kawo mu.

KA RIƘA BI DA MUTANE A HIDIMARKA YADDA KAKE SO SU BI DA KAI

17. Waɗanne hanyoyi ne za mu bi sanannen umurnin Yesu game da sha’ani da mutane sa’ad da muke wa’azi?

17 A taƙaice, ta yaya za mu bi sanannen umurnin Yesu game da sha’ani da mutane? Mu ɗauki mutumin da muhimmanci. Mu daraja gidan da kuma wasu mallakar mutumin. Mu yi ƙoƙarin fita wa’azi a lokatan da mutane za su kasance a gida kuma za so su saurare mu. Mu soma tattaunawarmu a yadda mutanen yankinmu za su ji daɗin saurarar mu.

18. Ta yaya za mu amfana idan muka bi da mutanen da ke yankinmu kamar yadda za mu so su bi da mu?

18 Za mu amfana a hanyoyi dabam-dabam idan muka bi da mutanen da ke yankinmu yadda za mu so su bi da mu. Ta wajen yin haka, muna nuna cewa bin umurnin Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci. Ƙari ga haka, muna ɗaukaka Ubanmu da ke sama. (Mat. 5:16) Hakan zai iya sa mutane da yawa su saurari bishara game da Mulki. (2 Tim. 4:5) Ko da mutanen da muke yi musu wa’azi sun amince da saƙon Mulkin ko a’a, za mu kasance da gamsuwa don mun san cewa muna iya ƙoƙarinmu a cika hidimarmu. (2 Tim. 4:5) Bari dukanmu mu bi misalin manzo Bulus da ya ce: “Ina kuwa yin abu duka sabili da bishara, domin in yi tarayya cikin samunta.” (1 Kor. 9:23) Saboda haka, bari mu ci gaba da bi da mutane a hidimarmu kamar yadda za mu so su bi da mu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba