Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/15 pp. 8-12
  • Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kasancewa da Ƙarfin Hali
  • Soma Tattaunawa Daga Littafi Mai Tsarki
  • Muhimmancin Saurarawa
  • Ka Kasance da Halin da ya Dace
  • Ka “Faɗi Maganar Allah Da Ƙarfin Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Yin Wa’azi Da Ƙarfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Me Ya Sa Hidimar Gida Gida Take Da Muhimmanci Yanzu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Kada Ka Gaji da Yin Wa’azi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/15 pp. 8-12

Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida

“Muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin husuma mai-yawa.”—1 TAS. 2:2.

1. Waɗanne ƙalubale ne Irmiya ya fuskanta, kuma yaya ya iya fuskantarsu?

IRMIYA mutum ne da yake ji yadda muke ji. Sa’ad da Jehobah ya gaya masa zai zama “annabi ga al’ummai,” sai ya ce: “Ai, Ubangiji Yahweh! ga shi, ni ba ni iya magana: gama ni yaro ne.” Duk da haka, ya dogara ga Jehobah, kuma ya karɓi aikin. (Irm. 1:4-10) Fiye da shekaru 40, Irmiya ya jimre da wariya, ƙi, ba’a, da kuma mugunta na zahiri. (Irm. 20:1, 2) Wani lokaci yana jin kamar ya daina aikin. Duk da haka, ya jimre wajen sanar da saƙon ga mutane da ba sa so su ji. Da ƙarfin da Allah ya ba shi, Irmiya ya cim ma abin da ba zai taɓa iya yi ba da kansa.—Ka karanta Irmiya 20:7-9.

2, 3. Ta yaya bayin Allah a yau suke fuskantar ƙalubale irin na Irmiya?

2 Bayin Allah da yawa a yau sun fuskanci abin da Irmiya ya fuskanta. Sa’ad da muke tunanin soma wa’azi na gida gida, wasu cikinmu sun yi tunani, ‘Ba zan iya yin wannan abu ba.’ Duk da haka, sa’ad da muka fahimci cewa nufin Jehobah ne mu yi shelar bishara sai muka daina tsoro kuma muka soma wa’azi. Duk da haka, yawancinmu muna fuskantar yanayi a rayuwarmu da yake sa ya kasance da wuya mu ci gaba da wa’azi, wataƙila na ɗan lokaci. Babu shakka, yana da wuya a soma wa’azi na gida gida kuma a ci gaba da wa’azi har zuwa ƙarshe.—Mat. 24:13.

3 Idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma kana halartar taron ikilisiya amma kana jinkirin soma wa’azi na gida gida kuma fa? Idan kai Mashaidi ne da ka yi baftisma kuma yana maka wuya ka fita hidimar kofa kofa, ko da yake kana da koshin lafiya kuma fa? Ka kasance da tabbaci cewa mutane daga al’adu dabam dabam suna magance ƙalubalen hidima na gida gida. Da taimakon Jehobah za ka iya.

Kasancewa da Ƙarfin Hali

4. Menene ya taimaki manzo Bulus ya yi bishara da ƙarfin hali?

4 Babu shakka ka fahimci cewa da ruhun Allah ne ake yin aikin wa’azi na dukan duniya ba da iko ko kuma hikimar ’yan adam ba. (Zech. 4:6) Haka yake da hidimar kowane Kirista. (2 Kor. 4:7) Ka yi la’akari da misalin manzo Bulus. Sa’ad da ya tuna lokacin da ’yan hamayya suka wulakanta shi da abokan tafiyarsa, ya rubuta: “Da muka rigaya muka sha wuya, har da wulakanci, . . . cikin Filibbi, muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin husuma mai-yawa.” (1 Tas. 2:2; A. M. 16:22-24) Ba za mu taɓa tunani cewa mai wa’azi da himma kamar Bulus yana da lokacin da yake fama ya yi wa’azi. Duk da haka, kamar dukanmu, Bulus ya dogara ga Jehobah don ya yi wa’azin bishara da ƙarfin hali. (Ka Karanta Afisawa 6:18-20.) Ta yaya za mu yi koyi da misalin Bulus?

5. A wace hanya ce za mu kasance da ƙarfin hali mu yi wa’azi?

5 Hanya ɗaya da muke kasancewa da ƙarfin hali mu yi wa’azi ita ce ta wajen yin addu’a. Wata majagaba ta ce: “Na yi addu’a don na yi magana da gaba gaɗi, na yi addu’a don na iya motsa zuciyar mutane, kuma na yi addu’a don na yi farin ciki a hidimata. Ballantana ma, wannan aikin Jehobah ne, ba tamu ba, saboda haka, ba za mu iya yin kome ba tare da taimakonsa ba.” (1 Tas. 5:17) Dukanmu muna bukatar mu yi addu’a a kai a kai don taimakon ruhu mai tsarki na Allah don mu yi wa’azi da ƙarfin hali.—Luka 11:9-13.

6, 7. (a) Wane wahayi ne Ezekiel ya gani, kuma menene yake nufi? (b) Wane darassi ne wahayin Ezekiel ya koya wa bayin Allah a yau?

6 Littafin Ezekiel ya faɗi wani abu da zai taimake mu mu yi magana da gaba gaɗi. A cikin wani wahayi, Jehobah ya ba Ezekiel littafin da aka rubuta “kuka, da makoki, da labarin balai” a dukan gefen kuma aka gaya masa ya ci shi, yana cewa: “Ɗan mutum, sai ka sa cikinka ya ci, kuma ka cika hanjinka da litafin nan da na ba ka.” Menene wannan wahayin yake nufi? Ya kamata Ezekiel ya fahimci saƙon da zai sanar. Zai zama jikinsa, wato, yana shafan yadda yake ji. Annabin ya ci gaba da cewa: “Sai na ci: a bakina kuwa yana da zaƙi kamar zuma.” Sanar da saƙon Allah a fili yana da daɗi kamar yadda shan zuma yake da zaƙi ga Ezekiel. Ya ji cewa gata ne na musamman ya wakilci Jehobah kuma ya cika wannan aikin da Allah ya ba shi ko idan hakan yana nufin ya sanar da saƙo mai girma ga mutane da ba sa so su ji.—Ka karanta Ezekiel 2:8-3:4, 7-9.

7 Wannan wahayin yana ɗauke da darassi mai kyau ga bayin Allah a yau. Mu ma muna da saƙo mai muhimmanci da za mu sanar wa mutane da ba sa amince da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu ba. Domin mu ci gaba da ɗaukan hidima ta Kirista a matsayin gata da Allah ya ba mu, dole ne mu ci abinci na ruhaniya da kyau. Rashin yin nazari a kai a kai ba zai taimake mu mu fahimci Kalmar Allah sosai ba. Za ka iya kyautata ko kuma ka ƙara yawan lokaci da kake yin nazari da kuma karatun Littafi Mai Tsarki? Za ka iya yin bimbini a kan abin da ka karanta a kai a kai?—Zab. 1:2, 3.

Soma Tattaunawa Daga Littafi Mai Tsarki

8. Menene ya taimaki wasu masu shelar Mulki su soma tattauna Littafi Mai Tsarki a hidima ta gida gida?

8 Ga masu shela da yawa, abu mai wuya a hidima na gida gida shi ne yadda za su soma magana da maigidan. Hakika, a wasu yankuna yana da wuya a soma tattaunawa da mutane. Wasu masu shela sun fi sake jiki sa’ad da suka soma magana da kalmomi kalilan da mutane a ƙofarsu, bayan haka kuma su ba mai gidan warƙa, yadda aka faɗa a akwati da ke cikin wannan talifin. Jigon warkar ko kuma hotunan zai iya jawo hankalin maigidan, hakan zai ba mu zarafin faɗan dalilin da ya sa muka ziyarce shi kuma mu yi tambaya. Wata hanya kuma ita ce nuna wa maigidan warƙoƙi uku ko huɗu kuma ka gaya masa ya zaɓi wanda yake so. Hakika, dalilin ba da warƙoƙi ko kuma yin amfani da su a kowace ƙofa shi ne don mu soma tattauna Littafi Mai Tsarki da zai sa a soma nazarinsa.

9. Me ya sa shiri mai kyau yake da muhimmanci?

9 Kowace hanya ka yi amfani da ita, shiri da kyau zai taimake ka ka kasance a shirye da ƙwazo a hidima ta gida gida. Wani majagaba ya ce: “Na fi yin farin ciki idan na yi shiri da kyau. Yana sa na so yin amfani da abin da na shirya na yi magana da mutane.” Wani majagaba kuma ya ce, “Idan na fahimci littattafai da zan bada, zai sa na yi niyyar yin amfani da su.” Ko da yake yana da kyau mu maimaita abin da za mu faɗa a cikin zuciyarmu, mutane da yawa sun ga ya fi kyau su riƙa furta abin da suke son su faɗa sa’ad da suke maimaitawa. Yin hakan zai sa su yi iya ƙoƙarinsu a hidimar Jehobah.—Kol. 3:23; 2 Tim. 2:15.

10. Menene za a yi don a amfana daga taron fita wa’azi?

10 Yin taron fita wa’azi da kyau yana sa mu ƙware kuma mu yi farin ciki a hidima na gida gida. Idan nassosi na yini na ranar ya yi maganar aikin wa’azi, zai yi kyau a karanta kuma a ɗan tattauna. Duk da haka, ɗan’uwa da yake gudanar da taron fita wa’azi ya ɗauki lokaci ya tattauna ko kuma ya gwada yadda za a yi wa’azi mai sauƙi da ya dace da yankin ko kuma ya tattauna wasu abubuwa da za a yi amfani da shi a hidima na ranar. Hakan zai taimaki waɗanda suka fito hidima su ba da shaida mai kyau. Dattawa da waɗanda suke gudanar da waɗannan taron za su iya cim ma hakan kuma su kammala taron daidai lokaci idan sun yi shiri da kyau.—Rom. 12:8.

Muhimmancin Saurarawa

11, 12. Ta yaya ne saurarawa da kyau zai iya taimakonmu mu yi wa mutane shelar bishara? Ka ba da misali.

11 Ban da shiri mai kyau, ƙaunar mutane za ta taimake mu mu soma tattaunawa daga Littafi Mai Tsarki kuma mu motsa zuciyar mutane a hidima. Wata hanya da za mu nuna irin wannan ƙauna ita ce ta wajen saurarawa. Wani mai kula mai ziyara ya ce: “Yin haƙuri da kuma saurarar mutane yana iya sa su saurari bisharar kuma hakan yana nuna cewa muna ƙaunar mutane.” Saurarawa da kyau zai iya sa masu gidan su gaya mana zuciyarsu, kamar yadda labari na gaba ya nuna.

12 A wasiƙa da aka rubuta a cikin jaridar Le Progrès, da ke birnin Saint-Étienne a Faransa, wata mata ta kwatanta ziyarar da wasu mutane biyu suka yi mata bayan da ta yi rashin ɗiyarta ’yar wata uku. “A nan take na gane cewa su Shaidun Jehobah ne,” ta ce. “Ina son in gaya musu su tafi, sai na lura da wata ƙasida da suke rabawa. Ƙasidar tana magana game da dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala. Sai na ce su shiga da niyyar ƙaryata abubuwan da za su faɗa . . . Shaidun sun zauna fiye da awa ɗaya. Sun saurare ni sosai kuma sun ji tausayi na, na yi farin ciki sosai da suka zo, har na yarda su sake ziyara ta.” (Rom. 12:15) Da shigewar lokaci, wannan mata ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Hakan ya nuna cewa abin da matar ta tuna a ziyararsu ta fari shi ne yadda Shaidun suka saurare ta.

13. Ta yaya za mu iya daidaita bishararmu ga mutanen da muka sadu da su?

13 Sa’ad da muka saurara da kyau, muna barin mutane su gaya mana dalilin da ya sa suke bukatar Mulkin. Hakan zai buɗe mana zarafin yi musu shelar bishara. Wataƙila ka lura cewa waɗanda suke koyarwa da kyau masu saurarawa ne da kyau. (Mis. 20:5) Suna nuna ƙauna ga mutanen da suka sadu da su a hidima. Suna tambayar sunayensu, adireshinsu, abubuwan da suke sha’awa da kuma bukatunsu. Sa’ad da wani ya yi tambaya, suna yin bincike kuma su koma su gaya masa amsar. Kamar manzo Bulus, suna daidaita saƙonsu na Mulki bisa ga mutanen da suka sadu da su. (Ka karanta 1 Korinthiyawa 9:19-23.) Irin wannan ƙauna tana sa mutane su saurari bishara kuma su nuna “jinƙai mai-taushi na Allahnmu.”—Luka 1:78.

Ka Kasance da Halin da ya Dace

14. Sa’ad da muke hidimarmu, ta yaya za mu nuna halayen Jehobah?

14 Jehobah ya daraja mu da ya ba mu ’yancin kai. Ko da yake shi ne Allah maɗaukaki, ba ya tilasta wa mutane su bauta masa, amma yana son mutane su so shi don suna ƙaunarsa, kuma yana yi wa waɗanda suka saurare shi albarka. (Rom. 2:4) Ya kamata mu masu yi masa hidima mu shirya mu yi shelar bishara a hanyar da za ta ɗaukaka Allahnmu mai jin kai a kowane lokacin da za mu yi wa’azi. (2 Kor. 5:20, 21; 6:3-6) Saboda haka muna bukata mu kasance da ra’ayin da ya dace ga mutanen da suke yankinmu. Menene zai iya taimakon mu mu cim ma hakan?

15. (a) Yesu ya umurci mabiyansu su yi menene idan mutane suka ƙi saƙon? (b) Menene zai iya taimakonmu mu samu waɗanda suka cancanta?

15 Yesu ya umurci mabiyansa kada su damu ainun idan wasu suka ƙi saƙon amma su mai da hankali wajen neman waɗanda suka cancanta. (Ka karanta Matta 10:11-15.) Kafa makasudai da zai yiwu zai taimake mu mu cim ma hakan. Wani ɗan’uwa ya kwatanta kansa da mai haƙa rami don neman zinariya. Ƙa’idarsa, ita ce “Ina ɗokin samun zinariya a yau.” Makasudin wani ɗan’uwa kuma shi ne “a kowane mako ya sami wanda yake son saƙon kuma ya koma a cikin ɗan kwanaki ya tattauna da shi.” Wasu masu shela suna ƙoƙari su karanta aya guda a cikin nassi da kowane mai gida idan zai yiwu. Waɗanne makasudai ne da za su yiwu za ka iya kafa wa kanka?

16. Waɗanne dalilai ne muke da shi na ci gaba da yin wa’azi?

16 Yin nasara a hidimar gida gida bai dangana ga yadda mutane suke saurara a yanki kawai ba. Hakika, aikin wa’azi hakki na musamman ne a ceton masu zuciyar kirki, amma yana kuma cika wasu abubuwa masu muhimmanci. Hidima ta Kirista tana ba mu zarafi mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah. (1 Yoh. 5:3) Tana taimakonmu mu guji ɗaukan alhakin jini. (A. M. 20:26, 27) Ta wajen wannan aikin ana yi wa marasa ibada gargaɗi cewa “sa’ar hukuncin [Allah] ta zo.” (R. Yoh. 14:6, 7) Ban da haka, ta wurin wa’azin bishara, ana yabon sunan Jehobah a dukan duniya. (Zab. 113:3) Shi ya sa, ko da mutane sun saurara ko ba su saurara ba, dole ne mu ci gaba da wa’azin saƙon Mulki. Hakika, dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na shelar bishara suna da kyau a gaban Jehobah.—Rom. 10:13-15.

17. Ba da daɗewa ba, menene za a tilasa wa mutane su fahimta?

17 Ko da yake mutane da yawa a yau suna ƙin wa’azi da muke yi, ba da daɗewa ba za su san amfaninsa. (Mat. 24:37-39) Jehobah ya tabbatar wa Ezekiel cewa sa’ad da shelar hukuncin da ya yi suka cika, Isra’ila masu tawaye “za su sani da annabi a cikinsu.” (Ezek. 2:5) Hakanan ma, sa’ad da Allah ya zartar da hukuncinsa a kan wannan zamanin, mutane za su fahimci cewa saƙon da Shaidun Jehobah suka yi wa’azinsa a wuraren da ake samu mutane da kuma gida gida ya fito daga wurin Allah na gaskiya Jehobah, kuma Shaidun wakilansa ne da gaske. Gata ne a gare mu mu masu ɗauke da sunansa mu yi shelar saƙonsa a wannan lokaci na musamman! Da taimakonsa bari mu ci gaba da magance matsaloli na hidimar gida gida.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya za ka kasance da gabagaɗi ka yi wa’azi?

• Menene zai taimake mu mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki a hidima ta gida gida?

• Ta yaya za mu nuna mun damu da wasu?

• Menene zai taimake mu mu kasance da hali mai kyau ga mutane da suke yankinmu?

[Box/Hoto a shafi na 9]

Hanya Ɗaya da za a Soma Tattauna Littafi Mai Tsarki

Yadda za ka soma:

◼ Bayan ka gai da mai gidan, kana iya ba shi warƙa kuma ka ce, “Dalilin ziyara ta a yau shi ne mu tattauna wani batu mai muhimmanci.”

◼ Ko kuma ka ba da warƙa kuma ka ce, “Ina ziyararka a yau domin ina son in san ra’ayinka game da wannan batun.”

Idan an karɓi warƙar:

◼ Ban da dakatawa na dogon lokaci, ka yi tambaya don sanin ra’ayin mutumin bisa jigon warƙar.

◼ Ka saurara da kyau, don ka fahimci ra’ayin maigidan. Ka gode masa don kalaminsa.

Don ka ci gaba da tattaunawa:

◼ Ka karanta kuma ka tattauna nassosi ɗaya ko fiye da haka, ka daidaita abin da kake faɗa da abin da mutumin yake sha’awa da kuma bukatunsa.

◼ Idan mutane suka nuna suna son saƙon, ka ba su littattafai kuma ka gwada musu yadda ake nazarin Littafi Mai Tsarki idan ya yiwu. Ka shirya ka koma.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba