Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 5-9
  • Ka “Faɗi Maganar Allah Da Ƙarfin Zuciya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka “Faɗi Maganar Allah Da Ƙarfin Zuciya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Muna Bukatan Ƙarfin Zuciya
  • Yadda Za Ka Samu Ƙarfin Zuciya
  • Amfanin Kasancewa da Ƙarfin Zuciya
  • Bari Ruhun Allah Ya Sa Ka Kasance da Ƙarfin Zuciya
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Yin Wa’azi Da Ƙarfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Nemi Amsoshin Wadannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Da’ira na 2018-2019​—Mai Kula da Da’ira
  • Ka Ba Mu Karfin Zuciya
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Yadda Za A Magance Ƙalubale Na Hidimar Gida Gida
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 5-9

Ka “Faɗi Maganar Allah Da Ƙarfin Zuciya”

“Suka cika da ruhu mai-tsarki, suka faɗi maganar Allah da ƙarfin zuciya.”—A. M. 4:31.

1, 2. Me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta mu ƙware a hidimarmu?

KWANAKI uku kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” Kafin ya koma sama, Yesu da aka ta da daga matattu ya ba mabiyansa umurni su ‘almajirtar da dukan al’ummai, suna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da ya umurce su.’ Ya yi musu alkawari cewa zai kasance da su “kullayaumi har matuƙar zamani.”—Mat. 24:14; 26:1, 2; 28:19, 20.

2 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna sa hannu sosai a aikin da aka soma a ƙarni na farko. Aikin ceton rai na yin wa’azin Mulki da almajirtarwa ne aiki da ya fi muhimmanci da muke da shi. Saboda haka, yana da muhimmanci mu ƙware a hidimarmu! A wannan talifin, za mu ga yadda ja-gorancin ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu yi magana da ƙarfin zuciya sa’ad da muke hidima. Talifofi biyu na gaba za su nuna yadda ruhun Jehobah zai yi mana ja-gora mu koyar da kyau kuma mu ci gaba da yin wa’azi ba fasawa.

Muna Bukatan Ƙarfin Zuciya

3. Me ya sa yin aikin wa’azin Mulkin yake bukatan ƙarfin zuciya?

3 Aikin da Allah ya ba mu na yin shelar Mulki gata ne mai girma sosai. Amma, a wani lokaci yana da wuya sosai. Ko da yake wasu mutane suna saurarar bisharar Mulkin Allah, yawanci suna kama ne da waɗanda suka rayu a zamanin Nuhu. “Ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka” in ji Yesu. (Mat. 24:38, 39) Bayan haka, akwai kuma waɗanda suke yi mana ba’a ko tsananta mana. (2 Bit. 3:3) Masu iko, abokan makaranta ko abokan aiki, ko kuma waɗanda suke cikin iyalinmu suna iya yin hamayya da mu. Ban da hamayya, muna fama da kumamancinmu, kamar su jin kunya da kuma tsoron yin watsi da mu. Abubuwa da yawa suna iya sa faɗin maganar Allah da “gaba gaɗi” ya yi mana wuya. (Afis. 6:19, 20) Nacewa da faɗin maganar Allah yana bukatan gaba gaɗi. Menene zai taimaka mana mu samu wannan halin?

4. (a) Menene ƙarfin zuciya? (b) Yaya manzo Bulus ya kasance da ƙarfin zuciya don ya yi magana da Tasalonikawa?

4 Kalmar Helenanci da aka fassara “ƙarfin zuciya” tana nufin “faɗin magana a fili, faɗan gaskiya.” Wannan kalmar tana nufin “gaba gaɗi, aminci, . . . rashin tsoro.” Ƙarfin zuciya ba ya nufin yin baƙar magana ko kuma taurin kai. (Kol. 4:6) Yayin da muke da ƙarfin zuciya, muna bukatan mu zauna lafiya da dukan mutane. (Rom. 12:18) Bugu da ƙari, yayin da muke wa’azin bisharar Mulkin Allah, muna bukatan mu kasance da daidaita tsakanin yin magana da ƙarfin zuciya da kasancewa da basira don kada mu ɓata wa mutane rai. Hakika, don mu kasance da ƙarfin zuciya da ya dace, muna bukatan mu nuna halayen da ake bukatan a ƙoƙarta sosai kafin mu same su. Amma don mu nuna irin wannan ƙarfin zuciya, ba za mu dogara ga iyawarmu ko kuma ƙarfinmu kawai ba. Bayan da aka ‘wulakanta su a Filibbi,’ yaya manzo Bulus da abokansa suka “yi ƙarfin hali” don su yi magana ga waɗanda suke Tasalonika? “Cikin Allahnmu” in ji Bulus. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:2.) Jehobah Allah yana iya kawar da tsoron da muke ji kuma ya ba mu irin wannan ƙarfin zuciyar.

5. Yaya Jehobah ya ba Bitrus, Yohanna, da sauran almajirai ƙarfin zuciya?

5 Sa’ad da “mahukuntan [mutanen] da datiɓansu da marubutansu” suka zarge su, manzo Bitrus da Yohanna suka ce: “Ko daidai ne gaban Allah mu fi jinku da Allah, sai ku hukunta: gama ba shi yiwuwa a garemu mu rasa faɗin abin da muka ji muka gani.” Maimakon su yi addu’a ga Allah don a daina tsananta musu, su da ’yan’uwa masu bi suka yi roƙo, cewa: “Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfin zuciya duka.” (A. M. 4:5, 19, 20, 29) Yaya Jehobah ya amsa roƙonsu? (Karanta A. M. 4:31.) Jehobah ya taimaka musu su kasance da ƙarfin zuciya ta hanyar ruhunsa. Ruhun Allah zai iya yi mana hakan. Ta yaya za mu samu ruhun Allah kuma ya yi mana ja-gora a hidimarmu?

Yadda Za Ka Samu Ƙarfin Zuciya

6, 7. Wace hanya ce ta kai tsaye za mu samu ruhu mai tsarki na Allah? Ka ba da misalai.

6 Yadda za ka fi samun ruhu mai tsarki na Allah kai tsaye shi ne yin roƙon samunsa. Yesu ya gaya wa masu sauraronsa: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luk 11:13) Hakika, ya kamata mu yi addu’a a kai a kai don samun ruhu mai tsarki. Idan muna jin tsoron wasu fannoni na hidima, kamar yin wa’azi a kan titi, yin wa’azi sa’ad da zarafin yin hakan ya samu, ko kuma yin wa’azi a yankin da ake yin kasuwanci, muna iya yin addu’a ga Jehobah don ya ba mu ruhunsa kuma mu gaya masa ya taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya da ake bukata.—1 Tas. 5:17.

7 Abin da wata mata Kirista mai suna Rosa ta yi ke nan.a Wata rana sa’ad da Rosa take wajen aikinta, wata malama da suke aiki tare tana karanta wani rahoto daga wata makaranta game da yadda ake wulakanta yara. Abin da malamar ta karanta ya dame ta sosai har ta ce, “Wai menene duniyar nan take juyawa ne?” Rosa ba ta ƙyale irin wannan zarafin ya wuce ta, ba tare da yin wa’azi ba. Menene ta yi don ta samu ƙarfin zuciyar soma yin magana? “Na yi addu’a ga Jehobah kuma na roƙa shi ya taimake ni da ruhunsa,” in ji Rosa. Ta ba da shaida mai kyau kuma ta yi shirin ƙara tattaunawa a kan batun. Ka yi la’akari kuma da labarin wata yarinya ’yar shekara biyar mai suna Milane, wadda take da zama a Birnin New York. Milane ta ce: “Kafin na tafi makaranta, ni da mamata muna yin addu’a a koyaushe ga Jehobah.” Menene suke addu’a a kai? Don Milane ta kasance da ƙarfin zuciya kuma ta yi magana game da Allahnta! “Hakan ya taimaka wa Milane ta bayyana matsayinta game da bikin ranakun haihuwa da bukukuwan da Allah ba ya so kuma ta ƙi sa hannu sa’ad da ake yin waɗannan bukukuwa,” in ji mamarta. Waɗannan misalan sun nuna cewa addu’a tana taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya.

8. Menene za mu iya koya daga annabi Irmiya game da samun ƙarfin zuciya?

8 Ka yi tunani a kan abin da ya taimaka wa annabi Irmiya ya samu ƙarfin zuciya. Sa’ad da Jehobah ya naɗa shi annabi ga al’ummai, Irmiya ya ce: “Ga shi, ni ban iya magana ba: gama ni yaro ne.” (Irm. 1:4-6) Amma, da shigewar lokaci, Irmiya ya nace kuma ya kasance mai magana da ƙarfi sosai a wa’azinsa da har yawancin mutane suka ɗauke shi mai saƙon bala’i kawai. (Irm. 38:4) Ya yi shelar hukuncin Jehobah da gaba gaɗi fiye da shekaru 65. An san shi sosai a Isra’ila don wa’azinsa da ƙarfin zuciya da kuma rashin tsoro har ta kai ga bayan fiye da shekaru 600 sa’ad da Yesu ya yi magana da ƙarfin zuciya, wasu sun gaskata cewa Irmiya ne ya sake dawowa. (Mat. 16:13, 14) Yaya annabi Irmiya mai jinkiri a dā ya sha kan kunyar da yake ji? Ya ce: “Cikin zuciyata [kalmar Allah ta zama] kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana, in gaji kuma da haƙuri.” (Irm. 20:9) Hakika, kalmar Jehobah ta ƙarfafa Irmiya kuma ta motsa shi ya yi magana.

9. Me ya sa kalmar Allah za ta iya shafan mu yadda ta shafi Irmiya?

9 A cikin wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, manzo Bulus ya rubuta: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa mararrabar rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) Saƙo, ko kalmar Allah za ta iya shafanmu yadda ta shafi Irmiya. Ka tuna cewa ko da yake an yi amfani da mutane su rubuta Littafi Mai Tsarki, ba tarin littattafai ba ne da ke ɗauke da hikimar ’yan Adam ba, domin Allah ne ya hure shi. 2 Bitrus 1:21 ta ce: “Ba a taɓa kawo kowane annabci bisa ga nufin mutum ba: amma mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” Sa’ad da muka keɓe lokaci muka yi nazari mai ma’ana na Littafi Mai Tsarki, za mu cika zuciyarmu da saƙon da ruhu mai tsarki ya hure. (Karanta 1 Korantiyawa 2:10.) Wannan saƙon yana iya zama kamar “wuta mai-ƙonewa” a cikinmu, kuma hakan zai hana mu riƙe saƙon ga kanmu kawai.

10, 11. (a) Yaya ya kamata mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki idan muna son mu samu ƙarfin zuciyar yin magana? (b) Ka ambata aƙalla mataki guda da ka shirya za ka ɗauka domin ka kyautata nazari na kanka.

10 Don nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu ya shafe mu sosai, ya kamata mu yi shi yadda saƙon da ke cikin Littafi Mai tsarki zai motsa zuciyarmu, kuma ya shafe mu a ciki. Alal misali, an nuna wa annabi Ezekiel wahayi inda aka ce ya ci littafi naɗaɗɗe da ke ɗauke da saƙon hukuncin da za a isar ga mutanen da ba sa so su ji. Ezekiel yana bukatan ya fahimcin saƙon sosai kuma ya zama jikinsa. Yin hakan zai sa aikin isar da wannan saƙon ya yi daɗi kamar zuma.—Karanta Ezekiel 2:8–3:4, 7-9.

11 Muna cikin yanayin da ya yi kama da na Ezekiel. A yau, mutane da yawa ba sa son su ji abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Idan za mu nace da yin maganar Allah, yana da muhimmanci mu yi nazarin Nassosi yadda za mu fahimce shi sosai kuma mu gaskata abin da ya faɗa. Ya kamata mu riƙa nazari a kai a kai, ba jifa-jifa ba. Ya kamata muradinmu ya zama kamar na mai zabura wanda ya rera: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.” (Zab. 19:14) Yana da muhimmanci mu ɗauki lokaci mu yi bimbini a kan abin da muka karanta, domin gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta kahu sosai a cikin zuciyarmu! Hakika, ya kamata mu ƙoƙarta mu kyautata nazari na kanmu.b

12. Me ya sa taron Kirista yake ba da taimako don ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora?

12 Wata hanya da za mu amfana daga ruhu mai tsarki na Jehobah ita ce “mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.” (Ibran. 10:24, 25) Yin ƙoƙari mu halarci taron Kirista a kai a kai, mu saurara da kyau, da kuma yin amfani da abin da muka koya, hanyoyi ne masu kyau da ruhu zai yi mana ja-gora. Ballantana ma, ruhun Jehobah yana yin ja-gora ta hanyar ikilisiya.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 3:6.

Amfanin Kasancewa da Ƙarfin Zuciya

13. Menene za mu iya koya daga abin da Kiristoci a ƙarni na farko suka cim ma a aikin wa’azi?

13 Ruhu mai tsarki ne ikon da ya fi ƙarfi a sararin samaniya, kuma zai iya ƙarfafa ’yan Adam su yi nufin Jehobah. A ƙarƙashin tasirinsa, Kiristoci na ƙarni na farko sun cim ma aikin wa’azi mai girma. Sun yi wa’azin bishara a “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Sa’ad da muka lura cewa yawancinsu “marasa-karatu ne,” hakan ya tabbatar da cewa iko mafi ƙarfi ne ya motsa su.—A. M. 4:13.

14. Menene zai taimaka mana mu riƙa “huruwa a cikin ruhu”?

14 Yin rayuwar da ta jitu da ja-gorar ruhu mai tsarki zai ƙarfafa mu kuma ya motsa mu mu yi hidimarmu da gaba gaɗi. Game da “wani Bayahudi, sunansa Apollos, asalinsa Ba’iskandari, mutum mai-hikima, [wanda] ya zo Afisus,” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Domin yana da zafin himma a ruhu, ya yi ta zance, yana koyarwa da zancen Yesu bisa ga hankali.” (A. M. 18:24, 25) Ta wurin “huruwa a cikin ruhu,” muna iya ƙara kasancewa da ƙarfin zuciya a hidimarmu ta gida-gida da kuma sa’ad da muka sami zarafin yin wa’azi.—Rom. 12:11.

15. Ta yaya yin magana da ƙarin gaba gaɗi yake amfanarmu?

15 Ƙara kasancewa da gaba gaɗi a aikin wa’azi zai kasance da tasiri mai kyau a gare mu. Muna kyautata halinmu domin mun fahimci muhimmanci da kuma amfanin aikinmu sosai. Muna ƙara kasancewa da himma domin muna yin farin ciki sosai sa’ad da muka ƙware a hidima. Muna ƙarfafa himmarmu domin mun san gaggawar aikin wa’azi.

16. Menene ya kamata mu yi idan himmarmu don hidima ta ragu?

16 Idan muka daina kasancewa da himma a hidima ko kuma himmarmu ba kamar yadda take a dā ba kuma fa? Hakan zai bukaci mu bincika kanmu sosai. Bulus ya rubuta: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.” (2 Kor. 13:5) Ka tambayi kanka, ‘Har ila ina huruwa a cikin ruhu? Ina addu’a ga Jehobah ya ba ni ruhunsa? Addu’o’ina suna nuna cewa na dogara a gare shi don yin nufinsa? Sun ƙunshi kalaman godiya don hidima da aka ɗanka mana? Yaya nazari na kaina yake? Menene yawan lokacin da nake amfani da shi don yin bimbini a kan abin da na karanta da wanda na ji? Ina saurarawa da yin kalami a taron ikilisiya yadda ya kamata?’ Yin tunani a kan irin waɗannan tambayoyi za su taimaka maka ka san wuraren da za ka yi gyara.

Bari Ruhun Allah Ya Sa Ka Kasance da Ƙarfin Zuciya

17, 18. (a) Yaya yawan yadda ake aikin wa’azi a yau? (b) Yaya za mu iya nuna “gaba gaɗi sarai” a shelar bisharar Mulkin Allah?

17 Yesu da aka ta da daga matattu ya gaya wa almajiransa: “Za ku karɓi iko lokacin da ruhu mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) A yau, ana yin aikin da aka soma a wannan lokacin sosai. Shaidun Jehobah fiye da miliyan bakwai ne suke shelar saƙon Mulki a ƙasashe fiye da 230, suna ba da sa’o’i kusan biliyan ɗaya da ɗari biyar a kowace shekara a hidima. Abin ban sha’awa ne a kasance da himma wajen yin wannan aikin da ba za a maimaita ba!

18 Kamar yadda yake a ƙarni na farko, ana yin aikin wa’azi a dukan duniya a ƙarƙashin ja-gorancin ruhun Allah. Idan muka bi ja-gorancin ruhun, za mu kasance da “gaba gaɗi sarai” a hidimarmu. (A. M. 28:31) Saboda haka, bari ruhun ya yi mana ja-gora yayin da muke shelar bisharar Mulkin Allah!

[Hasiya]

a An canja sunayen.

b Don ka amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki da nazari na kanka, ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, babobi masu jigo “Apply Yourself to Reading” (Ka Ba da Kanka ga Karatu) da “Study Is Rewarding,” (Nazari Yana da Lada Mai Kyau,” shafuffuka na 21 zuwa 32.

Menene Ka Koya?

• Me ya sa muke bukatan mu kasance da gaba gaɗi sa’ad da muke maganar Allah?

• Menene ya taimaka wa almajirai na farko su yi magana da ƙarfin zuciya?

• Yaya za mu kasance da ƙarfin zuciya?

• Yaya kasancewa da ƙarfin zuciya yake amfanar mu?

[Hoton da ke shafi na 7]

Yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su kasance da ƙarfin zuciya?

[Hotuna da ke shafi na 8]

Yin gajeriyar addu’a zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya a hidima

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba