Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Yin Wa’azi Da Ƙarfin Zuciya
“Muka yi ƙarfin hali . . . da za mu faɗa maku bisharar.”—1 TAS. 2:2.
1. Me ya sa bisharar Mulki take da kyau sosai?
ABU ne mai kyau a ji labari mai daɗi! Kuma labari mafi daɗi a cikin dukan labarai shi ne bisharar Mulkin Allah. Wannan bishara ta tabbatar mana cewa za a kawo ƙarshen wahala, ciwo, azaba, baƙin ciki da mutuwa. Ta sa mu kasance da begen samun rai madawwami, ta bayyana mana nufe-nufen Allah, kuma ta nuna mana yadda za mu ƙulla dangantaka na ƙauna da shi. Za ka yi tunanin cewa kowa zai yi farin cikin jin wannan bishara da Yesu ya gaya wa ’yan adam. Abin baƙin ciki, ba haka ba ne.
2. Ka ba da bayanin kalamin Yesu: “Na zo domin in haɗa mutum.”
2 Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kada ku yi tsammani na zo domin in kawo wa duniya salama: a’a ban zo domin in kawo salama ba, amma takobi. Gama na zo domin in haɗa mutum da ubansa, ɗiya kuma da uwatata, surukuwa kuma da sarakuwatata: maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Mat. 10:34-36) Maimakon su amince da bisharar, yawancin mutane sun ƙi ta. Wasu sun mai da kansu maƙiyan waɗanda suke shelarta, ko suna cikin iyali ɗaya.
3. Menene muke bukata don mu cim ma aikinmu na wa’azi?
3 Muna shelar gaskiyar da Yesu ya yi shelarta, kuma sa’ad da mutane suka ji wa’azi a yau, suna aikatawa yadda suka aikata a zamaninsa. Mun san cewa hakan zai faru. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Bawa bai fi ubangijinsa girma ba. Idan suka tsananta mini, zasu tsananta muku kuma.” (Yoh. 15:20) A ƙasashe da yawa ba ma fuskantar tsanantawa kai tsaye, amma muna fuskantar reni da kuma wariya. Saboda haka, muna bukatar bangaskiya da ƙarfin zuciya don mu jimre a aikinmu na wa’azin bishara da gaba gaɗi.—Karanta 2 Bitrus 1:5-8.
4. Me ya sa Bulus yake bukatar ya kasance da “ƙarfin hali” don ya yi wa’azi?
4 Wataƙila zuwa hidimar fage yana yi maka wuya, ko kuma wasu fannoninsa suna yi maka wuya. Ba kai kaɗai ba ne mai shela mai aminci da ke jin hakan ba. Manzo Bulus mai wa’azi ne da ƙarfin zuciya da ba ya jin tsoro kuma ya fahimci gaskiya sosai, duk da haka, akwai lokacin da ya yi fama don ya yi wa’azi. Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke Tasalonika cewa: “Da muka rigaya muka sha wuya, har da wulakanci, yadda kun sani, cikin Filibbi, muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin husuma mai-yawa.” (1 Tas. 2:2) A Filibi masu mulki sun yi wa Bulus da abokinsa Sila dūka da sanda, suka jefa su kurkuku, kuma suka sa ƙafafunsu cikin turu. (A. M. 16:16-24) Duk da haka, Bulus da Sila suka “yi ƙarfin hali” suka ci gaba da wa’azi. Ta yaya za mu iya yin hakan? Don mu sami amsar, bari mu bincika abin da ya taimaki bayin Allah a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki su yi magana game da Jehobah da ƙarfin zuciya, kuma mu koyi yadda za mu bi misalinsu.
Ana Bukatar Ƙarfin Zuciya Don a Fuskanci Magabtaka
5. Me ya sa waɗanda suke da aminci ga Jehobah suke bukatar ƙarfin zuciya?
5 Hakika, Yesu Kristi ne misali mafi kyau na ƙarfin hali da gaba gaɗi. Duk da haka, tun farko tarihin ’yan adam, dukan waɗanda suke da aminci ga Jehobah suna bukatar su kasance da ƙarfin zuciya. Me ya sa? Sa’ad da aka yi tawaye a Adnin, Jehobah ya annabta cewa magabtaka za ta kasance tsakanin waɗanda suke bauta wa Allah da waɗanda suke bauta wa Shaiɗan. (Far. 3:15) An ga wannan magabtaka nan da nan sa’ad da Kayinu ya kashe ɗan’uwansa, Habila, mutum mai adalci. Daga baya, an nuna magabtaka ga Anuhu, wani mutum mai aminci da ya yi rayuwa kafin Rigyawa. Ya yi annabci cewa Allah zai zo da rundunarsa masu tsarki don ya zartar da hukunci a kan marasa bin Allah. (Yahu. 14, 15) Babu shakka, mutane da yawa ba sa son wannan saƙon. Mutane sun ƙi jinin Anuhu, kuma wataƙila da sun kashe shi da a ce Jehobah bai ɗauki ransa ba. Babu shakka Anuhu ya nuna ƙarfin zuciya!—Far. 5:21-24.
6. Me ya sa Musa yake bukatar ƙarfin zuciya sa’ad da yake magana da Fir’auna?
6 Ka yi tunanin ƙarfin zuciya da Musa ya nuna sa’ad da ya yi magana da Fir’auna, sarkin da ake ɗauka a matsayin alla da kansa, ɗan Ra, allan rana, ba kawai wanda yake wakiltar alloli ba. Wataƙila, kamar sauran Fir’auna, ya bauta wa siffarsa. Kalmar Fir’auna doka ce; yana sarauta bisa doka. Da yake shi mai iko ne, girman kai, da kuma taurin kai, sun hana shi karɓan shawara daga wajen mutane. A gaban wannan mutumi ne Musa makiyayi mai tawali’u, ya bayyana a kai a kai ko da yake ba a gayyace shi ba kuma ba a son sa. Menene Musa ya annabta? Za a yi annoba masu ɓarna. Kuma menene yake son a yi masa? Yana son Fir’auna ya ba da izini don miliyoyin bayin Fir’auna su bar ƙasar! Musa yana bukatar ƙarfin zuciya ne? Ƙwarai kuwa!—Lit. Lis. 12:3; Ibran. 11:27.
7, 8. (a) Wane gwaji ne masu aminci da suka yi rayuwa kafin Kristi suka fuskanta? (b) Menene ya taimaki waɗanda suka rayu kafin zamanin Kiristanci su kasance da ƙarfin zuciya wajen ɗaukaka da kuma faɗaɗa bauta ta gaskiya?
7 Ƙarnuka da yawa bayan fitowarsu, annabawa da wasu bayin Allah masu aminci sun ci gaba da nuna ƙarfin zuciya don bauta ta gaskiya. Duniyar Shaiɗan ta tsananta musu. Bulus ya ce: “Aka jejjefe su da duwatsu, aka raba su biyu da zarto, aka jarabce su, aka sare su da takobi: suka yi yawo cikin fatun tumaki, da fatun awakai; suka sha rashi; ƙuntattu ne, wulakantattu.” (Ibran. 11:37) Menene ya taimaki waɗannan bayin Allah masu aminci su yi tsayin daka? A ayoyi kalilan na farko, manzon ya faɗi abin da ya ba Habila, Ibrahim, Saratu, da wasu ƙarfin jimrewa. Ya ce: “Ba su rigaya sun amshi alkawurai ba, amma [da bangaskiya] daga nesa suka tsinkaye su, suka yi masu maraba.” (Ibran. 11:13) Babu shakka, an taimaki annabawa kamar su Iliya, Irmiya, da wasu masu aminci kafin zamanin Kiristanci, waɗanda da ƙarfin zuciya suka yin tsayin daka don bauta ta gaskiya su jimre ta wajen dogara ga cikar alkawuran Jehobah.—Tit. 1:2.
8 Waɗannan masu aminci da suka rayu kafin zamani Kiristanci suna begen rayuwa mai kyau da za a yi a nan gaba. Sa’ad da aka ta da su daga matattu, daga baya za su zama kamilai kuma su “tsira daga bautar ɓacewa” ta wurin hidimomin firist Yesu Kristi, da kuma mataimakansa 144,000. (Rom. 8:21) Bugu da ƙari, Irmiya da wasu bayin Allah masu ƙarfin zuciya a zamanin dā sun kasance da ƙarfin zuciya domin tabbacin Jehobah da ke cikin alkawarin da ya yi wa Irmiya: “Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.” (Irm. 1:19) A yau, idan muka yi tunani a kan alkawuran Allah don nan gaba da kuma tabbacinsa na kāriya na ruhaniya, mu ma muna samun ƙarfafa.—Mis. 2:7; karanta 2 Korantiyawa 4:17, 18.
Ƙauna ta Motsa Yesu Ya Yi Wa’azi da Ƙarfin Zuciya
9, 10. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna gaba gaɗi a gaban (a) shugabannin addinai, (b) rukunin sojoji, (c) babban firist, (d) da Bilatus?
9 Yesu, wanda muke bin misalinsa ya nuna gaba gaɗinsa a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, ko da yake waɗanda suke da iko da tasiri sun ƙi jininsa, Yesu bai sauƙaƙa saƙon da Allah yake son mutane su ji ba. Da gaba gaɗi ya fallasa shugabanin addinai masu iko don adalcin kansu da kuma koyarwarsu na ƙarya. Yesu ya yi magana kai tsaye kuma kalmominsa sun fita sarai sa’ad da ya hukunta waɗannan mutane. Akwai lokacin da ya ce: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, munafukai! gama kuna kama da fararen kabarbura, waɗanda suna da kyaun gani daga waje, amma daga ciki cike su ke da ƙasussuwan matattu, da kowace irin ƙazamta. Hakanan ku kuma daga waje ana ganinku masu-adalci, amma daga ciki cike ku ke da riya da mugunta.”—Mat. 23:27, 28.
10 Da rukunin sojoji suka same shi a lambun Jathsaimani, Yesu ya nuna kansa da gaba gaɗi. (Yoh. 18:3-8) Daga baya aka kai shi gaban Majalisa kuma babban firist ya tuhume shi. Ko da yake ya san cewa babban firist yana neman illa don ya kashe shi, Yesu da ƙarfin zuciya ya tabbatar masa cewa shi Kristi ne da Ɗan Allah. Ya daɗa cewa za su gan shi “zaune ga hannun dama na iko, yana zuwa tare da gizagizan sama.” (Mar. 14:53, 57-65) Jim kaɗan bayan haka, an kai Yesu a gaban Bilatus wanda zai iya ’yantar da shi. Amma Yesu bai ce uffan ba ga dukan zargin da ake masa. (Mar. 15:1-5) Dukan waɗannan suna bukatar mutum ya kasance da ƙarfin zuciya.
11. Yaya ƙarfin zuciya yake da nasaba da ƙauna?
11 Yesu ya gaya wa Bilatus: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yoh. 18:37) Jehobah ya ba Yesu aikin wa’azin bishara, kuma Yesu ya yi farin cikin yin hakan domin yana ƙaunar Ubansa na samaniya. (Luk 4:18, 19) Yesu kuma yana ƙaunar mutane. Ya san cewa rayuwarsu tana da wuya. Hakazalika, muna wa’azi da ƙarfin zuciya ban da tsoro domin muna ƙaunar Allah da maƙwabcinmu.—Mat. 22:36-40.
Ruhu Mai Tsarki na Ƙarfafa Mu Mu Yi Wa’azi da Ƙarfin Zuciya
12. Menene ya sa almajirai na farko farin ciki?
12 Makonni bayan mutuwar Yesu, almajiran sun yi farin cikin ganin cewa Jehobah ya daɗa musu sababbin almajirai. A cikin rana guda, an yi wa Yahudawa da shigaggu dubu uku baftisma, waɗanda suka zo Urushalima daga ƙasashe dabam-dabam don bikin Fentakos! Babu shakka, mutanen da ke Urushalima sun yi magana game da abin da ya faru! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsoro ya afko wa kowane mai-rai, kuma aka gudana da al’ajibai da alamu da yawa ta hannun manzannin.”—A. M. 2:41, 43.
13. Me ya sa ’yan’uwan suka yi addu’a don samun ƙarfin zuciya, kuma menene sakamakon?
13 Domin sun ji haushi, shugabannin addinai sun kama Bitrus da Yohanna, suka sa su kwana a kurkuku kuma suka umurce su kada su yi magana game da Yesu. Da aka sake su, su biyun sun gaya wa ’yan’uwan abin da ya faru, kuma dukansu suka yi addu’a game da hamayyar da suke fuskanta, kuma suka yi wannan roƙon: “[Jehobah] ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfin zuciya duka.” Menene sakamakon? “Dukansu suka cika da Ruhu Mai-tsarki, suka faɗi maganar Allah da ƙarfin zuciya.”—A. M. 4:24-31.
14. Yaya ruhu mai tsarki yake taimakonmu a wa’azi?
14 Ka lura cewa ruhu mai tsarki mai iko na Jehobah ne ya taimaki almajiran su yi maganar Allah da ƙarfin zuciya. Ƙarfin zuciyar faɗin gaskiya ga mutane, har ga waɗanda suke hamayya da saƙonmu bai dangana a gare mu ba. Jehobah yana iya ba mu ruhunsa mai tsarki idan muka roƙe shi. Da taimakon Jehobah, mu ma za mu iya nuna ƙarfin zuciya da ake bukata don mu jimre kowace hamayya da aminci.—Karanta Zabura 138:3.
Kiristoci a Yau Suna Wa’azi da Ƙarfin Zuciya
15. Yaya gaskiya take raba mutane a yau?
15 Kamar yadda yake a dā, gaskiya ta ci gaba da raba mutane a zamaninmu. Wasu suna saurarar wa’azi, wasu kuma ba sa fahimta da kuma daraja yadda muke bauta. Wasu suna zargin mu, suna yi mana ba’a kuma sun tsane mu, kamar yadda Yesu annabta. (Mat. 10:22) Wani lokaci, muna zama waɗanda ake yin ƙarya game da su da kuma tsegumi a hanyar watsa labarai. (Zab. 109:1-3) Duk da haka, a dukan duniya, mutanen Jehobah suna shelar bishara da ƙarfin zuciya.
16. Wane labari ne ya nuna cewa kasancewa da ƙarfin zuciya zai iya canja ra’ayin mutanen da muka yi wa wa’azi?
16 Ƙarfin zuciyarmu yana iya sa mutane su canja ra’ayinsu game da saƙon Mulki. Wata ’yar’uwa a birnin Kyrgyzstan ta ba da wannan labarin: “Sa’ad da nake aikin wa’azi, wani maigida ya ce mini: ‘Na yi imani da Allah amma ba Allah na Kirista ba. Idan kika sake zuwa ƙofar gidan nan, zan cuna miki kare na!’ A bayansa da akwai karen da aka ɗaure da sarka. Amma, a lokacin kamfen na rarraba warƙar Kingdom News na 37 mai jigo, ‘Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!,’ na tsai da shawarar sake komawa wannan gidan da begen cewa zan sadu da wani a cikin iyalin wannan mutumin. Amma, wannan mutumin ne ya buɗe ƙofa. Nan da nan na yi addu’a ga Jehobah kuma na ce: ‘Na tuna taɗin da muka yi kwanaki uku da suka wuce, na kuma tuna da karen ka. Amma ina son na baka wannan warƙar domin na yi imani da Allah makaɗaici na gaskiya kamar yadda ka yi imani. Ba da daɗewa ba Allah zai hukunta addinai da ba sa ɗaukaka shi. Za ka ƙara koya game da hakan ta wajen karanta wannan.’ Na yi mamaki da wannan mutum ya karɓi wannan warƙa. Sai na wuce zuwa wani gida. Bayan ’yan mintoci, sai mutumin ya rugo ya zo ya same ni da warƙar a hannunsa. Ya ce, ‘na karanta. Menene nake bukatar na yi don kada na sha fushin Allah?’” Aka soma nazari da mutumin, kuma ya soma halartan taron Kirista.
17. Yaya ƙarfin zuciya na wata ’yar’uwa ya ƙarfafa wata ɗaliba na Littafi Mai Tsarki mai jin tsoro?
17 Kasancewa da ƙarfin zuciya zai iya ƙarfafa wasu su yi hakan. A Rasha, wata ’yar’uwa da take tafiya a cikin bas ta ba wata matar da ke cikin motar mujalla. Sai wani mutum ya miƙe daga inda yake zaune ya ƙwace mujallar daga hannun ’yar’uwar, ya dunƙule ta kuma ya jefar a ƙasa. Da yake zaginta, ya gaya wa ’yar’uwar ta ba shi adireshinta kuma ya gaya mata kada ta yi wa’azi a ƙauyen. ’Yar’uwar ta yi addu’a ga Jehobah don taimako kuma ta tuna kalmomin Yesu: “Kada ku ji tsoron waɗannan da su ke kisan jiki.” (Mat. 10:28) A hankali ta tashi kuma ta gaya wa mutumin, “Ba zan ba ka adireshi na ba, kuma zan ci gaba da wa’azi a ƙauyen.” Sai ta fita daga bas ɗin. ’Yar’uwar ba ta sani ba cewa ɗalibarta na Littafi Mai Tsarki tana cikin wannan motar. Matar ta ƙyale tsoron mutane ya hana ta halartan taron Kirista. Amma, bayan da ta ga ƙarfin zuciyar da ’yar’uwanmu ke da shi, ɗalibar na Littafi Mai Tsarki ta tsai da shawarar soma halartan taro.
18. Menene zai taimake ka ka yi wa’azi da ƙarfin zuciya, kamar yadda Yesu ya yi?
18 A wannan duniyar da ke rabe daga Allah, ana bukatar ƙarfin zuciya don a yi wa’azi yadda Yesu ya yi. Menene zai taimake ka ka yi hakan? Ka kasance da bege don gaba. Ka sa ƙaunarka ga Allah da maƙwabci ta yi ƙarfi. Ka yi addu’a ga Jehobah don ka kasance da ƙarfin zuciya. A koyaushe ka tuna cewa Yesu yana tare da kai. (Mat. 28:20) Ruhu mai tsarki zai ƙarfafa ka. Kuma Jehobah zai albarkace ka kuma ya tallafa maka. Saboda haka, bari mu kasance da ƙarfin hali kuma mu ce: “Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum zai mini?”—Ibran. 13:6.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa bayin Allah suke bukatar ƙarfin zuciya?
• A batun kasancewa da ƙarfin zuciya, menene muka koya daga . . .
masu aminci da suka yi rayuwa kafin Kristi?
Yesu Kristi?
Kiristoci na farko?
Kiristoci a yau?
[Hotunan da ke shafi na 21]
Yesu ya fallasa shugabannin addinai da gaba gaɗi
[Hotunan da ke shafi na 23]
Jehobah yana ba mu ƙarfin zuciya mu yi wa’azi