Hanya Mai Kyau da Za Mu More Waƙoƙinmu
Bayin Allah suna ɗaukan waƙoƙi a matsayin baiwa mai kyau daga wurin Jehobah. (Yaƙ. 1:17) Ikilisiyoyi da yawa suna more kaɗa Waƙoƙinmu kafin da kuma bayan tarurruka na ikilisiya. Kaɗa waƙoƙi na tsarin Allah hanya ce mai kyau na marabtarmu zuwa tarurruka. Yana taimaka mana mu yi shirin mai da hankalinmu ga taron. Ƙari ga hakan, kaɗa sababbin waƙoƙi daga littafin waƙarmu yana sa mu saba da waƙoƙin kuma yana taimaka mana mu iya rera waƙoƙin sosai. Irin wannan waƙar da ake kaɗawa bayan taro yana sa mu iya ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiya sosai. Saboda haka, rukunin dattawa ya shirya yadda za a riƙa yin kaɗe-kaɗe daga faifan nan Sing to Jehovah—Piano Accompaniment kafin taro da kuma bayan taro. Su tabbata cewa muryar kiɗar ba ta hana mutane tattaunawa da juna ba.