Ka Rera Waƙa Ga Jehobah!
“In raira yabbai ga Allahna har iyakar raina.”—ZAB. 146:2.
1. Mene ne ya motsa Dauda ya rubuta wasu waƙoƙin da ke cikin zabura?
SA’AD da yake matashi, Dauda ya yi amfani da sa’o’i da yawa a filaye kusa da Bai’talami yana kiwon tumakin mahaifinsa. Da yake kula da tumakin, Dauda ya samu zarafin lura da ayyukan halittu masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi, wato, sararin samaniya, da “namomin jeji,” da kuma “tsuntsayen sama.” Abubuwan da ya gani sun shafe shi sosai da har hakan ya motsa shi ya rera waƙoƙi na yabo masu motsa zuciya ga Mahaliccin waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi. Ana iya ganin waɗannan waƙoƙi masu yawa da Dauda ya rera a cikin littafin Zabura.a—Karanta Zabura 8:3, 4, 7-9.
2. (a) Yaya kiɗa zai iya shafan mutum? Ka ba da misali. (b) Mene ne za mu iya koya game da dangantakar Dauda da Jehobah daga Zabura 34:7, 8 da Zabura 139:2-8?
2 Mai yiwuwa a wannan lokacin ne Dauda ya ƙware a matsayin mawaƙi. Ya ƙware sosai har da aka kira shi ya kaɗa wa Sarki Saul garaya. (Mis. 22:29) Waƙar Dauda takan kwantar da hankalin sarkin da ya damu, kamar yadda kiɗa mai daɗi sau da yawa yake yi wa mutane a yau. Duk lokacin da Dauda ya ɗauki garayarsa, “Saul ya kan wartsake, ya sami lafiya.” (1 Sam. 16:23) Waƙoƙi da wannan mawaƙin mai jin tsoron Allah da mai rubuta waƙoƙi ya rera suna da amfani har yau. Ka yi la’akari da wannan batun! A yau, fiye da shekaru dubu uku bayan haihuwar Dauda, miliyoyin mutane masu yanayi dabam dabam da suke da zama a wurare dabam dabam na duniya a kai a kai suna karanta zabura na Dauda don su samu ta’aziya da bege.—2 Laba. 7:6; karanta Zabura 34:7, 8; 139:2-8; Amos 6:5.
Kiɗa Yana da Matsayi Mai Daraja a Bauta ta Gaskiya
3, 4. Waɗanne shirye-shirye na haɗa waƙa a bauta mai tsarki aka yi a zamanin Dauda?
3 Dauda yana da iyawa, kuma ya yi amfani da iyawarsa a hanyar da ta fi kyau, wato, don ya ɗaukaka Jehobah. Bayan ya zama sarkin Isra’ila, Dauda ya shirya a saka kiɗa mai daɗi a cikin hidimomin mazaunin. An ba fiye da kashi goma na dukan Lawiyawa masu ƙwazo, wato, dubu huɗu daga cikinsu aikin ‘ba da yabo,’ kuma “waɗanda aka koya masu su yi waƙa ga Ubangiji, watau dukan gwannai” sun kai ɗari biyu da tamanin da takwas.—1 Laba. 23:3, 5; 25:7.
4 Dauda da kansa ya rubuta waƙoƙi masu yawa da Lawiyawa suka rera. Babu shakka, duk wani Ba’isra’ila da yake da zarafin halarta a lokacin da aka rera zaburar Dauda ya ji daɗin abin da ya ji. Daga baya sa’ad da aka kai akwatin alkawari zuwa Urushalima, “Dauda . . . ya yi magana da manya na Leviyawa su sanya ’yan’uwansu mawaƙa, tare da kayan musika, su molo da giraya da kuge, suna kiɗi da ƙarfi, suna tada murya da murna.”—1 Laba. 15:16.
5, 6. (a) Me ya sa aka mai da hankali sosai ga waƙa a lokacin sarautar Dauda? (b) Ta yaya muka sani cewa waƙa tana da matsayi mai muhimmanci a bauta a Isra’ila ta dā?
5 Me ya sa aka mai da hankali sosai ga waƙa a zamanin Dauda? Domin sarkin da kansa mawaƙi ne? A’a, akwai wani dalili, wanda aka bayyana bayan ƙarnuka da yawa sa’ad da Sarki Hezekiya ya dawo da hidimomi a haikalin. Littafin 2 Labarbaru 29:25 ya ce: ‘Ya sa [wato, Hezekiya] Lawiyawa cikin gidan Ubangiji, da kuge da molaye, da giraya, bisa ga umurnin Dauda, da na Gad mai-gani na sarki, da Nathan annabi kuma: gama umurni daga wurin Ubangiji ne ta wurin annabawansa.’
6 Hakika, ta wurin annabawansa Jehobah ya umurci masu bauta masa su yabe shi da waƙa. An cire mawaƙa daga yin hidimomi da wasu Lawiyawa suke bukatan su yi domin su ba da isashen lokaci ga rubuta da kuma gwada waƙoƙin.—1 Laba. 9:33.
7, 8. Idan ya zo ga batun rera waƙoƙinmu na Mulki, mene ne ya fi gwani muhimmanci?
7 Za ka iya cewa, “In ya zo ga rera waƙa, babu shakka ba za a haɗa ni tare da gwanaye waɗanda suka rera waƙa a tantin taro ba!” Amma fa, ba dukan Lawiyawa mawaƙa ba ne gwanaye. In ji 1 Labarbaru 25:8, akwai ‘masu koyo’ kuma. Wani abin da za a yi la’akari da shi kuma shi ne wataƙila akwai waɗansu mutane daga wasu ƙabilu na Isra’ila da suka iya rera waƙa kuma gwanayen makaɗa ne, amma Jehobah ya naɗa Lawiyawa su kula da waƙa. Muna da tabbaci cewa ‘gwanaye’ ko kuwa ‘masu koyo’ dukan amintattun Lawiyawa da suka rera waƙar sun yi hakan da dukan zuciyarsu.
8 Dauda yana son waƙa kuma ya gwaninta wajen yin ta. Amma Allah yana mai da hankali ga iyawa ne kawai? A Zabura 33:3, Dauda ya rubuta: “[“Ku yi iyakar ƙoƙarinku,” NW] ku kyauta taken da babban amo.” Saƙon a bayyane yake: Abin da yake da muhimmanci shi ne ‘mu yi iyakar ƙoƙarinmu’ wajen yabon Jehobah.
Matsayin Waƙa Bayan Zamanin Dauda
9. Ka kwatanta abin da za ka gani da kuma ji da a ce ka halarci keɓewar haikali a lokacin sarautar Sulemanu.
9 A lokacin sarautar Sulemanu, waƙa ta ci gaba da kasancewa da matsayi mai muhimmanci a bauta ta gaskiya. A lokacin da ake keɓe haikali akwai rukunin mawaƙa masu ban sha’awa da sashen kaɗa jan ƙarfe mai ƙara da aka rera da ƙahoni guda 120. (Karanta 2 Labarbaru 5:12.) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “masu-ƙafo [waɗanda dukansu firistoci ne] da mawaƙa suka yi muwafaka, da za a ji muryarsu baki ɗaya ta yabo da godiya ga Ubangiji . . . gama nagari ne shi; gama jinƙansa ya tabbata har abada.” Da kammala waƙar, nan da nan sai “gidan ya cika da girgije,” da ke nuna amincewar Jehobah. Babu shakka zai kasance da ban sha’awa a ji amon dukan waɗannan ƙahoni tare da mawaƙa dubban da suke rerawa da murya ɗaya!—2 Laba. 5:13.
10, 11. Mene ne ya nuna cewa Kiristoci na farko sun yi amfani da waƙa a bautarsu?
10 Kiristoci na farko sun yi amfani da waƙa a bautarsu. Hakika, masu bauta a ƙarni na farko ba su yi taro a mazauni ba ko kuma haikali amma a gidajen mutane. Har ila sun yabi Allah cikin waƙa, duk da cewa an tsananta musu kuma suna da matsaloli da yawa.
11 Manzo Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci da ke Kolosi: “Kuna kuwa gargaɗi tare da zabura da waƙoƙin yabo da waƙoƙi masu-ruhaniya, kuna rairawa da godiya.” (Kol. 3:16) Bayan da aka jefa Bulus da Sila cikin kurkuku, sun fara “addu’a suna rera waƙa ga Allah,” ko da yake ba su da littafin waƙa da za su bi. (A. M. 16:25) Idan aka jefa ka cikin kurkuku, nawa ne cikin waƙoƙinmu na Mulki za ka iya rerawa a ka?
12. Yaya za mu nuna cewa mun san darajar waƙoƙinmu ta Mulki?
12 Tun da waƙa tana da matsayi mai daraja a bautarmu, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina nuna godiya ga waƙoƙi kuwa? Ina iya ƙoƙarina don na halarci tarurruka, taron da’ira da na musamman, da kuma taron gunduma a kan lokaci don na rera waƙar farawa tare da ’yan’uwana maza da mata, kuma idan na yi hakan ina rerawa da dukan zuciyata? Shin ina ƙarfafa yarana kada su ɗauki waƙoƙin da ake yi idan an idar da Makarantar Hidima ta Allah kuma za a soma Taron Hidima ko kuwa wanda ake yi sa’ad da aka idar da jawabi ga jama’a kuma za a soma Nazarin Hasumiyar Tsaro a matsayin lokacin shaƙatawa, zarafin da suke da shi na barin wurin zamansu?’ Rera waƙa tana cikin bautarmu. Hakika, ko da mu ‘gwanaye’ ne ko kuma ‘masu koyo,’ dukanmu za mu iya, haɗa muryoyinmu tare don yabon Jehobah.—Gwada 2 Korintiyawa 8:12.
Bukatunmu Suna Canjawa da Shigewar Lokaci
13, 14. Wane amfani ne rera waƙa da dukan zuciyarmu a lokacin taron Kirista yake da shi? Ka ba da misali.
13 Fiye da shekara ɗari da ta wuce, mujallar Zion’s Watch Tower [Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona] ta bayyana ɗaya daga cikin dalilai da ya sa waƙoƙinmu ta Mulki suke da muhimmanci sosai. Ta ce: “Rera waƙa ta gaskiya ita ce hanya mafi kyau ta sa gaskiya ta shiga kai da zuciyar mutanen Allah.” Kalmomin waƙoƙinmu da yawa suna da jigon Nassi, saboda hakan koyon kalmomin wasu cikin waƙoƙin zai iya kasance hanya mai kyau na sa gaskiya ta kasance a zukatan mutane. Sau da yawa, rera waƙa da muke yi da dukan zuciya a ikilisiya tana motsa baƙi da yawa da suka halarci taronmu a rana ta fari.
14 Sa’ad da C. T. Russell yake dawowa daga wurin aiki a wata yamma a shekara ta 1869, ya ji ana rera waƙa a wata majami’a. A lokacin, ya riga ya gaskata cewa ba zai taɓa sanin gaskiya game da Allah ba. Saboda haka ya yanki shawara ya ba da kai sosai ga sana’arsa, ya yi tunani cewa idan ya samu kuɗi, zai iya magance wasu bukatun mutane ko da ba zai iya taimaka musu su san gaskiya game da Allah ba. Ɗan’uwa Russell ya shiga cikin babban ɗakin taro da ba a share ba kuma ya ga ana hidimomin addini a ciki. Ya zauna kuma ya saurara. Daga baya ya rubuta cewa abin da ya ji da daddaren “da taimakon Allah ya isa ya ƙarfafa bangaskiyarsa da ta raunana cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki.” Ka lura cewa waƙoƙi ne da farko suka jawo hankalin Ɗan’uwa Russell zuwa taron.
15. Waɗanne gyare-gyare ne game da fahiminmu ya sa ya dace a sake littafinmu na waƙa?
15 Da shigewar lokaci an yi gyara ga fahiminmu na Nassosi. Misalai 4:18 ta ce: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” Ƙarin haske ya sa aka bukaci yin gyara a yadda muke “rera waƙa ta gaskiya.” A cikin shekara 25 da ta shige, Shaidun Jehobah a ƙasashe da yawa sun more yin amfani da littafin waƙa mai jigo Sing Praises to Jehovah.b A cikin waɗannan shekaru tun lokacin da aka wallafa wannan littafin da farko, haske ya haskaka a kan batutuwa masu yawa, kuma an daina yin amfani da wasu furci da suke cikin wannan littafin waƙa. Alal misali, ba ma cewa “sabon tsari” amma “sabuwar duniya.” Kuma yanzu muna cewa za a tsarkake sunan Jehobah, ba za a kunita sunan ba. A bayane yake cewa, a batun koyarwa da akwai bukatar daidaita littafinmu na waƙa.
16. Ta yaya sabon littafinmu na waƙa zai taimaka mana mu bi gargaɗin Bulus da ke Afisawa 5:19?
16 Saboda wannan da wasu dalilai, Hukumar Mulki ta amince a wallafa sabon littafin waƙa mai jigo Sing to Jehovah. An rage adadin waƙoƙin a cikin sabon littafinmu na waƙa zuwa ɗari da talatin da biyar. Domin waƙoƙi kaɗan ne kawai za a koya, zai yiwu mu haddace aƙalla wasu cikin sababbin waƙoƙin. Hakan ya jitu da gargaɗin Bulus da ke rubuce a Afisawa 5:19.—Karanta.
Za Ka Iya Nuna Godiyarka
17. Wane tunasarwa ne zai iya taimaka mana mu sha kan jin kunya idan ya zo ga rera waƙa a ikilisiya?
17 Shin ya kamata mu bar kunya ya hana mu rera waƙa a taron Kirista? Ka yi la’akari da shi hakan: Idan ya zo ga batun furcinmu, gaskiya ne cewa “dukanmu mu kan yi tuntuɓe.” (Jas. 3:2) Duk da haka, ba ma ƙyale furcin ajizanci ya hana mu yabon Jehobah ta wajen wa’azi gida gida. Saboda haka bai kamata mu ƙyale yin waƙa da muryoyinmu na ajizanci ya hana mu yabon Allah ba. Jehobah wanda ya “yi bakin mutum” yana farin ciki ya saurara yayin da muke amfani da muryoyinmu don rera yabonsa.—Ex. 4:11.
18. Ka ba da shawarwari don koyon waƙoƙin.
18 An wallafa faifan CD mai jigo Sing to Jehovah—Vocal Renditions a cikin harsuna da yawa. Suna ɗauke da kaɗe-kaɗe masu kyau na sababbin waƙoƙin. Saurarar shirye-shiryen waƙar tana da daɗi. Ka riƙa saurararsu a koyaushe, ta hakan ba da daɗewa ba za ka koya aƙalla wasu cikin kalmomin sababbin waƙoƙinmu. An rubuta kalmomin waƙoƙinmu da yawa yadda idan ka rera layi ɗaya, za ka iya sanin abin da za a rera a na gaba. Saboda haka, sa’ad da ka saka faifan CD, ka yi ƙoƙari ka bi waƙoƙin. Idan ka saɓa da waƙoƙin a gida, babu shakka za ka iya rera ta sosai a Majami’ar Mulki.
19. Waɗanne abubuwa aka yi don a shirya waƙoƙinmu na Mulki?
19 Yana da sauƙi mu ƙi ɗaukan kaɗe-kaɗe da ake sakawa a ranar taro na musamman, taron da’ira, da taron gunduma da muhimmanci. An yi aiki da yawa wajen shirya waƙar. Bayan an zaɓa waƙar, sai a ba mambobin WatchTower sittin da huɗu waɗanda za su yi kaɗe-kaɗen takardar a kan yadda za a tsara waƙar. Sai mawaƙan su yi sa’o’i da yawa suna gwada waƙoƙin da za su maimaita kuma a ƙarshe sai su yi naɗin waƙoƙin a Patterson, New York. Mutum goma cikin waɗannan ’yan’uwa maza da mata ba sa zama a ƙasar Amirka. Dukansu sun ɗauka gata ne su sa hannu wajen yin tanadin waƙa mai daɗi don ayyukanmu na tsarin Allah. Muna iya nuna godiyarmu don ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na ƙauna. Sa’ad da mai kujera a taronmu na da’ira na musamman da na gunduma ya gayyace mu mu zauna, bari mu yi hakan nan da nan kuma mu saurara ga kaɗe-kaɗe da aka shirya da kyau.
20. Mene ne ka kuɗiri aniya ka yi?
20 Jehobah yana saurarar waƙoƙinmu na yabo. Suna da muhimmanci a gare shi. Muna iya sa shi farin ciki ta wajen rera waƙa da dukan zuciyarmu duk lokacin da muka yi taro don bauta. Hakika, ko mu gwanaye ne ko kuma masu koyo, bari mu “raira ga Ubangiji.”—Zab. 104:33.
[Hasiya]
a Abin farin ciki, ƙarnuka goma bayan mutuwar Dauda, mala’iku masu yawa sun sanar da haihuwar Almasihu ga makiyaya waɗanda suna lura da tumakinsu a filaye kusa da Bai’talami.—Luk 2:4, 8, 13, 14.
b Akwai duka waƙoƙi ɗari biyu da ashirin da biyar a cikin fiye da harsuna ɗari.
Mene ne Ra’ayinka?
• Waɗanne misalai na zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa waƙa tana da matsayi mai muhimmanci a bautarmu?
• Wane nasaba ka gani yake tsakanin yin biyayya ga umurnin Yesu da ke rubuce a Matta 22:37 da kuma rera waƙoƙin Mulki da dukan zuciyarmu?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna godiya da ta dace don waƙoƙinmu na Mulki?
[Hoton da ke shafi na 23]
Kuna hana yaranku barin wurin zamansu ba gaira ba dalili a lokacin waƙa?
[Hoton da ke shafi na 24]
Kana koyon kalmomin sababbin waƙoƙinmu na mulki a gida?