Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/14 p. 7
  • Sababbin Waƙoƙi don Ibada!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sababbin Waƙoƙi don Ibada!
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waka da Farin Ciki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Kana Shirye Ka Yi Waƙa Ga Jehobah a Taronmu?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Ka Rera Waƙa Ga Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Shawara a Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 12/14 p. 7

Sababbin Waƙoƙi don Ibada!

1 A taron shekara-shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da aka yi a ranar 4 ga Oktoba, 2014, an sanar da mahalarta cewa za a yi gyara a littafin waƙa da muke amfani da shi a yanzu. Hakika wannan sanarwar ta sa ’yan’uwa farin ciki sosai. An tuna wa dukan mahalarta muhimmancin waƙoƙin Mulki a ibadarmu.—Zab. 96:2.

2 Kana iya tunanin cewa, ‘Me ya sa ake so a yi gyara a littafin waƙarmu?’ Akwai dalilai da dama. Na ɗaya, muna daɗa samun ƙarin haske a yadda muka fahimci Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya shafi kalmomin da aka yi amfani da su a cikin waƙoƙinmu. (Mis. 4:18) Ga dalili na biyu: Kalmomi da kuma furuci da yawa a littafin waƙar da muke amfani da shi yanzu an ɗauko su ne daga juyin New World Translation na dā. Saboda haka, wajibi ne a daidaita kalmomin waƙar da na sabon juyin New World Translation. Da yake daidaita waɗannan kalmomin zai ɗan ɗauki lokaci, an yanke shawarar daɗa sababbin waƙoƙi a kan waɗanda ake da su yanzu.

3 Shin za mu jira sai an fito da sabon littafin waƙar ne kafin mu soma rera sababbin waƙoƙin? A’a. Muna farin cikin sanar da ku cewa daga yanzu zuwa ’yan watannin da ke gaba, za a riƙa fitar da sababbin waƙoƙin a dandalinmu na jw.org/ha. Idan an fitar da sabuwar waƙa, za a saka ta a sashe na ƙarshe a Taron Hidima da sunan nan “sabuwar waƙa.”

4 Yadda Za Ku Koyi Sababbin Waƙoƙin: Koyan sabuwar waƙa yana iya zama abu mai wuya. Duk da haka, zai dace mu rera waƙoƙi da murya sosai a taro kamar marubucin zabura, maimakon ‘mu yi shuru.’ (Zab. 30:12) Ga wasu matakan da za mu iya bi don mu koyi sababbin waƙoƙin.

  • Ku saurari sautin waƙar da aka haɗa da piano sau da sau a dandalinmu. Idan muka saurari sautin sau da sau, zai yi mana sauƙi mu tuna waƙar.

  • Ku koyi kalmomin waƙar kuma ku yi ƙoƙari ku haddace su.

  • Ku riƙa rera kalmomin kuna bin sautin har sai kun saba da waƙar.

  • Ku rera sababbin waƙoƙin sau da sau sa’ad da kuke Ibada ta Iyali har sai kun saba da waƙoƙin.

5 A cikin watanni masu zuwa, idan za a kammala Taron Hidima da wata sabuwar waƙa, ’yan’uwa za su saurari sautin sau ɗaya. Bayan haka, sai a sake kunna sautin don masu sauraro su rera waƙar tare, kamar yadda muka saba.

6 Waƙoƙinmu suna ba mu damar haɗa muryoyinmu wajen yabon Jehobah. Saboda haka, sa’ad da muke taro, kada mu riƙa barin wurin zamanmu a duk lokacin da ake so a rera waƙa.

7 Akwai wata hanya kuma da za mu iya nuna cewa muna ɗaukan waƙoƙin ibadarmu da muhimmanci sosai. A manyan taronmu, akan soma kowane sashe da kaɗe-kaɗe. ’Yan’uwa maza da mata daga ƙasashe dabam-dabam suna ɗaukan nauyin kansu zuwa Patterson da ke birnin New York sau biyu a shekara, don su harhaɗa waƙoƙin da ake amfani da su a ibadarmu. Saboda haka, idan mai kujera ya gaya mana mu zauna don mu saurari abin da mawaƙan nan suka shirya mana, ya kamata mu yi hakan. Yin haka zai taimaka mana mu shirya zukatanmu don taron.—Ezra 7:10.

8 Za mu rufe taronmu na yau da sabuwar waƙar nan “An Kafa Mulkin a Sama—Bari Ya Zo!” An rubuta wannan waƙar ne musamman domin cika shekara ɗari da kafa Mulkin Allah kuma an rera ta a taron shekara-shekara da aka yi kwanan nan.

9 Hakika sababbin waƙoƙin nan suna cikin abubuwa “masu kyau” da Jehobah ya ba mu. (Mat. 12:35a) Bari mu ƙuduri anniya cewa za mu koyi waɗannan sababbin waƙoƙin kuma mu rera su da zuciya ɗaya, domin mu yabi Allah kuma mu ɗaukaka shi.—Zab. 147:1.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba