Shawara a Kan Yin Nazari
Ka Haddace “Waƙoƙin Godiya ga Allah”
Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lorraine daga Amurka, ta ce: “A duk lokacin da nake fama da baƙin ciki, Jehobah yana amfani da waƙoƙin JW ya ƙarfafa ni.”
Kiristoci sun daɗe suna rera “waƙoƙin godiya ga Allah.” (Kol. 3:16, New World Translation) Idan ka haddace waƙoƙin nan, hakan zai taimaka maka ka iya rera su ko a lokacin da ba ka da littafin waƙar ko kuma waya. Ka bi shawarwarin da ke gaba don su taimaka maka ka iya haddace waƙoƙinmu.
Ka karanta kalmomin waƙar da kyau don ka fahimci maꞌanarsu. Idan ka fahimci abu da kyau, ba zai yi maka wuya ka tuna da shi ba. Duka kalmomin waƙoƙinmu, har da na JW da na yara, suna dandalin jw.org. A sashen Laburare, ka shiga inda aka ce, “Waƙa.”
Ka rubuta kalmomin waƙar a takarda. Hakan zai ƙara taimaka maka ka yi saurin tunawa da su.—M. Sha. 17:18.
Ka rera waƙar da babbar murya. Ka karanta ko ka rera waƙar sau da yawa.
Ka gwada ka ga ko za ka iya haddace waƙar. Ka rera waƙar ba tare da kallon takardar waƙar ba, saꞌan nan ka duba takardar don ka ga ko ka iya tuna kalmomin daidai.