Sabon Talifin da Zai Soma Fita a Cikin Hasumiyar Tsaro
Mun saba amfani da talifofin nan, “Ka Koya Daga Kalmar Allah” da ke fitowa a Hasumiyar Tsaro don soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a Asabar ta farko na kowane wata. Somawa daga Janairu, za a sauya shi da “Amsoshi Daga Littafi Mai Tsarki,” wanda zai riƙa fitowa a bangon baya na Hasumiyar Tsaro na wa’azi. Za mu iya amfani da talifin sa’ad da muke wa’azi kamar yadda muke amfani da “Ka Koya Daga Kalmar Allah.” (km 12/10 shafi na 2) Kuma kamar yadda muka saba yi, za a riƙa saka bayani game da yadda za a gabatar da talifin a Hidimarmu ta Mulki don mu yi amfani da shi a Asabar ta farko na kowane wata don soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.