Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Sa’ad da Kuke Wa’azi
Ku Ƙarfafa Mutane Su Shiga Dandalin: Wasu mutanen da ba sa son su tattauna da mu ko kuma su karɓi littattafanmu za su yarda su yi bincike game da Shaidun Jehobah ta wajen shiga Dandalin jw.org sa’ad da suke cikin gidansu. Saboda haka, ku riƙa gaya wa mutane game da Dandalin a duk lokacin da kuka sami damar yin haka.
Ku Amsa Tambayoyi: A wasu lokatai, wani da ke son saƙonmu ko wani idon sani zai iya mana tambaya game da Shaidun Jehobah ko kuma koyarwarmu. Ku nuna masa amsar nan take ta wajen amfani da kwamfuta ko kuma wayar salula mai Intane. Amma zai fi dacewa mu karanta ayoyi da aka rubuta daga Littafi Mai Tsarki kai tsaye. Idan ba ku da waya ko kuma wata ƙaramar na’ura mai Intane, ku bayyana wa mutumin yadda zai iya samun amsar tambayar da kansa a dandalin jw.org.—Ku danna “Abubuwan da Aka Koyar Daga Littafi Mai Tsarki/Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki” ko kuma “Game da Shaidun Jehobah/Tambayoyin da Ake Yawan Yi.”
Ku Tura Talifi ko Kuma Littafi ga Wani da Kuka Sani: Za ku iya aika wa mutane littattafai a nau’in PDF ko kuma EPUB ta saƙon imel. Ko kuma ku sauko da karatun littafin a cikin CD. A duk lokacin da kuka ba da cikakken littafi ko ƙasida ko kuma mujalla da kuka saukar daga dandalin ga wani da bai yi baftisma ba, za ku iya rubuta hakan a cikin rahotonku na wa’azi a ƙarshen wata. Kada ku tura littattafai ba tare da kun saka sunanku ba kuma kada ku tura littattafai ga mutane da yawa a take. Ƙari ga haka, kada ku saka littattafanmu a wasu dandalin Intane dabam.—Ku danna “Littattafai.”
Ku Nuna wa Mutane Labarai na Kwanan Nan Game da Shaidun Jehobah: Hakan zai taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki da kuma wasu da kuke musu wa’azi su fahimci cewa muna aikin wa’azi ne a faɗin duniya kuma muna hakan cikin haɗin kai. (Zab. 133:1)—Ku danna “Talifofin Labarai.”
[Hotunan da ke shafi na 5]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Ku Gwada Shiga Dandalin
1 Idan kuka danna “Littattafai,” sai ku zaɓi littattafan da kuke so ku saukar. Bayan haka, ku danna EPUB ko PDF don ku sauko da littafin ko kuma danna MP3 ko kuma AAC don ku sauko da sautin karatun da kuke so.
2 Ku danna MP3 don ku sami jerin talifofi dabam-dabam da ke ciki. Sai ku danna jigon talifin don ku sauko da shi ko kuma ku danna alamar nan ▸ don ku saurari karatun ta Intane.
3 Za ku iya zaɓan wani yare dabam daga wannan jerin idan kuna son ku sauko da littafi a wannan yaren.