Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi don Ku Taimaki Wanda Yake Wani Yare Dabam
Ku Nuna Masa Dandalinmu: Ku nuna masa yadda zai iya amfani da fasalin nan “Harshen Dandalin” don ya bincika dandalin a yarensu. (A wasu harsuna, wani sashe ne kawai zai bayyana.)
Ku Nuna Masa Wani Shafi a Yarensu: Ku buɗe wani shafi daga cikin littattafanmu, alal misali, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? Ku shiga inda aka rubuta “Ka Karanta a” don ku zaɓi yaren mutumin.
Ku Sa Ya Saurari Karatun Wani Talifi: Ku duba wani talifin da za a iya sauraronsa a yaren mutumin, sai ku kunna masa don ya ji karatun. Idan kuna koyon wani yare, ku riƙa sauraron karatu a wannan yaren yayin da kuke karanta wani talifi kuma ta hakan, za ku ƙware.—Ku danna “Littattafai/Littattafai da Ƙasidu” ko kuma “Littattafai/Mujallu.”
Yi wa Kurame Wa’azi: Idan kun haɗu da wani kurma, ku kunna masa bidiyon wani surar Littafi Mai Tsarki ko kuma wani littafi ko ƙasida ko warƙa a yaren kurame.—Ku danna “Littattafai/Yaren Kurame.”
[Hotunan da ke shafi na 6]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Ku Gwada Shiga Dandalin
1 Ku danna ▸ don ku saurari abin da kuka zaɓa (idan akwai a yarenku) ko kuma ku danna “Hanyoyin Saukowa” don ku sauko da littafin.
2 Za ku iya zaɓan wani yare ta wajen danna “Ka Karanta a” don shafin ya bayyana a yaren.
3 Za ku iya danna “Na Gaba” ko kuma ɗaya daga cikin kan magana da ke “Abubuwan da ke Ciki” don ku karanta wani talifi ko kuma babi dabam.