Kana Magana Da “Harshe Mai-tsarki” Sosai?
“Zan juya ma al’ummai da harshe mai-tsarki, domin dukansu su kira sunan Ubangiji.”—ZEPH. 3:9.
1. Wace kyauta ce Jehobah ya yi tanadinta?
MAHALICCIN ’yan adam, Jehobah Allah ne ya ba da kyautar harshe ba mutane ba. (Fit 4:11, 12) Ya sa Adamu, mutum na farko ya iya magana kuma ya tsara sababbin kalmomi kuma ta hakan ya faɗaɗa tsarin kalmominsa. (Fa. 2:19, 20, 23) Wannan kyauta ce mai ban al’ajabi. Hakan ya sa ’yan adam suna iya magana da Ubansu na samaniya kuma su yabe sunansa.
2. Me ya sa ’yan adam ba sa magana a harshe ɗaya kuma?
2 A ƙarnuka na 17, dukan mutane suna yin yare ɗaya, kuma suna “magana ɗaya.” (Far. 11:1) Sai tawayen da aka yi a zamanin Nimrod. Maimakon su bi umurnin Jehobah, ’yan adam masu tawaye suka taru a wurin da daga baya aka kira Babel domin suna so su kasance a wuri ɗaya. Sai suka soma gina babban hasumiya ba don su girmama Jehobah ba, amma don su ‘yi ma kansu suna.’ Jehobah ya riƙitar da ainihin harshen waɗannan masu tawaye kuma ya sa suka soma magana a harsuna dabam dabam. Da haka, sai suka watsu a duniya.—Ka karanta Farawa 11:4-8.
3. Menene ya faru sa’ad da Jehobah ya riƙitar da harshen ’yan tawaye a Babel?
3 A yau, wasu sun ce ana magana a harsuna fiye da 6,800 a dukan duniya. Dukan waɗannan harsuna suna bukatar tsari dabam dabam. Kamar dai a lokacin da Jehobah ya riƙitar da harsunan waɗanda suka yi tawaye, ya sa ba su iya tuna da yarensu na dā ba. Ya yi musu tanadin tsarin sababbin kalmomi kuma ya canja yadda suke tunani. Shi ya sa aka kira wajen hasumiyar “dagula,” ko kuma Babel. (Far. 11:9; LMT.) Littafi Mai Tsarki ne kaɗai ya bayyana tushen harsuna dabam dabam da muke da su a yau.
Sabon Harshe Mai Tsarki
4. Menene Jehobah ya ce zai faru a zamaninmu?
4 Kamar yadda labarin abin da Allah ya yi a Babel yake da sha’awa, akwai wani abu mafi ban sha’awar da kuma muhimmanci da ya faru a zamaninmu. Ta wurin annabinsa Zephaniah, Jehobah ya ce: “Sa’annan zan juya ma al’ummai da harshe mai-tsarki, domin dukansu su kira sunan Ubangiji, su bauta masa da zuciya ɗaya.” (Zeph. 3:9) Menene “harshe mai-tsarki,” kuma ta yaya za mu koyi yin magana da shi sosai?
5. Menene harshe mai tsarki, kuma menene sakamakon wannan canjin harshe?
5 Harshe mai tsarki shi ne gaskiya game da Jehobah Allah da kuma nufinsa da ke cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Wannan “harshe” ya ƙunshi fahimtar gaskiya sosai game da Mulkin Allah da kuma yadda zai tsarkaka sunan Jehobah, ya ɗaukaka ikon mallakarsa, da kuma yadda zai kawo albarka ga amintattu mutane har abada. Menene sakamakon wannan canjin harshe? An gaya mana cewa mutane za su “kira sunan Ubangiji” kuma za su “bauta masa da zuciya ɗaya.” Ba kamar abin da ya faru a Babel ba, wannan canjin zuwa harshe mai tsarki ya jawo yabo ga sunan Jehobah kuma ya kawo haɗin kai a tsakanin mutanensa.
Koyon Harshe Mai Tsarki
6, 7. (a) Menene koyar sabon harshe ya ƙunsa, kuma yaya hakan ya shafi koyon harshe mai tsarki? (b) Menene za mu tattauna yanzu?
6 Sa’ad da mutum yake son ya koyi wani yare, ba haddace sababbin kalmomi ne kawai ya kamata ya yi ba. Koyan sabon yare ya ƙunshi koyon sabuwar hanyar yin tunani. Yadda ake tunani da kuma yadda za a iya sa mutum dariya zai iya kasance dabam a wani yare. Yadda za a furta sabon sauti zai bukaci yin amfani da gaɓoɓin magana dabam, kamar harshe. Haka yake idan muka soma koyon harshe mai tsarki na koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ana bukatar fiye da koyon muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki. Koyon wannan sabon harshe ya ƙunshi gyara tunaninmu.—Ka karanta Romawa 12:2; Afisawa 4:23.
7 Menene zai taimake mu mu fahimci harshe mai tsarki kuma mu yi amfani da shi sosai? Kamar yadda yake da koyon wani yare, akwai wasu hanyoyi na musamman da za su taimake mu mu gwaninta a yin amfani da harshe na koyarwar Littafi Mai Tsarki. Bari mu tattauna wasu hanyoyi na musamman da mutane suke amfani da shi don koyon wani harshe kuma mu ga yadda waɗannan hanyoyi za su iya taimakon mu mu koyi wannan sabon harshe na alama.
Magana da Harshe Mai Tsarki Sosai
8, 9. Me ya kamata mu yi idan muna so mu koyi harshe mai tsarki kuma me ya sa hakan na da muhimmanci sosai?
8 Saurarawa da kyau. Da farko, ga wanda bai taɓa jin wannan yaren ba, zai ga kamar ba zai taɓa iya fahimta ba. (Isha. 33:19) Amma sa’ad da mutum ya soma mai da hankali ga abin da yake ji, zai soma fahimtar wasu kalmomi kuma ya koyi yadda ake amfani da su. Hakazalika, an aririce mu: “Lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.” (Ibran. 2:1) Sau da yawa, Yesu ya aririce mabiyansa: “Wanda ya ke da kunnuwa, bari shi ji.” (Mat. 11:15; 13:43; Mar. 4:23; Luk 14:35) Hakika, ya kamata mu ‘ji, mu fahimci’ abin da muke saurara domin mu sami cin gaba a wajen fahimtar yare ta alama.—Mat. 15:10; Mar. 7:14.
9 Saurara yana bukatar mai da hankali sosai, amma ƙoƙarin yin haka yana da amfani. (Luk 8:18) Idan muna taron Kirista, muna sauraron abin da ake koyarwa kuwa, ko hankalinmu yana rabe? Yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari don mu riƙa mai da hankali ga abin da ake koyarwa. Idan ba haka ba, za mu iya zama masu nauyin ji.—Ibran. 5:11.
10, 11.(a) Ban da saurara da kyau, me ya kamata mu yi? (b) Menene yin magana da harshe mai tsarki ya ƙunshi?
10 Yin koyi da masu iya magana sosai. Ana ƙarfafa ɗalibai da suke koyon sabon yare su saurara kuma su koyi yadda masu iya magana sosai suke furta kalmomi da kuma yadda suke magana. Hakan zai taimaki ɗaliban su guje wa koyon wani lafazi da zai hana wasu fahimtar su. Don haka, ya kamata mu koya daga waɗanda suka zama gwani a ‘koyarwar’ da sabon raye. (2 Tim. 4:2) Ka nemi taimako. Ka amince da gyara idan ka yi kuskure.—Ka karanta Ibraniyawa 12:5, 6, 11.
11 Yin magana da harshe mai tsarki ya ƙunshi gaskatawa da gaskiya, koya wa wasu da kuma daidaita halinmu da dokokin Allah da ƙa’dominsa. Don mu koyi yin hakan, muna bukatar mu yi koyi da wasu. Hakan ya ƙunshi yin koyi da bangaskiyarsu da kuma ƙwazonsu. Ya kuma ƙunshi yi koyi da dukan tafarkin rayuwar Yesu. (1 Kor. 11:1; Ibran. 12:2; 13:7) Idan muka sa ƙwazo a yin wannan, hakan zai jawo haɗin kai a tsakanin mutane Allah, ya sa su su yi magana da harshe ɗaya.—1 Kor. 4:16, 17.
12. Ta yaya ne haddacewa yake da amfani a wajen koyan sabon yare?
12 Haddacewa. Ya kamata ɗalibai da suke koyon wani yare su haddace sababbin abubuwa. Hakan ya ƙunshi sababbin kalmomi da yadda ake furta su. Haddacewa zai taimaki Kiristoci a wajen iya magana da harshe mai tsarki. Hakika yana da kyau mu haddace sunayen littattafai da ke cikin Littafi Mai Tsarki a yadda aka tsara su. Wasu sun ƙuduri aniyar haddace ayoyi a cikin Littafi Mai Tsarki. Wasu sun amfana daga haddace waƙoƙin Mulki, sunayen kabilun Isra’ila, manzanni 12, da kuma halayen da suka ƙunshi ɗayar ruhu. A zamanin dā, Isra’ilawa da yawa sun haddace zabura. A wannan zamani, wani yaro ɗan shekara shida ya haddace surori 80 na Littafi Mai Tsarki. Za mu iya yin amfani da wannan baiwa mai muhimmanci kuwa?
13. Me ya sa maimaitawa yake da muhimmanci?
13 Maimaitawa yana taimako a wajen tuna abubuwa, kuma tunasarwa a kai a kai sashe ne mai muhimmanci a koyarwarmu ta Kirista. Manzo Bitrus ya ce: “Zan fa kasance da shiri kullayaumi garin in tuna muku da waɗannan al’amura, ko da shi ke kun san su, kun kuwa kahu cikin gaskiya da ke tare da ku.” (2 Bit. 1:12) Me ya sa muke bukatar tunasarwa? Saboda suna sa mu ƙara fahimtar abubuwa, suna faɗaɗa ra’ayinmu, kuma su ƙarfafa ƙudurinmu na yin biyayya ga Jehobah. (Zab. 119:129) Tuna mizanai da ƙa’idodin Allah zai taimake mu mu bincika kanmu kuma hakan zai taimake mu mu guji zama masu ‘ji da suke mantawa.’ (Yaƙ. 1:22-25) Idan ba mu ci gaba da tuna wa kanmu gaskiya ba, wasu abubuwa za su shafi zuciyarmu kuma hakan zai hana mu magana da harshe mai tsarki sosai.
14. Menene zai taimake mu idan muna nazarin harshe mai tsarki?
14 Ka furta kalamai idan kana karatu. Wasu ɗalibai suna ƙoƙari su koyi sabon yare a zuciyarsu ba tare da sun furta ba. Hakan ba ya kawo sakamako mafi kyau. Sa’ad da muke koyon harshe mai tsarki, wani lokaci za mu bukaci yin karatu “ciki-ciki” don mu mai da hankali da abin da muke karantawa. (Ka karanta Zabura 1:1, 2, NW.) Yin hakan zai sa mu riƙe abin da muka karanta sosai a zuciyarmu. A Ibrananci, furcin nan “karatu ciki-ciki” ya yi daidai da yin bimbini. Kamar yadda muke son abinci da muka ci ya yi aiki a jikinmu, muna bukatar mu yi bimbini idan muna so mu fahimci abin da muka karanta sosai. Muna keɓe lokaci sosai don yin bimbini bisa abin da muka yi nazari kuwa? Bayan mun karanta Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu yi tunani sosai bisa abin da muka karanta.
15. Ta yaya za mu bincika “nahawu” na harshe mai tsarki?
15 Bincika nahawu. Yana da kyau mu san yadda ake amfani da nahawu ko kuma yadda ake tsara kalmomi su zama jimla a sabon yare da muke koya. Hakan zai sa mu fahimci tsarin yaren, kuma mu yi yaren daidai. Kamar yadda yare yake da tsarin kalmomi da za a bi, harshe mai tsarki na Nassosi yana da “sahihiyan kalmomi.” (2 Tim. 1:13) Ya kamata mu yi amfani da wannan ‘sahihiyar’ kalma.
16. Wace matsalar ce ya kamata mu sha kan ta, kuma yaya za mu iya yin hakan?
16 Ci gaba da koyon yaren. Wani zai iya koyon yare sosai har ya iya tattaunawa a yaren amma sai ya daina ci gaba da koyon yaren. Hakazalika, hakan zai iya faruwa da masu koyon harshe mai tsarki. (Ka karanta Ibraniyawa 5:11-14.) Me zai iya taimakon mu mu sha kan irin wannan matsalar? Ka ci gaba da koyon wannan yaren. “Domin wannan fa bari mu daina zancen ruknai na Kristi, mu nace bi zuwa kamala; kada a sake kafa tushe na tuba ga barin matattun ayyuka, na bangaskiya ga Allah kuma,na koyaswar baptisma, na ɗibiyar hunnuwa, na tsahin matattu, da na hukumci maramatuƙa.”—Ibran. 6:1, 2.
17. Me ya sa yin nazari a kai a kai yake da muhimmanci? Ka ba da misali.
17 Ka tsara lokacin yin nazari. Yin nazari kaɗan a kai a kai ya fi yin nazari na dogon lokaci da ba a yi kullum. Ka yi nazari a lokacin da babu wani abin da zai ɗauke maka hankali. Koyon sabon yare yana kama da yin hanya a jeji. Idan ana bin hanyar koyaushe, tafiyar za ta yi sauki. Idan ba a bi hanyar na dogon lokaci ba, hanyar za ta rufe. Saboda haka, ana bukatar Nacewa da yin amfani da yaren kullum. (Dan. 6:16, 20) Ka yi addu’a don ka “tsare wannan da iyakar naciya” idan ya zo ga yin yaren Littafi Mai Tsarki.—Afis. 6:18.
18. Me ya sa ya kamata mu yi magana da harshe mai tsarki a koyaushe?
18 Yin yaren! Wasu da suke koyon sabon yare suna jinkirin yin yaren don suna jin kunya ko kuma suna jin tsoro ka da su yi kuskure. Hakan zai iya hana su ci gaba. Idan ya zo ka koyon yare, koyo a kai a kai yana da muhimmanci. Idan ɗalibin ya ci gaba da yin sabon yaren, zai iya yaren sosai. Da haka, ya kamata muma mu ci gaba da yin amfani da harshe mai tsarki a kowane lokaci. “Da zuciya mutum ya ke bada gaskiya zuwa adalci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto.” (Rom. 10:10) A lokacin baftisma muna ba da “shaida” a fili, kuma muna yin hakan a duk lokacin da muke yin magana game da Jehobah, har a lokacin da muke wa’azi. (Mat. 28:19, 20; Ibran. 13:15) Taronmu na Kirista suna ba mu zarafin yin furci da harshe mai tsarki.—Ka karanta Ibraniyawa 10:23-25.
Ku Haɗa Kai a Wajen Yin Amfani da Harshe Mai Tsarki don Ku Yabi Jehobah
19, 20. (a) Wani abin ban mamaki ne Shaidun Jehobah suke cim ma wa a zamaninmu? (b) Menene ka ƙudura za ka yi?
19 Da a ce kana Urushalima a ranar Lahadi da safe, na 6 ga Sivan, a shekara ta 33 K.Z da ka yi farin ciki sosai. Da sassafe, kafin ƙarfe tara, waɗanda suka taru a gidan bene suka soma “zance da waɗansu harsuna.” (A. M. 2:4) A yau, bayin Allah ba su da baiwar yin magana da wasu harsuna. (1 Kor. 13:8) Duka da haka, Shaidun Jehobah suna shelar bisharar Mulki a harsuna guda 430.
20 Abin farin ciki ne mu sani cewa kowane irin yare ne muke yi yanzu, dukanmu muna magana da harshe mai tsarki na koyarwar Littafi Mai tsarki ne. Hakan ya bambanta da abin da ya faru a Babel. Da harshe guda, mutanen Jehobah suna yabon sunansa. (1 Kor. 1:10) Bari mu ƙuduri aniyar ci gaba da bauta wa Jehobah da “zuciya ɗaya” tare da ’yan’uwanmu a dukan duniya yayin da muka ci gaba yin magana da harshe ɗaya sosai, don mu ɗaukaka Jehobah Ubanmu na Samaniya.—Ka karanta Zabura 150:1-6.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene harshe mai tsarki?
• Menene yin magana da harshe mai tsarki ya ƙunsa?
• Menene zai taimake ka ka yi magana da harshe mai tsarki sosai?
[Akwati a shafi na 23]
Ka Kyautata Yadda Kake Magana da Harshe Mai Tsarki ta wajen:
◆ saurarawa da kyau.
Luka 8:18; Ibran. 2:1
◆ yin koyi da masu magana sosai.
1 Kor. 11:1; Ibran. 13:7
◆ haddacewa da maimaitawa.
Yaƙ. 1:22-25; 2 Bit. 1:12
◆ furta kalamai idan kana karatu.
Zab. 1:1, 2; R. Yoh. 1:3
◆ bincika “nahawun.”
2 Tim. 1:13
◆ ci gaba da koyon yaren.
Ibran. 5:11-14; 6:1, 2
◆ tsara ainihin lokacin nazari.
Dan. 6:16, 20; Afis. 6:18.
◆ yin yaren.
Rom. 10:10; Ibran. 10:23-25
[Hotuna a shafi na 24]
Mutanen Jehobah suna da haɗin kai a wajen yin amfani da harshe mai tsarki