DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 9-11
“Mutanen Duniya Suna da Yare Ɗaya”
11:1-4, 6-9
Jehobah ya warwatsar da mutane masu rashin biyayya a Babel ta wajen rarraba yarukansu. A yau, yana tattara mutane da suke yaruka dabam-dabam kuma yana ba su “tsabtacciyar magana” ko harshe mai tsabta domin su “kira ga Sunan Yahweh, su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.” (Zaf 3:9; R. Yar 7:9) Harshe mai tsabtan yana nufin gaskiya da muka koya game da Jehobah da kuma nufinsa a Littafi Mai Tsarki.
Koyan sabon yare ya wuce koyan yadda ake furta sabbin kalmomi. Ya ƙunshi koyan yin tunani a wata hanya dabam. Haka ma, bayan mun koyi harshe mai tsabta, wato gaskiyar Littafi Mai Tsarki, hakan na sabonta tunaninmu. (Ro 12:2) Tunaninmu zai ci gaba da yin kyau kuma hakan zai sa mu bayin Allah mu kasance da haɗin kai.—1Ko 1:10.