Shin Za Ku Iya Ba Su Dama?
A ikilisiyoyi da yawa akwai masu shela da ba sa iya fita wa’azi sosai domin rashin lafiya ko kuma tsufa. (2 Kor. 4:16) Shin za ku iya ba waɗanda suke cikin irin wannan yanayin damar bin ku zuwa inda kuke nazari da mutane? Ko kuwa za ku iya shirya don ku je wa’azi gida-gida ko kuma ku ziyarci mutane na ɗan lokaci kawai da mai shelar da ke rashin lafiya? Idan mai shelar ba ya iya fita daga cikin gida, za ku iya kawo ɗalibinku gidansa don ku yi nazarin a wurinsa. Masu shela da yawa da suka tsufa sun ƙware sosai a yin wa’azi. Saboda haka idan kuka ƙoƙarta ku ƙarfafa su, ku ma za ku amfana. (Rom. 1:12) Ban da haka ma, Jehobah zai albarkace ku don yadda kuke ƙoƙari ku nuna musu ƙauna.—Mis. 19:17; 1 Yoh. 3:17, 18.