Ku Yi Amfani da Dandalinmu Wajen Koyar da Yaranku
1. Me ya sa aka tsara sashen “Yara” a dandalinmu?
1 An tsara dandalinmu na jw.org a hanya mai ban sha’awa don mutane manya da ƙanana. An tsara sashen “Yara” (danna Koyarwar Littafi Mai Tsarki > Yara) don ya taimaka wa yara su kusaci iyayensu kuma ya taimaka wa dukansu su kusaci Jehobah. (K. Sha 6:6, 7) Ta yaya za ku iya yin amfani da wannan sashen wajen koyar da yaranku?
2. Ta yaya za ku iya zaɓan batutuwan da suka dace da yaranku?
2 Ku Shirya Bisa ga Yanayinsu: Halin kowane yaro ya bambanta. (1 Kor. 13:11) Saboda haka, ta yaya za ku iya zaɓan batutuwan da suka dace da yaranku? Ku tambayi kanku: ‘Mene ne zai fi jawo hankalin yarana? Shin za su iya fahimtar abubuwa da yawa a take kuwa? Za su iya mai da hankali na dogon lokaci ne ko na ɗan lokaci?’ Idan kuna da yara ’yan shekara uku ko ƙasa da hakan, za ku iya tattauna labaran da ke ƙarƙashin sashen “Abin da Na Koya a Littafi Mai Tsarki.” Wasu iyalai kuma suna jin daɗin karanta labaran Littafi Mai Tsarki da ke sashen “Ku Koyar da Yaranku.” Ku yi la’akari da wasu abubuwa da ke gaba.
3. Ta yaya iyaye za su iya yin amfani da labarai da kuma ayyukan da ke sashen “Ayyuka don Bauta ta Iyali” yadda ya dace?
3 Ayyuka don Bauta ta Iyali: Iyaye suna iya yin amfani da wannan sashen don su yi nazari da yaransu. Idan kuna son ku san yadda za ku yi amfani da labaran da kuma ayyukan, ku danna inda aka rubuta “ka saukar” a sashen “Umurni ga Iyaye.” Ku yi amfani da abubuwan da ke sashen hotuna, kamar yi wa hotuna kala, don ku koyar da ƙananan yara. Ku taimaka wa yara da suka iya karatu su yi abin da ke cikin sashen “Ayyuka don Nazari.” A kowane aiki don Bauta ta Iyali, dukan ayyuka da za a yi a kan labarin mutum ɗaya ne a cikin Littafi Mai Tsarki, saboda haka dukan yaran za su iya jin daɗin yin ayyuka da ke cikin sashe ɗaya a bauta ta iyali.
4. Waɗanne abubuwa ne ke sashen “Ka Zama Abokin Jehobah”?
4 Ka Zama Abokin Jehobah: A wannan sashen, akwai bidiyoyi da waƙoƙi da kuma wasu ayyuka da za su taimaka wa iyaye su koya wa yaransu ƙanana Kalmar Allah. (K. Sha 31:12) Kowane gajeren bidiyon katoon yana koya wa yara darasi mai muhimmanci. Wasanni kamar na taimaka wa yara su nemi abubuwa a cikin zane suna nuna waɗannan darussan. Da yake yara suna jin daɗin rera waƙa sosai, waƙoƙi za su iya taimaka musu su tuna da abubuwan da suka koya. Saboda haka, ana saka waƙoƙinmu game da Mulkin Allah da kuma waɗanda aka rera musamman don yara a dandalin a kai a kai.
5. Me ya sa ya kamata iyaye su roƙi Jehobah ya taimake su su koya wa yaransu gaskiya?
5 Iyaye, Jehobah yana so ku yi renon yaranku da kyau. Saboda haka, ku roƙe shi ya taimaka muku ku koya wa yaranku gaskiya. (Alƙa. 13:8) Jehobah zai iya taimaka muku ku koyar da yaranku don su kasance da hikima kuma hakan zai taimaka musu su sami “ceto ta wurin bangaskiya wanda ke cikin Kristi Yesu.”—2 Tim. 3:15; Mis. 4:1-4.