Ku Yi Amfani da jw.org Yayin da Kuke Wa’azi—“Ka Zama Abokin Jehobah”
A ƙarƙashin “Koyarwar Littafi Mai Tsarki” a dandalin jw.org, akwai wani sashe a shafin yara da ake kira “Ka Zama Abokin Jehobah,” kuma wannan sashen na ɗauke da waƙoƙi da bidiyo da kuma umurni ga iyaye. Kun taɓa yin amfani da wannan sashen a wa’azi? Idan kuna yin nazari da mahaifiya ko kuma mahaifi mai ƙananan yara, zai dace ku nuna masa sashen nan. Daga nan, zai iya shiga wasu sassan dandalinmu.
Sa’ad da wani ɗan’uwa yake rarraba wa mutane Bishara ta Mulki na 38, ya ba wata mata kofi guda kuma ta soma karantawa nan da nan. Matar tana da yara ƙanana kuma su ma sun so su san abin da ke cikin warƙar. Sai ɗan’uwan ya ɗan bayyana abin da ke cikin warƙar kuma ya nuna mata adireshin dandalinmu a bayan warƙar. Tun da yake matar ta nuna cewa tana son saƙonmu, sai ya kunna ma ita da yaranta wani bidiyon Kaleb a cikin na’urarsa.
Wata ’yar’uwa ta gaya wa abokiyar aikinta mai ƙananan yara game da dandalinmu da kuma bayanai masu amfani ga iyalai da ake samu a dandalin. Sai matar ta shiga dandalinmu tare da yaranta kuma daga baya ta gaya wa ’yar’uwan cewa yaranta sun yi ta zagaya gidan suna raira waƙar nan “Preach the Word,” wanda ɗaya ne cikin waƙoƙin da ke sashen “Ka Zama Abokin Jehobah.”
Ku ƙoƙarta ku san abubuwan da ke wannan sashen dandalin jw.org, kuma ku saukar da ɗaya daga cikin bidiyo ko waƙoƙi ko kuma umurni ga iyaye da ke sashen a cikin na’urarku. Ta hakan, za ku iya yin amfani da wannan sashen dandalin jw.org yayin da kuke wa’azi. Hakika, wannan sashen kayan aiki ne mai kyau da zai taimaka mana mu yi wa Ubangiji hidima!—A. M. 20:19.