Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Satumba p. 3
  • Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Shawara A Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Shawara A Kan Dandalinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Dandalinmu na Intane—An Tsara Shi Ne don ’Yan’uwa da Kuma Wasu Su Amfana
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Satumba p. 3

RAYUWAR KIRISTA

Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?

A Littafi Mai Tsarki, akwai shawarwarin da za su iya taimaka mana wajen magance matsalolin da muke fuskanta a kwanakin ƙarshen nan. (2Ti 3:​1, 16, 17) Duk da haka, a wasu lokuta muna bukatar mu san yadda za mu sami ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana sa’ad da muke fuskantar wata matsala. Alal misali, ku iyaye ne, kuma kuna neman shawara game da renon yara? Ko ku matasa ne, kuma riƙe aminci ga Jehobah yana yi muku wuya? Ko kuma kuna baƙin ciki ne don abokan aurenku sun mutu? Akwai talifofi a dandalin jw.org/ha da za su taimaka muku ku sami ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da matsalolin nan da wasu.​—K. Ma 2:​3-6.

Dandalin jw.org a waya. Wurin da aka nuna KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI.

A shafin farko na jw.org, ka danna KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI. (Ku duba hoto na 1.) A cikin jerin batutuwan da ke wurin, sai ku zaɓi batun da kuke so. Ko kuma ku danna LABURARE > TALIFOFI sai ku zaɓi batun da kuke so. (Ku duba hoto na 2.) Za ku kuma iya samun su a manhajar JW Library®.a Za ku iya dudduba talifofin a wuraren nan da aka ambata a sama. Wata hanya kuma ita ce, saka batun a inda aka rubuta “bincika” a jw.org/ha.

Dandalin jw.org a waya. Wurin da aka nuna LABURARE da sashen TALIFOFI.

Ku saka batutuwan da ke gaba a inda aka rubuta “bincika” sai ku zaɓi talifofin da za ku so ku karanta.

  • Renon yara

  • Baƙin cikin matasa

  • Idan aboki ko abokiyar aurenka ta rasu

a Za ku iya samun wasu batutuwan da akwai talifofinsu gabaki ɗaya a jw.org/ha ne kaɗai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba