Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/14 pp. 2-7
  • Sabon Tsari da Aka Yi ma Sababbin Warƙoƙi!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sabon Tsari da Aka Yi ma Sababbin Warƙoƙi!
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da Warka a Yin Shelar Bishara
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Yadda Za Mu Yi Amfani da Warkoki a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Kalmar Allah Rayayyiya Ce, Ka Yi Amfani da Ita!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Gabatarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 4/14 pp. 2-7

Sabon Tsari da Aka Yi ma Sababbin Warƙoƙi!

1. Waɗanne abubuwa ne aka yi musu sabon tsari mai ban sha’awa?

1 An fitar da sababbin warƙoƙi guda biyar a Taron Gunduma na 2013 mai jigo, “Kalmar Allah Gaskiya Ce!” Ƙari ga haka, an daɗa Bishara ta Mulki na 38 mai jigo “Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?” ga waɗannan sababbin warƙoƙi. An tsara waɗannan warƙoƙi shida a hanya mai ban sha’awa sosai. Me ya sa aka yi wannan sabon tsarin? Ta yaya za mu yi amfani da sabon tsarin nan sa’ad da muke wa’azi gida-gida?

2. Don me aka yi wannan sabon tsarin?

2 Abin da Ya Sa Aka Yi Wannan Sabon Tsarin: A yawancin lokatai, ana samun sakamako masu kyau sosai idan aka bi waɗannan matakai huɗu sa’ad da ake wa’azi: (1) Ka yi tambaya da za ta sa mutum ya bayyana ra’ayinsa. (2) Ka karanta wani Nassi. (3) Ka ba maigidan littattafai. (4) Ka yi tambaya da za ka ba da amsarta idan ka dawo, sa’an nan ka shirya ranar da za ka sake dawowa. Yadda aka tsara waɗannan sababbin warƙoƙi zai taimaka mana mu bi matakan nan cikin sauƙi.

3. Ta yaya za mu iya ba mutane sababbin warƙoƙin sa’ad da muke wa’azi?

3 Yadda Za A Yi Amfani da Su: (1) Bayan ka yi gaisuwa, ka nuna wa maigidan tambaya mai amsoshi dabam-dabam da ke gaban warƙar, kuma ka gaya masa ya faɗi ra’ayinsa a kan tambayar. (2) Ka buɗe warƙar kuma ka tattauna “Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce.” Ka karanta nassin da aka rubuta a wurin daga cikin Littafi Mai Tsarki, idan da hali. Idan maigidan yana da lokaci, ka tattauna “Abin da Za Ka Iya Mora Idan Ka Gaskata da Hakan.” (3) Ka ba shi warƙar, kuma ka ƙarfafa shi ya karanta idan ya sami lokacin yin hakan. (4) Kafin ka bar wurin, ka nuna masa tambayar da ke bayan warƙar a ƙarƙashin jigon nan “Ka Yi Tunani a Kan Wannan Tambayar” kuma ka shirya ranar da za ka dawo don ku tattauna amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar a kan tambayar.

4. Ta yaya za mu iya amfani da waɗannan sababbin warƙoƙi sa’ad da muka koma ziyara?

4 Yin amfani da warƙoƙin sa’ad da muka koma ziyara ma bai da wuya. Ka yi amfani da nassosin da aka rubuta a bayan warƙar don ka amsa tambayar da ka yi wa maigidan a tattaunawarku ta ƙarshe. Kafin ka tafi, ka nuna masa hoton ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a bayan warƙar, ka ba shi ƙasidar, sa’an nan ka nuna masa darasin da ya yi ƙarin bayani a kan batun da kuka tattauna. Idan ya karɓa, ka shirya da shi don ka dawo ku tattauna daga ƙasidar. Ta hakan, ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutumin ke nan! Idan ba ka so ka ba da ƙasidar, za ka iya ba mutumin wata warƙa dabam kuma ka shirya da shi don ku tattauna warƙar idan ka sake zuwa.

5. Ta yaya warƙoƙi suke taimaka mana a wa’azi?

5 Mun yi shekaru sama da 130 yanzu muna amfani da warƙoƙi a wa’azi. Ko da yake an canja fasalinsu da girmansu sau da sau, amma suna da amfani sosai. Bari mu yi amfani da waɗannan warƙoƙi masu sabon tsari wajen yaɗa koyarwar Littafi Mai Tsarki a duk faɗin duniya.—Mis. 15:7a.

[Taswira a shafi na 3-6]

RAHOTON HIDIMAR SHAIDUN JEHOBAH A DUKAN DUNIYA NA SHEKARA TA 2013

(Ka duba littafin)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba