Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/12 pp. 2-3
  • Ku Yi Amfani da Warka a Yin Shelar Bishara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Amfani da Warka a Yin Shelar Bishara
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Sabon Tsari da Aka Yi ma Sababbin Warƙoƙi!
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Kalmar Allah Rayayyiya Ce, Ka Yi Amfani da Ita!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yadda Za Mu Yi Amfani da Warkoki a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Gabatarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 10/12 pp. 2-3

Ku Yi Amfani da Warka a Yin Shelar Bishara

1. Ta yaya Shaidun Jehobah suka yi amfani warƙoƙi wajen yaɗa bishara?

1 Shaidun Jehobah sun daɗe suna amfani da warƙoƙi da ke ɗauke da bayanin Littafi Mai Tsarki wajen yin shelar bishara. A shekara ta 1880 ne C. T. Russell da abokan aikinsa suka fara wallafa warƙoƙi da ake kira Bible Students’ Tracts. An tanadar da waɗannan warƙoƙin wa masu karanta Hasumiyar Tsaro don su rarraba wa mutane. Warƙoƙi suna da muhimmanci sosai a yin wa’azin Mulkin Allah shi ya sa a shekara ta 1884 C. T. Russell ya yi rajistan wata ƙungiya wadda ba ta cin riba ba kuma an saka kalmar nan “tract,” wato, warƙa a cikin sunan da aka tsara ma ƙungiyar. Sunan ƙungiyar ita ce, Zion’s Watch Tower Tract Society, amma yanzu ana ce da ita, the Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. A shekara ta 1918, Shaidun Jehobah da aka fi saninsu da sunan nan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin, sun rarraba warƙoƙi miliyan 300. Har wa yau, yin amfani da warƙoƙi yana taimakawa wajen yaɗa bishara sosai.

2. Me ya sa warƙoƙi suke da muhimmanci?

2 Dalilan da Ya Sa Suke da Muhimmanci: Warƙoƙi suna da kyan gani kuma suna jan hankalin mutane. Kuma suna ɗauke da taƙaitattun bayanai masu ƙayatarwa da kuma ilimantarwa. Wasu sun gwammace a ba su warƙa saboda suna ganin cewa ba su da lokacin karanta mujalla ko kuma littafi. Kuma ba su da wuyar bayarwa sa’ad da ake wa’azi, ko da yara ma suna iya ba wa mutane ba tare da wani dogon bayani ba. Ƙari ga haka, ba su da girma kuma za a iya sakawa a aljihu.

3. Ka ba da labarin da ka taɓa karantawa ko kuma da ya taɓa faruwa da kai wanda ke nuna muhimmancin warƙa.

3 Mutane da yawa sun fara sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki ne daga karanta wata warƙa da Shaidun Jehobah suka wallafa. Alal misali, wata mata a ƙasar Haiti ta tsinci wata warƙarmu a kan titi. Sa’ad da ta karanta, sai ta ce, “Wannan ita ce gaskiyar da Littafi Mai Tsarki ke koyarwa!” Sai ta fara halartar taro a Majami’ar Mulki kuma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Daga baya, ta yi baftisma. Me ya taimaka mata ta fahimci gaskiyar? Warƙarmu da ke ɗauke da gaskiyar Kalmar Allah.

4. Mene ne burinmu sa’ad da muke ba da warƙoƙi a wa’azi?

4 Wa’azi Gida-gida: Tun da warƙoƙi suna da amfani sosai wajen yin wa’azi, za a riƙa saka su a cikin littattafan da za a ba da kowane wata, somawa da watan Nuwamba. Ba wai muna so mu ba mutane warƙoƙin ne kawai ba, amma ya kamata mu yi amfani da warƙoƙin wajen soma tattaunawa da su. Idan sun nuna cewa suna son su san gaskiya game da koyarwar Littafi Mai Tsarki sa’ad da muka yi musu wa’azi ko kuma sa’ad da muka koma don mu ziyarce su, za mu nuna musu yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ta wajen amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma wani littafi da aka tsara don yin haka. Mene ne za mu faɗa sa’ad da muke ba da warƙa a wa’azi gida-gida? Ya kamata mu karanta kuma mu fahimci bayanan da ke cikin warƙoƙin da muke ba wa mutane a wa’azi domin kowace warƙa da batun da take magana a kai.

5. Mene ne za mu faɗa sa’ad da muke ba da warƙa a wa’azi gida-gida?

5 Ya kamata gabatarwarmu ta dace da bayanin da ke cikin warƙar da kuma mutanen da ke yankinmu. Za mu iya soma tattaunawa da mutum ta wajen ba shi warƙar. Yadda aka tsara bangon warƙar zai iya sa mutumin ya yi marmarin jin wa’azinmu. Ƙari ga haka, za mu iya nuna masa warƙoƙi da dama kuma mu gaya ma sa ya zaɓi wanda ya fi so. Sa’ad da muke wa’azi a yankin da mutane ba sa son buɗe mana kofa don mu tattauna da su, za mu iya riƙe warƙar a yadda maigidan zai ga abin da ke bangon warƙar ko kuma mu ce muna so mu ji ra’ayinsu game da wani batu, sai mu tura musu warƙar ta ƙarƙashin kofar ko ta gefen kofar. Idan tambaya ce jigon warƙar, za mu iya tambayarsa ko mene ne ra’ayinsa game da jigon. Ko kuma za mu iya yin wata tambaya da za ta sa maigidan ya so tattaunawa da mu. Bayan haka, sai mu karanta wani sashe daga warƙar, idan muka karanta wata tambaya a ciki sai mu ba wa maigidan dama ya bayyana ra’ayinsa. Kuma za mu iya karanta wani nassi daga Littafi Mai Tsarki wanda ke ba da ƙarin haske game da jigon warƙar. Bayan mun gama tattauna batun, sai mu shirya lokacin da za mu dawo don mu ci gaba da tattaunawa. Idan ’yan ikilisiya sun saba ajiye littattafai wa waɗanda ba sa gida a lokacin wa’azi, sai su ajiye warƙar a inda wani ba zai gani ba don maigidan ya zo ya samu.

6. Ta yaya za mu ba da warƙoƙi sa’ad da muke wa’azi a kan titi?

6 Wa’azi a Titi: Ka taɓa yin amfani da warƙa sa’ad da kake wa mutane wa’azi a kan titi? Wasu suna sauri kuma ba za su so su tsaya su tattauna da mu ba. Saboda haka, ba za mu iya sanin ra’ayinsu game da Littafi Mai Tsarki ba. A maimakon mu ba su sababbin mujallu ba tare da mun tabbatar da cewa za su karanta ba, zai dace mu ba su warƙa. Da yake bangon yana da kyan gani kuma saƙon da ke ciki taƙaitacce ne, za su so su karanta idan suka samu ɗan lokaci. Amma idan ba sa hanzari, za mu iya tattauna abin da ke cikin warƙar da su.

7. Ka ba da labari da ke bayyana yadda za a yi wa’azi da warƙa a duk lokacin da aka sami zarafi.

7 Wa’azi a Duk Inda Aka Sami Zarafi: Yin wa’azi da warƙa a duk inda aka sami zarafi bai da wuya. Wani ɗan’uwa yakan saka warƙoƙi a cikin aljihunsa a duk lokacin da yake barin gida. Sa’ad da ya haɗu da wani, alal misali, mai sayar da kanti, sai ya ba shi warƙar don ya karanta. Sa’ad da wasu ma’aurata suke shirin zuwa yawon buɗe ido, sai suka ɗauki ƙasidar nan Good News for People Of All Nations da warƙoƙi a yaruka dabam-dabam don sun san cewa za su haɗu da mutane daga ƙasashe dabam-dabam. Da suka isa wurin sai suka kasa kunne, idan suka ji wani mutum mai sayar da kaya a kan titi ko kuma wani da ke zaune kusa da su a tasha ko a gidan abinci yana wani yare, sai su ba shi warƙa a yarensa.

8. Ta yaya za a kwatanta warƙa da iri?

8 “Ka Shuka Irinka”: Za a iya kwatanta warƙa da iri. Manomi yakan shuka iri a yalwace don bai san ko waɗanne ne za su tsira ba. Littafin Mai-Wa’azi 11:6 ya ba mu wannan shawara: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” Saboda haka, bari mu ci gaba da “watsa ilimi” game da Allah ta wajen yin amfani da warƙa a kowane lokaci.—Mis. 15:7.

[Bayanin da ke shafi na 3]

Tun da warƙoƙi suna da amfani sosai wajen yin wa’azi, daga watan Nuwamba, a lokaci-lokaci, za a riƙa saka su a cikin littattafan da za a ba da wa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba