Ku Yi Amfani da jw.org Yayin da Kuke Wa’azi
Dandalinmu na Intane hanya ce mai ban taimako wajen yaɗa bishara zuwa “iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Yawancin mutane ba su iya shigan dandalin jw.org da kansu ba, sai dai wani mai shela ya nuna musu yadda za su iya yin hakan.
Wani ɗan’uwa mai kula mai ziyara ya sauƙo da bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a wayarsa kuma yana nuna wa mutane a duk inda ya sami damar yin hakan. Alal misali, idan yana wa’azi gida-gida, yakan ce: “Na kawo ziyara ne don in taimaka wa mutane su sami amsoshi ga waɗannan muhimman tambayoyi: Me ya sa ake shan wahala sosai a duniya? Ta yaya Allah zai kawo ƙarshenta? Kuma mene ne zai taimaka mana mu jure a yanzu? Wannan gajeren bidiyon ya ba da amsar waɗannan tambayoyin.” Sai ɗan’uwan ya kunna bidiyon kuma ya lura da yadda suke ji yayin da suke kallon bidiyon. Bidiyon yana jan hankalin yawancin mutane sosai, har ma ba sa ƙifta ido yayin da suke kallon har sai ya ƙare. Bayan hakan, ɗan’uwan yakan ce: “Ka ji an ce za ka iya cika akwati a dandalinmu don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai. Amma, tun da ga ni nan, zan iya nuna maka yadda muke yin nazarin.” Idan maigidan ya yarda, sai ɗan’uwan ya nuna masa yadda ake nazari da ƙasidar Albishiri Daga Allah! Idan maigidan ya ce bai da lokaci, sai ɗan’uwan ya shirya da shi don ya sake dawowa wani lokaci ya nuna masa yadda ake nazarin. A duk lokacin da ya je shan shayi a kanti, yakan yi irin wannan tattaunawar da wanda ke kusa da shi bayan sun gaisa. Shin kuna amfani da jw.org yayin da kuke wa’azi?