Za Ka Kasance Mai Himma Kamar Jehobah da Yesu a Wannan Lokacin Tuna da Mutuwar Yesu?
1. Mene ne Shaidun Jehobah suke ƙoƙarin yi a lokacin Tuna da Mutuwar Yesu?
1 Jehobah yana cim ma nufinsa da himma. A yayin da marubucin littafin Ishaya yake ambata wasu albarkun da Mulkin Allah zai kawo, ya ambata a Ishaya 9:7 cewa: “Himmar Ubangiji mai-runduna za ya aikata wannan.” A lokacin da Ɗan Allah yake hidima a duniya ma, ya nuna cewa yana da himma sosai don ibada ta gaskiya. (Yoh. 2:13-17; 4:34) A lokacin Tuna da Mutuwar Yesu a kowace shekara, masu shela da yawa a faɗin duniya suna yin iyakacin ƙoƙarinsu su kasance masu himma kamar Jehobah da kuma Yesu ta wajen yin wa’azi da ƙwazo sosai. Za ku so ku bi misalinsu?
2. Idan mu masu himma ne, mene ne za mu yi daga ranar 7 ga Maris?
2 Kamfen don Gayyatar Mutane: A wannan shekarar za mu soma gayyatar mutane zuwa taron ne a ranar Asabar, 7 ga Maris. Ku soma shirya yadda za ku yi wa’azi da himma a lokacin tun yanzu. ’Yan’uwa za su yi farin ciki sosai a yayin da suke iyakacin ƙoƙarinsu su gayyaci dukan mutane da ke yankinsu. Zai dace ku ƙoƙarta sosai ku gayyaci abokan aikinku da abokan makarantarku da danginku da ɗalibanku da dai sauran mutane zuwa wannan taron, ta wajen yin amfani da takardar gayyata ko kuma dandalin jw.org.
3. Ta yaya za mu yi wa’azi da himma sosai a watannin Maris da Afrilu?
3 Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci: Idan muna da himma, za mu so mu faɗaɗa hidimarmu. Babu shakka, ’yan’uwa da yawa za su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watannin Maris da Afrilu domin a waɗannan watannin, majagaba na ɗan lokaci suna da damar ba da rahoton awa 30. Sa’ad da kuke nazari ku kaɗai ko kuna ibada ta iyali, ku yi tunani a kan yadda za ku iya yin hakan kuma ku yi addu’a Jehobah ya taimake ku. (Mis. 15:22) Idan kuka nuna himma a yin wannan kamfen, hakan zai iya motsa wasu su bi misalinku. Idan kuka daidaita al’amuranku don ku yi wa’azi da ƙwazo sosai, za ku nuna cewa kuna bin misalin Yesu.—Mar. 6:31-34.
4. Wane sakamako ne za mu samu idan muka zama masu himma kamar Jehobah da Yesu?
4 Za mu sami sakamako masu kyau sosai idan muka kasance masu himma kamar Jehobah da Yesu a wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu. Za mu yi wa’azi ga mutane da yawa a yankinmu. Za mu yi farin ciki don mun yi wa Jehobah hidima kuma mun ba da lokacinmu wajen taimaka ma wasu. (A. M. 20:35) Mafi muhimmanci ma, za mu sa Allahnmu mai himma da kuma Ɗansa farin ciki sosai.